BY MIEMIEBEE
PAGE 75
*March, 2017*
Cikin d'an k'ank'anin lokaci ta cinye tas. Shi Al'ameen tsoro ma cin Zeezee ke basa yanzu, just some hours back taci fried rice da kaji yanzu kuma take kukan yunwa.
"Are we good to go?" Ya tambayeta idonsa cike dam da bacci. Kai ta gyad'a a hankali "thank you for being the perfect husband Sweetheart I love you." He was mad kad'an amman jin kalamunta seyaji ya huce. "I love you more" ya fad'a tare da matsowa kusa da ita ya kashe musu wuta suka kwanta.
****
Haka rayuwa ta cigaba da kasancewa seda Zeezee ta kusa haihuwa ta soma d'an banzan masifa da wani irin wawan chi da shan k'ank'ara. Kullum cikin fad'a Al'ameen ke mata data rage ci or else tazo haihuwa zata sha wuya idan ta tashi seta ce mishi ai ba shi ze haihun ba saboda haka ba ruwanshi da ita.
Ga masifa, abu kad'an ta haura sama tayita masifa shi Al'ameen yasan depression na labour ke damunta shiyasa yake binta a hankali koda ta mai masifa seya sak'a mata da love and calming words sekuma daga baya taji kunya tazo tayita basa hak'uri. Tun ana sauran one week due date na Zeezee Al'ameen ya shirya maternity bag nata suka zama ready. Ganin date ya matso kusa fa Zeezee ta shiga tsoro a k'alla a kullum setayi kuka ita tana jin tsoro batason ta haihun kuma.
Tun safe Al'ameen ya fita yau, Zeezee ce kad'ai da Baaba a gida. Yau ma bayan ta gama shan kukanta tayi alwala tayi sallah da k'yar sannan ta d'ibo ice blocks daga fridge ta faffasa tasa cikin bowl sannan tayi d'aki ta zauna kan gado tana sha tana buga game. Tana cikin sha kawai tajiyo muryan Baaba nayiwa Al'ameen sannu da dawowa. Kid'imewa tayi gun gabaki d'aya tama rasa nayi ta wulla bowl na ice blocks d'in k'ark'ashin gado ne ko yaya? Al'ameen ya hanata sha saboda mutane na cewa yawan shan k'ank'ara nasa a haifo yaro da pneumonia ko kuwa asthma. Kafin tace zata miqe ta wulla bowl d'in k'arkashin gado har Al'ameen ya bud'e k'ofan ya shiga. Pillow tayi sauri ta aza kan bowl d'in a tunaninta wai Al'ameen bega bowl d'inba shiko tun shigansa idanunsa sukayi tozali da bowl d'in wanda he is sure k'ank'ara ne aciki.
"Sweetheart sannu da zuwa"
"Yauwa Princess sannu da hutawa."
"Uhn amman bada mota ka shigo ba ko?"
Seda ya k'ariso gefen gado yace, "a waje na sauk'a Abba ze wuce dashi car wash." Ba yabo ba fallasa ya amsatan as if bata yimai komi ba. Ganin yana neman zama kan gadon kuma idan yayi hakan yana iya gano abinda take 6oyewan tace, "karka zauna anan ruwa ya zube." Da sauri.
"A ina?" Ya juya yana kallon wajen.
"Nan." Tayi pointing da yatsa.
"Nan d'inne a jik'e Princess kode kina 6oye wani abu ne?"
"B'oye abu kuma? Me zan 6oye?"
"D'aga pillon muga."
"Babu komi fah Sweetheart."
"Princess k'arya kuma kika soma yimin yanzu? Ba halin ki bane fa, ban san ki da k'arya ba." Sekuma taji ba dad'i.
"I'm sorry."
"Ban hana ki shan k'ank'aran nan ba?"
"Sw-"
"Yes or no?" ya katse ta.
"Yes ka hana."
"Mesa kike sha toh?"
"My Soldier wallahi dad'i yake min idan ban sha ba har wani rashin lafiya nakeji."
Matsowa yayi kusa da ita tare da riqo hands nata cikin nasa "Princess bawai ina son tauye miki hak'k'in ki bane na hanaki shan k'ank'aran, lafiyan baby'nmu zaki duba the more kina shan k'ank'aran nan the more kina exposing d'inshi ko ita the risk na kamuwa da pneumonia ki dena please."
