Wednesday, 15 March 2017

‘YAR GATA CE!

   BY MIEMIEBEE
PAGE 65
March 2017




    _Here's to third page of dedication My Special Star ⭐️ AUNTY SIS, my love for you is like tears from the sky thanks for everything._



      Washegari bayan sallan Azahar Lovebirds d'in suna zaune a parlour suna shak'atawa. Zeezee ta kwantar da kanta bisa cinyan Al'ameen suna kallon sports. Chan ta juyo tana kallonsa, "Princess wani abu ne?" Ya tambayeta.
  "Ya Al'ameen dagaske yanzu this week zaka koma?"
   "Princess haven't we talked about this? Kiyi hak'uri nima fa ba son tafiyan nan nake ba."
  "Toh ka fasa mana."
  "Its not possible they need me."
  "And I need you also."
  "Princess am here for you ain't I?"
 "For the time being ba, wai ma aurenka suke ne da zamu na sharing time naka. Ni wallahi banaso, you are mine alone."
 "Princess who says am not yours? Am yours alone Kiyi hak'uri kinji? I won't take long zan dawo."
  "Bawani nasan ka tafi sena sake ganinka ne" tana kaiwa nan ta fice zuwa d'akinsu. Kuka ta shiga yi a rayuwa bata son abinda ze nisantar da ita daga Al'ameen nata. Tana cikin rera kukan taji hannunsa akan bayanta, ignoring nasa tayi sema dad'a k'arfin kukan nata da tayi.

   "Princess why are you punishing me like this? Yanzu da gan-gan kike wannan kukan ko sanin banaso." Banza dashi tayi se kukan take. Zagayowa yayi ta gaban ta da wuri ta gwada juyawa wanda tuni Al'ameen ya rik'o face nata. A hankali ya d'agata tare da zaunar da ita, "I'm sorry kinji? Nasan kina hak'uri but ki k'ara, its never my wish to leave you all by yourself." Hawayenta ya share mata da hannunsa, hugging nasa kawai tayi "not a tear again please Princess." Da k'yar ta danne kukan sannan ta d'ago daga jikinsa tana kallonsa. Kallo d'aya ya mata ya gano tana buk'atar mijinta ne, shikuwa duk abinda take so shi zeyi mata. Ba k'aramin dad'i Zeezee ta jiyo ba ganin yau bata nemi Al'ameen ba amman ya biya mata buk'atar ta.

***
   Da La'asr bayan sun idar da Sallah Zeezee taje ta samu Al'ameen dake miqe kan gado ta kwanta a gefensa, "Sweetheart?"
  "Yes Princess."
  "Am bored mu d'an fita please, tunda kazo ba inda muka je."
  "Ina kikeson muje?"
  "Ko ina ni ka kaini." Matso da ita jikinsa yayi "bari zuwa 5 haka yanzu mu d'an huta kinji?" Kai ta gyad'a mai a hankali sannan ta aza kanta bisa k'irjinsa "I love you Ya Al'ameen, you are My Everything."
    "As you are to me also Princess lets get some nap." Daga nan duk sukayi shiru inda a hankali bacci yayi gaba dasu. 5:20pm Al'ameen ya tashi, a hankali ya raba jikin Zeezee daga nasa sannan ya fad'a bathroom yayi wanka ya shirya sannan itama ya tada ita. Cikin k'ank'anin lokaci duk suka shirya sunzo fita Zeezee ta kalli Al'ameen a marainace.

  "What is it Princess?"
  "My Soldier kullum ne bodyguards nakan nan se sun raka ka duk inda zaka?"
  "Why? What is it?"
  "I want us to go out just the two of us, be the one to drive us."
  "Is that what you want?"
  "Yes Sweetheart."
  "Toh chill, your wish is my absolute command. Ahmad and co, ku koma posts naku I'll be the one to drive today."
   "With all due respect Sir we are being assigned to guard you anywhere you go." Ahmad yayi explaining.
   "And my wife says no, she wants me to drive her today, any question?"
 "No Sir" cewar Sadeeq a tare sukayi saluting nasa suka ja baya. Dad'i sosai Zeezee taji ganin yadda da zaran tacewa Al'ameen ga abinda take so yake kwatanta yi mata.
   "I love you Sweetheart" ta fad'a tare da pecking nasa a cheeks nasa, murmushi ya mata sannan da kansa ya bud'e mata motar ta shiga "thank you My Soldier."
   "You're most welcome Princess."
   Su biyu abinsu suka fita yau ya kaita shopping daga chan suka wuce Ice Cream shop ya saya mata sannan suka dawo gida.

