*BY MIEMIEBEE*
PAGE 57
*FEBRUARY, 2017*
"Mallam ko nan ne gidansu Nusee?"
"Eh nan ne Hjy, a bud'e muku gate ne?"
"A'a yanzu zamu fito kada ka damu."
"Yauwa sannun ku da zuwa toh." Maza-maza suka fito suka shiga ciki inda suka soma yin sallaman tsiya.
"Sallama de!" Cewar Ruky tana bubbuga entrance door in gidan. "Mutan gidan basu nan ne wai kam?"
"Suna nan" cewar Maman Nusee dake zaune a gefen 'yarta akan dining table suna having lunch.
"Toh kunyi bak'i" cewar Safiyya.
"Toh ana zuwa" Mama tayi maganan da d'an k'arfi yadda zasu jita sannan ta sassauta muryarta wa Nusee "tashi kije ki bud'e musu." One more spoon ta kai baki sannan ta tashi ta bud'e musu "sannunku da zuwa" ta fad'a cikin innocent voice nata cike da fara'a.
"Yauwa sannu kece Nusee ne ko Nusaiba?" Asked Ruky.
"Itace mana bakiga pengelgel legs natan bana?" cewar Safiyya tana bin legs na Nusee dake cikin leggings da dirty look. Ignoring her tace "eh nice, bismillah ku shigo."
"A'a nan ma yayi" cewar Ruky tana hararta. "ina wuni toh?" Cewar Nusee.
"Wuni?" Asked Ruky. "Wuni yana gidan biki dan uwarki. Kinji ba? Nace kin barosa a gidan biki." Kafin Nusee tayi comprehending wani abu Ruky tasa hannu tajawota waje kaman doll baby. Nan Mama ta miqe da gudu tayi wajen ita ma. "Bayin Allah ya da haka, meke faruwa?"
"Ikon Allah" answered Safiyya tana me hararan Mama.
"Ku sake min 'ya meh haka?"
"Ank'i" cewar Ruky tana sake matse rigan Nusee a wuya tana cukuikunawa. Har anan Nusee ta kasa cewa k'ala se raba ido kawai take, ita de ko a mafarki bata ta6a yin gamo da any of them ba, toh me tayi musu?
Ganin Mama ta ibi k'afa zata k'wato 'yarta Safiyya tasha gabanta da sauri "uh-uh-uh Mama tsayawa zakiyi kiji abinda ya kawo mu bawai kiyi mana tashin hankali ba."
"Wasu irin wawayen mata ne ku? Kuma daga ina kuke?"
"A'a fa Mama wallahi ki dasa aya kafin na sauk'e girman danake baki na had'aki da 'yar taki na cii maku mutunci duka" Ruky tayi stating comfortably tare da dawo da kallonta kan Nusee. "Ke kin sanni?" Kaman bazata amsata ba se ta kad'a kai. "Tunda ba alak'a da mahaukata nake ba ina zan ku?"cewar Nusee.
"Ke!!! Ki iya bakin ki wallahi domin bamuda mutunci, se muyi reaping naki naked muci uwarki don laifin dake kanki." Cewar Safiyya.
"Ammatas barni da k'aramar k'waron nan, dama nasan da hakan so bari nayi miki introducing d'in kaina. Suna na Ruky Mama matar Adeel da kike neman aura kin gane?" Se anan hankalin Mama da Nusee ya buga, no wonder.