"I'm sorry Sweetheart bazan sake ba."
"Can you promise me?"
"Do I have to?"
"In bakiyi ba bazaki bar shan k'ank'aran ba kenan."
"Toh I promise."
"Sure?"
"Yes ai sauran befi sati ba due date d'ina bazan sake ba anything for My Soldier."
"Thats My Princess tashi ki shirya muje mu siya miki shawarma ko bakiya so?"
"Inaso wallahi."
"Tashi toh mu shirya ki." Da kansa ya ciro mata wani had'ad'd'en dogon riga da hijabi tasa sannan suka fita.
*^*^*^
Dare d'aya Al'ameen da Zeezee suna kwance suna bacci wajajen 11:47pm Zeezee ta farka sanadin ciwon cikin da tun da tasan kanta bata ta6a yin irinsa ba not even menstral cramps. Juyi take so tayi amman dan yadda cikinta yake k'ato tama kasa, ta zauna kuma murd'in cikin baze barta ba. Hawaye kawai ta shiga yi a hankali duk anan kuwa Al'ameen na bacci besan meke faruwa ba, ta tadashi kuma bata so tuna yadda yau ya yini yana training men nasa tasan he must be exhausted. Da k'yar ta iya ta sauk'o daga kan gadon ta tukuikuye kanta akan tiles tana rik'e da cikinta. Tsan-tsan azaba da murd'in da cikinta keyi mata har tambayan kanta ta soma anya kuwa ba mutuwa zatayi ba? Ganin zafin is getting out of hand ta shiga kiran Al'ameen cikin k'aramin murya.
"Ya Al'ameen! Ya Al'ameen!" Shiru be jita ba dake in a low tune take kiransa shi kuwa baccinsa yayi nisa.
"Ya Al'ameen please wake up zan mutu, ka tashi don All- argghhhh!" Ta saki wani irin k'ara wane ana cire wa kafiri rai sanadin murd'awan da cikinta yayi. A firgice Al'ameen ya tashi yana kiran sunanta "Princess!" A cewarsa ma mafarki yake saboda jin sautin ihunta. Ta6a gefensa yayi yaji wayam tashin hankali! "Princess!" Ya fad'a tare da kunna bedside lamb. Har anan be ganta ba dake tana maqe gefen gadon tana ta kuka ba sauti.
"Princess ina kike?" Yayi maganan tare da barin kan gadon.
"Ya Al'ameen" ta furta cikin wani irin murya. Da sauri yayo wajen salati ya saki ganinta kwance k'asa a gun. Da hanzari ya k'arisa ya aza kanta bisa cinyansa yana share mata hawayenta a hankali "Princess what's wrong? Mesa kike kuka haka? Me kikeyi a k'asa?" Hannunta ta aza akan nasa dake kan fuskarta sannan tana kad'a kai tace, "I'm sorry Ya Al'ameen I don't think I can make it saboda mutuwa zanyi."
"Subhanallah! Wani irin magana kike haka Princess? You are not going to die please kibar fad'in haka, cikinki ne ke miki ciwo?" Kai ta gyad'a a hankali ta bud'e baki zatayi magana cikin nata ya sake yimata murd'i. K'ara ta saki nan ma sosai se kuma kuka "I think you are in labor bari insa kaya in d'auko maternity bag naki mu wuce asibiti" yayi stating all confused kwata-kwata ya rasa meke masa dad'i, tun da yake be ta6a ganin Zeezee cikin bad situation kaman wannan ba. Pillow yaja yana son aza kanta akai, "Ya Al'ameen please don't leave me karka barni in mutu ni kad'ai stay with me please."
"Zainab please bazaki mutu ba kibar fad'in haka in shaa Allahu zaki haihu safe and sound kinji?"
"Toh dan Allah karka tafi ka barni you promise not to ever leave my side."
"I am not leaving your side Princess maternity bag naki zan d'auko mu wuce asibiti kinji? Hold still I love you." Kai ta gyad'a a wahalince. Pecking forehead nata yayi ya miqe ya sanya jallabiyansa da sauri sannan yaje ya kira Baaba daga d'akinta ta fito musu da maternity bag d'in.