     A daren ranan da Al'ameen ze koma Abj Zeezee ta shirya masa akwatinsa tsaf sede komi sime-sime takeyi, don bata son ya tafi ji take as if tayi faking rashin lafiya yace ya fasa tafiyan. Daren ranan Al'ameen keta shisshigewa Zeezee itako se basar dashi take ta na nuna mai bata so badan komi ba kuwa don yasan she is not happy ze tafi ya barta gobe ne. Shiko yasan halinta sarai bayan tafiyansa tana iya kiransa ma tace koda ze tafi be bata hak'k'inta ba yasa yak'i hak'ura yata binta har seda yayi turning nata on daman yasan she can't ignore him. Sosai ya gamsar da ita daren ranan making he forget all of her problems.

   Da Asubah yau tare ma sukayi wankan sannan sukayi Sallah, Zeezee bata koma bacci ba kasancewar flight na Al'ameen 8am ne. Chores nata ta gama ta yi musu breakfast sannan taje ta tada Al'ameen yayi wanka. Kallonta yake tayi tun da suka idar da Sallah yau take ta faman had'a mishi rai. She couldn't hold her tears back anymore a lokacin da Saje yazo ya fita da akwatin Al'ameen. Juyawa tayi da suri zata wuce d'aki inda ya rik'e hannunta restraining her. "Princess in duk wani tafiya na zakina kuka haka ya kikeson ina ji a jikina? Gani nake like ni ke saki kukan." Ya fad'a cikin zazzak'ar muryansa a hankali.
 "Ba kai bane Ya Al'ameen just go."
  "I can't leave you kina kuka haka."
 "Ya Al'ameen I don't want you to go" tayi maganan cikin kuka sosai, bending yayi a hankali yayi owning lips nata be barta ba seda yaji tabar kukan da takeyin. "I won't take long zan dawo in shaa Allah kinji?" Kai ta gyad'a a hankali hannayenta dake cikin nasa ya d'ago yayi pecking both sannan back to her forehead, cheeks, nose, jaw and neck by now dariya take sosai.
   "Thats My Woman don't cry again okay?"
  "I won't, go hurry don't be late." Har bakin mota ta rakasa seda taji driver ya kunna motar kuma taji bazata iya ba, a guje ta ruga ciki ta baje kan gado tana kuka sosai. Shima Al'ameen ji yake as if ya fasa tafiyan, layinta ya shiga dialing wanda tana ganin call d'in amman ta kasa d'agawa tsan-tsan kuka. Agun bacci 6arawo ya saceta ba ita ta tashi ba se bayan Azahar, a hankali ta nufi bayi tayi alwala ta yi Sallah sannan ta d'ago wayarta inda ta tarar da countless missed calls na Al'ameen so take ta kirasa amman bata jin zata iya saboda tasan how infectious jin muryansa ke a gareta, yanzun seya sake sata sabon kuka. Layin Lubiee kawai ta kira wanda tayi picking immediately.