"Wallahi na zo ne na kashe miki warning da ki fita daga harkan mijina tun wuri, in bahaka ba zaki yaba wa aya zak'inta." Hannu Nusee tasa don kar6e kanta amman ta kasa. "So what dan kece matar Adeel? Mata nawa Allah ya halitta mai da zaki zo kina cemin in fita daga harkansa? You're insanely crazy idan baki sani ba ki sani yau auren Adeel ba fashi." Sake cukuime mata wuyan riga Ruky tayi a yayinda zuciyarta ke tafasa "ke! K'aramar k'waro kamar ki har kinada bakin magana? Toh bari kiji in gaya miki ko shi Adeel nakin bayi min iskanci bale ke" ta jijjik'ata irin nothing as a shell d'innan. "Yadda kike nan kaman lafiya be ishekin nan ba wallahi zama zanyi kan ruwan cikinki sekin harar da hanjin cikin ki, ki iya bakinki ba sa'ar wasar ki bace ni. Mama!" ta kirata tare da dawo da kallonta kan Mama tana rik'e da kwalar rigan Nusee har yanzu
"Naga alaman 'yarki har yanzu bata gama sanin ciwon kanta ba, as her mother nasan ke kinyi. Wallahi warn her, warn her sosai saboda idan ta kuskura ta taka k'afanta a gidan Adeel toh wallahi sede ki sake haifar wata Nuseen dan kasheta zanyi da hannu na, ga k'awata nan kuna iya tambayar ta waya fitar da first wife tasa Zeezee a gidan. Nice nan Ruky Mama, wai ita uwar gidan data fini sanin kan gidan ma kenan bale wannan" ta maido da kallonta kan Nusee. "Wallahi k'ona ki zanyi da kalanzir sekin zamo toka. Kad'an daga cikin aikin Ruky Mama kenan, idan kunne yaji...?"
"Jiki ya tsira" Safiyya ta k'arisa mata.
"Yauwa Ammatas so shawara ya rage wa me shiga rijiya, idan har bawai kin gaji da zaman duniya bane kinason na lahira daga yau bazaki sake kiran mijina ba or else" ta wani turata seda Nusee ta fad'i a k'asa. "Mutuwa" taja layi a wuyanta da hannunta tana mata nuni. "Lets go Ammatas" harara suka bi Mama da Nusee dashi sannan suka fice inda a hanyan fita suka ci karo da geese nasu Nusee, shima Ruky bata barsa ba seda ta kwad'a mai dutse. Wai wannan ma agwagwan gidan ne inaga mutanen gidan?
Da sauri Mama tayi kan Nusee, "Nusaiba are you okay?"
"I am Mama" ta amsa tana mik'ewa da taimakon Mama. "You?"
"I am also, Nusaiba wannan tashin hankali da mai yayi kama? Dama Adeel d'in yanada aure ne?" Kai Nusee ta d'aga a hankali.
"Shine kuma still kikeson ki auresa?"
"Mama bansan matar tasa mahaukaciya bace se yau."
"Yanzu fa? Are you still willing to marry him?"
"Yes Mama auren Adeel ba fashi bazan bari wannan barazanar da tayi ya hanani abinda nayi niyyah ba, inason Adeel."
"Lallai bakida hankali Nusaiba, toh wallahi kiji ki sani idan har ni na tsuguna na haifeki bazaki auri Adeel ko wa yake ba, bakida hankali ne? Kina ganin ko agwagwan nan bata bari ba bale ke? Lallai ya tabbata bakida hankali."
"Kamar ya Mama? Saboda wannan mahaukaciyan sena bar masoyina?"
"Ke baki tunanin wani hali zakisa kanki aciki idan kika auri mijin matar nan? Wallahi yadda tace zata k'ona ki da kalanzir tsab zata iya saboda mahaukaciya ce."
"So be it then."
"So be it? Toh ni ban gaji da ganin kiba wallahi bazaki auri Adeel ba se inde wannan mahaukaciyar ta mutu bata raye, Babanku zan kira in gaya mishi yanzun nan." Tana kaiwa nan tayi ciki inda tabar Nusee tsaye tana aikin kuka. Cikin itama ta nufa inda ta kira Adeel tana kuka sosai, da k'yar ya samu ta tsagaita kukan nata sannan tabasa labarin abinda Ruky tayi mata da Mamanta. Adeel yasan Ruky mahaukaciya ce amman be tsamman haukan nata yakai wannan matakin ba.
"Kiyi hak'uri please Beautiful wallahi I have no idea how she found out about your address, dan Allah kiyi hak'uri ni nasan hukuncin da zan mata."