Seda yayi dagaske sannan ya samu ya d'agata ya sata a mota suka fice asibiti. K'arfe 12-:24am na dare akayi labor room da ita. Al'ameen na tsaye bakin k'ofan d'akin gabad'aya he is out of it besan meke masa dad'i ba again, nayi ma besani ba. Yafi minti ishirin tsaye bakin k'ofan yayi nan yayi chan finally ya zaro wayansa daga aljihunsa har ya shiga kiran Mama se kuma ya fasa kada ya tayar mata da hankali da daren nan sanin ba wanda ze kawo ta asibitin a yanzu tunda ba driving take ba ita. Mama Babba ya kira right away wanda seda call d'in ya kusa yankewa ta d'aga.
"Hello Al'ameen da daren nan Allah yasa lafiya."
"Mama" kad'ai ya furta sounding sad and worried. Tuni Mama Babba ta miqe zaune jin yanayin muryan d'anta. "Subhanallah Al'ameen lafiya dai ko? Kayi magana don Allah ina kake yanzu?"
"Mama Zainab ce." Yadda yake magana mutum na iya imani yana kuka ne tsan-tsan tashin hankali.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Meya sameta Al'ameen? Meya samu Zeezee?"
"Mama she is dying and ba abinda zan iya mata, labour'n ta yayi hitting."
"Kuna asibiti ne yanzu?" Tayi maganan sounding relieved kad'an cause at first ta d'au ma ko mutuwa Zeezee tayi.
"Eh."
"Ka kwantar da hankalinka kaji? Shi dama labor haka yake, kata yi mata karatu kawai su ayyatul kursiyu d'innan in shaa Allahu zata sauk'a lafiya kaji?"
"Mama am afraid I don't want to lose Zainab."
"You won't lose her Al'ameen trust me okay? Ka nitsu ka yimata karatu sosai nima zan tashi nan inyi sallah mu rok'a mata Allah, Allah ya sauk'e ta lafiya."
"Toh Mama thank you."
"Ka kira Hajya Hafsah ne?"
"A'a banason in tayar mata da hankali se idan naga abin nason fin k'arfin Doctors d'inne se in kirata."
"Kayi tunani me kyau Allah ya sauk'ar da Zeezee lafiya."
"Ameen."
"Ka kwantar da hankalinka kaji? Zeezee zata sauk'a lafiya in shaa Allahu."
"Toh Mama Allah yasa, thank you duk abinda akwai I'll let you know."
"Yauwa Son semun sake magana." Ahaka sukayi sallama. Leqa ta windown d'akin ya gwada yi amman ba abinda yake gani sema k'aran ihun Zeezee dayake ji. Ji yake kaman yayi kuka there is his Princess suffering, fighting for her life shi yana tsaye anan doing nothing. How he wish ze iya kar6an mata pain d'in yaso se shi yayi suffering.
Safa da marwah ya shiga yi wajen ya zauna ya nitsu yayi mata karatu kaman yadda Mama Babba ta fad'a mishi ma ya kasa. Ana cikin haka ne aka bud'e k'ofan d'akin da Zeezee ke ciki. Da sauri ya miqe ya sami nurse d'in.
"Nurse how is she please? How is my wife?"
"Still no improvement."
"Please is she going to make it?"
"Idan har kana TARE DA ITA, yes. She needs you inside mu shiga daga ciki please." Ji yake kaman yace mata baze iya ba saboda baze iya sauraron sautin kukan Zeezee ba standing beside her and doing nothing, on the other side kuma tuna ya ta6a d'aukan mata alk'awarin cewa he'll always be by her side harta labor room nata yada yayi manning up kawai.
"Muje please Sir tana jiran ka tak'i pushing wai se kana kanta tukuna." Hanky ya zaro a pocket nasa ya share gumin dake ta kan k'eto masa sannan yabi bayanta suka k'arisa ciki. Kallo d'aya yayi wa Zeezee ya kawar da kansa baya jin ze iya sake sata a ido gumin da take had'awa ko wanda ke cikin oven albarka.
"Ya Al'ameen" ta kira sunansa cikin wani irin sauti. "Ya Al'ameen please don't go don't leave me." Guiwa ba k'arfi ya k'arisa kan gadon nata tare da rik'e hannunta d'aya cikin nasa duka yana pecking kai "shhh! Am here Princess am never gonna leave your side." Hanky ya zaro next ya share mata gumin nata tas sanna yayi pecking forehead nata tare da fad'a mata, "we are in this together Princess I love you so much morethan you can ever imagine."