"Its of no use Adeel saboda Mama ta riga ta rantse inde ba mutuwa taji Ruky tayi ba she aiint letting me marry you."
"Please don't give up on us, let's show them how strongly and deeply in love we are, please Nusee I love you, you remind me of My Zeezee."
"Adeel I don't know what to do ni kaina I am fearing abinda Ruky zata iya min, she's so evil."
"Ki sa a ranki bazata iya miki komai ba se abinda Allah ya k'addara, kibarni da ita I know what's right for her. Ni ke nakeso if it takes me to divorcing her I'll, bana sonta ke nakeso."
"I love you too, just do all you have to do amman de karka saketa, it'll only worsen the situation."
"Kiyi hak'uri please kinji? I'm on my way." Anan ya katse, barin office d'in yayi yaje gidansu Nusee inda seda ta saci idon Mama sannan ta samu ta fito. Hak'urin ya cigaba da bata yana sake jaddada mata shifa ita yake so. Seda ya tabbata she is okay sannan sukayi sallama ya nufi gida zuciyarsa na tafasa sosai. Banging k'ofar yayi tare da sa ma Ruky kira.
"Ruqayya! Ina kike mahaukaciya kawai! Ki fito nace!" Cike da isa ta fito daga d'akinta tana sanye da vest da skirt na atamfa. "Gani wani abu ne?" Isa gabanta yayi "jahilar ina ce ke iyyeh? Level na haukan ki har ya kaiga kije gidan su Nusee kici mutuncin ta kici na mahaifiyarta?"
"Aww wai kana nufin ita shegiyar karuwarkan?" Tayi magana finally.
"Repeat what you just said now" yayi glaring at her.
"Shegiyar kar-" bata idda maganan ba tajiyo sauk'an hannun Adeel tas! A fuskarta, sosai marin ya gigita ta saboda tunda tasan kanta ba'a ta6a marinta ba se yau. Wajen ta rik'e da hannunta bibbiyu tana kallonsa da mamaki. "Ni? Adeel ni ka d'aga hannu ka mara akan wata shegiyar da bata taka kara ta karya ba?"
"An mare kin, kika sake zaginta wallahi sena k'ara miki wani."
"Lallai!" tayi maganan tana sauk'e hannayen nata. "Lallai zakayi nadaman mari na da kayai kaji na rantse wallahi tallahi rantsuwa ba kaffara bazaka auri Nusee ina raye ba, idan kaga ka angwance to Ruky bata numfashi."
"Haka kikace?"
"Eh kuma ka tsaya kaga ikon Allah."
"Me kika isa kiyi? Banza dake ne zaki hanani yin abinda nayi niyya? Toh wallahi ki bud'e kunnawanki da kyau ki saurare ni, idan bakiyi complying hankalinki gu d'aya ba kika nitsu wallahi a bakin auren ki, sakan ki zanyi in huta kema ki huta dan bakida wata amfani mani."
"Hehehe!" Ta sa wata maqirar dariya tana shewa. "Ni zaka saka? LOL this is where you are wrong, Ruky Mama bata sakuwa wallahi ko ka sakeni ba inda zani ina nan a matsayin matarka kuma uwar gidan ka a gidan nan. Nan gani nan bari sadakin bazawara. In fact wallahi idan ka kuskura ka sakeni believe me bazaka so ganin ta'addancin da zanyi wa Nusee ba."
"Me kika isa kiyi mata?"
"Me kuwa? Wanka da acid zanyi mata from head to toe. Idan kuma kana ganin wasa nake try divorcing me ka gani, aikin banza kawai! Warning dana kashe wa Nusee idan har Uwarta tana sonta bazata barta ta aureka ba so shawara ya ragewa me shiga rijiya, koka nitsu mu cigaba da zaman mu kokuwa wallahi kowa ya mutu, don a kanka kowa na iya mutuwa Adeel you are mine and mine alone." Bata jira jin me zai sake fad'a ba ta yi hanyar d'akinta. Ji Adeel yake kaman ya buga mata saki uku take but sanin aljanu da ipiritu na yawo akan Ruky ya fasa dan tsab zata iya tayi ma Nusee wankan acid d'in kamar yadda ta fad'a.
Wani irin bala'i ne wannan? Tun farko daya rufa wa kansa asiri yayi zamansa da Zeezee dake sonsa da duk haka be faru ba. Gashi nan yanzu yaje ya auro abinda yafi k'arfinsa, Ruky tafi k'arfinsa, ina ma ace ze iya sakanta ya huta.
Ba yadda Adeel beyi ba don convincing Maman Nusee amman abun ya gagara. Seda ya kusan giving up sannan Mama ta amince bayan rantsuwan da yayi mata na cewa ba a nan garin Bauchi ze ajiye Nusee ba bayan sunyi aure. A chan Katsina ze kaita where he is sure Ruky batasan kowa ba kuma agun aikinsa ma ze nemi transfer zuwa chan d'in. Bayan komi ya sake daidaita tsakaninsa da su Nusee ne Ruky taji labari akan Adeel na shirye-shiryen yin aure inda taje ta gidan su Nusee ta sake buga wani rashin hankalin fiye da wanda tayi da a baya.
Ruwa ta cika cikin wani white mini galon tajeta gidan su Nusee dashi inda ta ringa ikirarin acid ne undiluted one ma kuwa, and that seta k'ona Nusee dashi. Had'ata da Allah suka rik'ayi ciki harda K'awarta Safiyya da suka had'a baki.
"Wallahi sena k'onaki tukun yaso hukuma ta kamani amman de nasan na lalata miki rayuwa."
"Ruky kiyi hak'uri" cewar Safiyya.
"Nak'i ina ita da uwar nata kunnen uwayen shegu ne dasu wallahi basu sanni bane." Da d'ayan hannunta ta d'ago gallon d'in kaman dagaske dama d'ayan hannunta na rik'e da kwalan rigar Nusee ne, ita kanta Nusee ta gama tsurewa yau, mamanta kam banda kuka ba abinda take. Ganin dagaske Ruky na neman bulbula wa 'yarta ruwan da suka d'au acid ne yasa ta saki ihu sosai stopping Ruky.
"Dan Allah baiwar Allah karki k'ona min 'ya, in harkan mijinki kikeson tafita you have my words ko bayan ranki bazata auri mijinki ba, don Allah karki illata min ita."
"Kunsan da haka kukamin kunnen uwayen shegu wancan karan? Kun d'au wasa nake abee? Zaku ga aiki da cikawa wallahi I'll prove to you both that ba'a wasa da Ruky Mama."
"Ruky don Allah nace karki zuba mata." Cewar Safiyya.
"Kifa bar had'ani da Allah don sena zuba."
"You heard me right wallahi Nusaiba ba zata sake kula mijinki ba." Mama ta fad'a pleadingly.
"Naji daga bakinta tukunah."
"Nusaiba tell her yourself har abada bazaki sake shiga harkan Adeel ba, kin bar mata kayanta." Banza Nusee tayi da Mama hakan yasa Ruky sake matso da gallon d'in ready to shower her with it.
"Ruky please karki zuba mata, zata fad'a don Allah."
"One..." Ruky ta shiga counting "two...-"
"Bazan sake shiga harkan mijinki ba" Nusee ta fad'a a wahalince tana kuka sosai.
"Banji ba ki sake nanatawa."
"Bazan sake shiga harkan mijinki ba, nabar miki abinki har abada."
"In kika kuma fa?" Asked Safiyya.
"Bazama ta sake ba in shaa Allahu" cewar Mama a rud'e.
"K'aramar k'waro kawai Allah ya soki wallahi da kinyi sallama da wannan kyakkyawan fuskar taki yadda ba Adeel kad'ai ba kowani na miji ma seya k'yama ceki." Tureta tayi seda taci karo da bango sannan ta rufe gallon d'in tare da cewa "mu tafi ammatas, a word is enough for the wise." Kuka sosai Nusee tasa da suka fita, itama Mama tana kuka tana lalashin 'yar tata.