"Ya Al'ameen bazan iya ba, please forgive me."
"You can do this Zainab because am here with you, we are in this together kinji?"
"Try pushing okay? " Cewar Dr Sammy dake expecting baby.
"I can't I can't please do something Ya Al'ameen." Zeezee ta fad'a tana hawaye.
"Yes you can Zainab, you can just do as yadda Dr ta fad'a kinji? Ke kad'ai kike da ikon kawo mana Little soldier'nmu into life and I trust you push okay am here for you."
"I can't Ya Al'ameen zan mutu its too painful."
"I know Princess and kina k'ok'ari ma sosai just push kinji koda so d'aya ne I love you, after the count of three sekiyi pushing. Ready?" Kai ta gyad'a da k'yar bayan data gama 6ata musu lokaci. "Okay, here we go 1... 2... 3 push!" Aiko tak'i pushing d'in ita tana jin tsoro se kuka take. "Princess you have to push if not Little Soldier'n mu baze fito ba fah."
"Ya Al'ameen I can't I feel like am dying, I need some air please." Wani file yaja a gefe ya shiga yi mata fifita dashi a yayinda take ta jan numfashi. Ya mata na kusan 2 minutes tace she is okay, "so zakiyi pushing yanzu?" Da sauri ta kad'a kai "I can't."
"Yes you can, ko kin manta matar wacece ke Princess? Matar Soja ce fa, matan sojoji kuma kuma ba ragwaye bane ko bakison kiga Little Soldier'n mu muga da wa yake kama?"
"Ina so."
"Good you have to push then." Kai zalla ta gyad'a mishi.
"Zakiyi for your Soldier?" Nan ma kai ta gyad'a "thats My Woman so after the count of three okay? One... two... three!" Pushing d'in tayi da iya k'arfin jikinta har seda jijiyoyin goshinta suka bayyano. "Wayyoo! Zan mutu" Tasa k'ara bayan pushing da aka samu tayi. "I can't I can't Ya Al'ameen ni kubarmin baby na aciki kawai I can't force him out kuka ce senayi kashe ni zakuyi kubarmin shi a ciki na yafe ganinsan." Sosai d'ayan nurse d'in ta tsaya da dariya yau tana ganin labor kam.
"A bar shi kuma Princess? Taya za'a barsa yi hak'uri ki sake pushing." Kai tayi saurin kad'awa tana kuka ita a miyar da ita gida, abu fa kaman wasa Zeezee tayi pushing tak'i. Su Dr Sammy basu ta6a ganin abu haka ba, daga k'arshe ma tsayawa sukayi daga gefe suna k'are ma Zeezee da Al'ameen dake ta faman calming nata yana rok'anta da tayi pushing kallo. Sun yi morethan 30 minutes suna abu d'aya Al'ameen nata rok'onta da tayi pushing da k'yar finally tayi agreeing to push anan suka marmartso. Fiye dana d'azu ta sake wani push d'in, nan kam har Dr Sammy ta soma ganin kan baby'n, se kuma yanzu wani sabon azaba da zafin labor ya sake hitting Zeezee.
"Ga baby's head nan two more push in shaa Allah ze fito push again kinji Zainab?" Dr Sammy tayi information tana murmushi.
"I can't ni kubarni please kun d'au pushing d'in wasa ne? Ni Mama nakeso nasan ita bazata ce in yi pushing in kashe kaina ba, kaima Ya Al'ameen ban zata mugu ne ba kai se yau, Allah ze sak'a min ba pushing da zan sake in kashe kaina ni ku kira min Mama." Kuka take sosai tsakanin ta da Allah. K'us-k'us nurses suka shiga dariya jin wannan kalamu na Zeezee.
"Naji kuma na yarda ni mugu ne Princess amman yi hak'uri ki sake pushing ko sau d'aya ne."
"Nak'i bazan yi ba ni ka fita min daga d'aki mugu kawai" ta rushe da kuka. Yasani sarai she don't mean any of those words azaba ne kawai yayi mata yawa. "I am here with you Princess I am never leaving your side."