****
Da yamma bayan Adeel ya taso daga office ya biya mini mart yayo siyayyan chocolates kaca-kaca ma Nusee. A gaba da gidansu kad'an yayi parking kamar yadda ya saba sannan yayi beckoning mai gadi over da yayi mai Nusee sallama.
"Sede kayi hak'uri Ranka Shi Dad'e."
"Kaman ya fa Baba bata gida ne?"
"Alhj baka da labari ne?"
"Labarin me fa?"
"Abinda Uwar gida tazo tayi d'azu." Ido sosai Adeel ya kwararo waje, "kana nufin Ruky ta sake zuwa nan?"
"Sosai ma kuwa tazo tayi abinda ko a jarida na jima banji anyi ba."
"Innalillahi! Me tayi?"
"Ita da K'awarta..." labarin duk yadda aka yi Baba me gadi ya basa. Wani wutan tsanan Ruky ke ruruwa a zuciyansa ji yake as if yaje ya bugu ya taho yayi mata d'ankaren dukan da seta kwana biyu a asibiti ba tare da tasan inda take ba. Still yak'i yarda da maganan Mai gadi ya d'aga wayansa ya shiga neman Nusee. Sede yayi mata several missed calls duk tak'i d'aukawa ita kanta ta tsorata da actions na Ruky earlier. For the love of herself zata yi hak'uri da soyayyan Adeel.
"Tun ranan da na rabu dake Zeezee na tafka babban kuskure a rayuwana, I miss you so much" k'aramin hauka ne kawai Adeel beyi ba sanadin Ruky yanzu ya rasa two most beloved mata a rayuwansa, gashi yana ji yana gani ba abinda ya isa yayi mata if not tace zata yima Nusee wankan acid. Ba inda yake zuwa kwana biyu banda bar yaje ya bugar da kansa don rage tunanin Zeezee da Nusee, office ma ya yanke zuwa. Yayi hakan na over a week ya soma getting mind nasa back together by resuming office. Tun kuma abinda Ruky tayi masa be sake shiga harkanta ba, girki ma ko tayi bayya ci. Ba ruwansa da ita.
Yau da misalin k'arfe 9:29pm Adeel ya d'au wanka sannan ya fita ba tare da ya sanar da Ruky inda zasa ba. Tun anan jikin Ruky ya bata party zasa, "aiko baka isa ba wallahi." K'awarta Safiyya ta kira "Ammatas please kiyo min bincike akwai inda za'ayi hosting party yau?"
"Ai yanzu haka ma shiri nake akwai wani a Larema htl sannan akwai wani a Zaranda."
"Please do find out for me, wanne d'aya Adeel yaje saboda he just left home now, kwana biyu kaman ya shiryu ashewa am wrong."
"Kai Babe! Baki barin wannan mijin naki fah."
"Yo taya zan barsa? Ina kishin abuna wallahi."
"Toh naji don't worry"
"Yyauwa and also gobe ki sake min confirming idan da akwai party lemmi know please."
"Toh Babe an gama!" Anan tayi hanging. Gabad'aya ta kasa bacci ranan kasancewar ko kwana a gida Adeel beyi ba. Da Asubah Safiyya ke sanar da ita kan taga Adeel a party'n da akayi na nan a Zaranda kuma in bawai wasa idanunta suke mata ba ta gansa da wata chick.
"Chick fa kikace?"
"Wallahi kuwa wata wai ita Xarah."
"Ai kuwa wallahi ze sha mamaki be sanni bane, shi ba wai neme-neme ba? Nikuwa kore-kore ce, Allah yana samunsu ina korarsu har seya gaji ya dena."
"Pwhahhaha kai Babe bakida dama fah."
"Ahtoh bari muga zuwa nan da one week if they are getting along se muyi making move namu amman kafin nan ki nemo min numban shegiya in ajiye saboda tsaro."
"Zuwa anjima toh."
"No prob nagode fa Ammatas."
Washegari wuraren 9:12pm Ruky tayi timing Adeel saboda Safiyya ta sanar da ita akwai wani party tonight. Seda ta bari ya shiga bayi sannan ta shiga d'akinsa ta d'ago keys nasa. Back and front door tabi tasa musu key sannan ta je d'akinta ta 6oye key'n acikin pillow case nata. Tsaf yau ma ya shirya gwanin sha'awa ya fito ready to party. Sede yayita waine-wainen handle, k'ofa bai bud'uwa. Key holder'nsa ya zaro ya shiga neman key'n k'ofar shima babu, "ha'a! Ina key'n ya shiga newai? " D'aki ya koma yayi ta dube-dubensa amman be samu ba. Ta baya yabi nanma same story, jikinsa ne kawai yabasa Ruky is behind this. D'akinta ya nufa direct inda ya tarar a rufe don haka ya shiga bubbugawa. "Ruky! Ruky! Ki fito kibani makullin."
"Kabani ajiya ai dole kace na baka."
"Ki taso ki bud'e k'ofan."
"Dalili? D'akinka ne? Kamar yadda kake korina daga d'akinka nima bazan barka ka shigo min nawa ba" tayi maganan tana buga candy crush a wayarta hankali kwance tayi ruf da ciki.
"Ruky! Kinsan bani wasa dake koh? Ki fito ki bud'en k'ofan am running out of time."
"Time for what? Saboda kaje party kana meeting new girls kana iskanci dasu? Ai wallahi inba wai ta ceiling zaka fita ba, ba inda zaka yau kaji ka sani."
"Ke wai dan k'aniyanki me kika mai dani ne a gidan nan k'aninki ko meh? Don't let me repeat myself ki taso ki bud'e k'ofan nan nace."
"Wallahi bazan bud'e ba." Tuna yanada spare key ya nufi d'akinsa and in a bit ya fito rik'e da key'n, wainawa yayi ya bud'e nan ya sameta tana buga game.
"Ina wasa dake ne? Ina key'n nace?" Yayi maganan moving closer to her. Ko d'aga kai ta kallesa ma batayi ba bale tasan yanayi hakan ba k'aramin haushi ya basa ba, besan a lokacinda ya d'aga hannu ya sake mata mari tas a bayan taba.
"Ai wallahi ka mari banza, dan ba marinka ze sa na baka key'n ba kaji ka sani idan kuma ka sake marina ramawa zan da ba jakar ka bace ni. Idan kaga ka fita daga gidan nan toh gobe zaka fita aiki ne." Ba kalan zagin da beyi mata ba amman tayi mai turning deaf ears don kansa ya gaji ya bari ya koma d'akinsa. Har mak'ora ta kaisa daren ranan haka yana ji yana gani yayi missing party'n and above all yayi missing chance na had'uwa da Xarar sa.
The following day da safe ta bud'ewa Adeel k'ofa sanin zasa office. Haka fa rayuwa ta juya kuma, idan har Adeel ya fita yaga Xarah toh idan an tashi daga office ne kafin ya dawo gida seya biya mata, but any moment yace wai ze fita party da daddare lock Ruky ke sawa ta rufe ko ina.
_If you know you miss MAJ-GEN. MUH'D AL'AMEEN, let Miemiebee see your hands up👆🏾👯 our Legend will be coming back next chapter in shaa Allah_
*MIEMIEBEE. Team #YGC!🎀*
Beeenovels.blogspot.com
👄👄👄👄👄👄
8 comments:
Hands up! Hands up!! I can't wait to see major general is back, sannu da kokari sis, Allah ya kara basira .
I missed him 100%,my hands up 100times
☝☝☝☝☝☝☝☝☝
Enx sis All hands up
My hands are up, I really missed Maj. Gen, Tnk u sis, Allah ya kara basira.
Please we still prefer the older version, please sis change it for us.
OH my Allah, I miss him more than ZeeZee does. hahahaha!!!! can't wait!!!
MIEMIEBEE pls we r waiting...
Post a Comment