"Just go I don't love you anymore ni Mama nakeso, duk kaine wallahi bazan sake kwanciya dakai a d'aki d'aya ba." Dariya sosai har Dr Sammy ta tsaya yi.
"Toh naji Princess amman yanzu yi hak'uri kiyi pushing."
"Ni Mama nakeso kuma ka sake cemin push zan ja Allah ya isa."
"Princess you don't need Mama, kema Maman kanki nefa bakiji Dr tace taga kan baby'nki ba? Push a bit seya k'arisa fitowa yi hak'uri."
"Ni Mama nake so" ta sake rushewa da wani kukan.
"Breathe Zainab you can do this." cewar wata nurse "idan kikayi pushing baze baki wahala ba." Wani d'an banzan kallo Zeezee ta bita dashi "Inba hancin ki kikeso in ara inyi nishin ba kan bansan wani irin nishi kikeson iny- arghh!" Wani irin rik'o tayi ma Al'ameen sanda faracunta suka tsattsaga mishi skin, "labor'n ya sake hitting" cewar Dr Sammy "Maj-Gen ask her to push idan muka ci sa'a tayi yanzu baby'n na iya fitowa."
"Push kinji Princess? Yi hak'uri Mama na zuwa na mata waya."
"Argghhh! no please I can't."
"Yes you can in bakiyi ba Mama ain't coming fa." Sake gangamesa tayi which in the process take yak'ushinsa sosai gabad'aya hannunsa ya tashi shima da rabon labor'nsa, danne zafin yayi sanin tana cikin more pain. "I hate you Ya Al'ameen wallahi Allah ze sak'a min tunda shi ba azzalumi bane" ta k'are maganan cikin kuka sosai.
"I know Princess ni kuma I love you push okay?"
"Bazan yi ba mugu kawai."
Haka suka ta drama cikin labor room d'in tayi pushing tak'i. A takaice seda tayi wasting another 20 minutes sannan da k'yar Al'ameen ya iya convincing nata tayi pushing. Da tayi da k'arfi da an wuce gurin yanzu amman dake raguwa ce kad'an tayi pushing hakan yasa only rabin kan baby'n ya fito they need one more push. Kafin Zeezee tayi one more push d'innan su Dr Sammy sunji jiki barin ma Al'ameen da har k'odewa yayi ga yak'ushin da Zeezee keyita masa, hannunsa gabad'aya ya 6aci da shati ga uwa uba masifa da zagin data shiga yi masa bashi kad'ai har Dr Sammy ta samu share nata.
_4:19am_
After all the struggles, cries and screams Zeezee tayi pushing one last time da iya k'arfin jikinta suuul Dr Sammy ta jawo baby. Wani irin relieved sigh Zeezee ta saki ji take kaman ansa mata sabon rai, like dama iska na blowing haka shine take ta had'a gumin nan? Se yanzu tama soma jin fresh air'n dake hurata tun d'azu ta d'au a oven na gasa biredi take.
"You did it Princess!" Al'ameen yayi alerting nata sounding delighted he can't believe baby'nsu Dr Sammy ke rik'e da. "Wow we have a bouncing LITTLE SOLDIER here" tayi informing nasu tare da juya musu baby'n suna kalla, se wani mammatse jikinsa yake yana tukuikuye kansa gu d'aya wane me jin sanyi. Butt nasa Dr Sammy tad'an buga wanda hakan yasa sa sakar da k'ara which was damn adorable. "Awwwwn! He's so cute Sweetheart." Zeezee ta furta tana kallon Little Soldier'n ta she cant believe that wannan d'anta ne "congratulations Maj-Gen and wife, bari a shirya shi a kawo muku, amsa Nafeesa." Dr Sammy ta fad'a tare da miqa wa nurse dake gefenta ita kuma ta fice. A nitse Zeezee ta dawo da kallonta kan Al'ameen "you did it Princess" ya sake fad'a mata fuskansa d'auke with the most expensive smile.
"I couldn't have done it without you My Soldier, I love you."
*MIEMIEBEE. Team #YGC!🎀 ZAIMEEN Flames🔥🔥🔥*
Beeenovels.blogspot.com 👄
3 comments:
Tnx a lot sis, Allah ya kara basira. More grease to ur elbow
Tnx a lot Allah ya kara basira, amma kamar kin tsallake page daya
mmmmmm enx sis
Post a Comment