   "Ya tafi kenan?" Abinda Lubiee ta soma  tambayarta. Rai a dak'ule Zeezee tace, "wa?"
   "Wa kuwa inba Soldier'n mu ba."
  "Mschww!" taja tsuka.
  "LOL" Lubiee ta k'yalk'yale da dariya "my question has already been answered. Ai dama na sani, se idan mijin naki ya tafi kike neman mutane."
   "Lubiee wallahi zanci k'aniyanki akan haushin dake damuna yanzu."
  "See me see wahala! Tell me Babe meya faru?"
  "Bansani ba." Tayi maganan tana murgud'a baki wane Lubieen na gabanta. "Easy mana Babe meya faru ne?"
   "Ya Al'ameen ya tafi."
  "Ahaap! Ai dama na sani, wato ke se in Ya Al'ameen Ya tafi ne zaki tuna dani ko? Nima am busy, tun yaushe nake trying numbernki bai shiga, sede inta ganin story'n ki kina posting pics and vids na Ya Al'ameen na miki magana still shekaran jiya a snapchat d'in kika k'i replying."
   "Babe ba haka bane, bazan iya raba hankalina bane idan Sweetheart d'ina na gida, I need to take care of him closely kamin wasu shegu chan a waje su min gaba da abuna."
  "Tohhh su masu Sweetheart manya nima am busy, saurayi na na jira na a waje."
  "Wallahi Babe kika katse wayar nan sena ci k'aniyanki banason tsiya."
  "Akwai wanda ya kaiki tsiya ne? Sheggur kawai."
  "Uhm niba wannan ba kina gida ne yau?"
  "Wai zuwa zakiyi?"
  "Eh."
  "Hehe Amaryar Ya Al'ameen, ba'a ganinki se mai gida bai gari."
  "Mschww! da alama fad'a kikeso muyi nama fasa zuwa gidan naku zani gun Mama."
  "Yi hak-" karap Zeezee ta katse wayan abinta. Bata kaiga ajiye wayan ba taga video call na Al'ameen na shigowa. Kaman bazata d'aga ba se kuma taga ya bata tausayi tayi picking tare da juya ma wayan baya yadda baze ma iya ganin fuskarta ba.

    "Thanks Gee!" Ya furta "thanks for picking up Princess." Shiru tayi not ready to talk, "Princess baki hak'ura ba?" Still shiru. "Okay lemmi go down on my knees." Da sauri ta juya "no please don't."
  "Princess mesa kike min haka ne? Kuka kikeson in soma yi neh?" A hankali ta kad'a mai kai "look up at me, yi hak'uri ki kalleni am already missing your eyes on me."
  "I miss you more" tayi maganan finally tana kallonsa. "Shhh! Don't cry again kinji? I love you so much."
   "I love you more Sweetheart."
   "Princess please nan gaba don't punish me like this, sau nawa nake kiranki baki d'aukawa."
  "Its because I don't wan to listen to your voice."
  "But why?" Ya tambayeta cike da mamaki, "is my voice that bad."
  "Oh God no! Kai kanka kasan muryanka ya fiye min komi dad'in sauraro a duniyan nan."
   "Then mesa kika k'i picking?"
   "It is infectious to me, muryanka ba k'aramin affecting d'ina yake ba Sweetheart."
  "Hakane princess?"
  "Sosai kuwa Sweetheart"
   "Toh da ana changing voice da nayi."
   "See you, kai baka san voice naka ba d'aya daga cikin abubuwan da nakeso a tattare da kai ba? Your voice is damn sweet."
    "Just like yours."
  "Uhm yauwa My Soldier ni zan koma gida gun Mama kafin ka dawo."
  "Bakiya son zama ke kad'ai ko?" Kai ta gyad'a a shagwa6ance, "in ni kad'ai ne I keep on missing you."
   "I'm sorry Princess se ki koma gun Mama before in dawon I don't want you to be feeling lonely."
   "I am lonely already Sweetheart, I miss you bansan ya zan cigaba da rayuwa before ka dawo ba."
  "Haba Princess! We'll always keep in touch ai, we are in touch already."
  "Se waya da video call kawai can I hug or kiss you? Ko kuma zaka iya bani hak'k'i na ne ta wayan?" Tayi stating rai a dak'ule.
  "I know that's not possible shiyasa nake baki hak'uri Princess."
  "Ni bana son hak'urin ka kai nakeso, hak'k'i na nakeso."
   "Don't worry zan dawo soon enough in baki hak'k'in ki Princess nima kuma in kar6i nawa."
  "Ai naka is available all the time nine de abar tausayi." Dariya sosai ta basa, "aww dariya ma nake baka? Ai abar a tausaya min d'ince ga miji but when am in need of him baya nan, akwai abin tausayin da yafi wannan ne?" Da k'yar ya iya ya tsagaita dariyan nasa amman ya kasa magana.

   "Eh kayita min dariyan."
  "I'm sorry Princess" ya fad'a murmushin fuskansa na bunk'asa. "Princess Ji yadda kike magana fa as if rabuwan ki dani irin months d'innan ne."
  "Ai kaman months d'inne a minute without you is like a thousand days to me."
  "Haba Princess" yayi frowning face nasa. "Jiya-jiya ma fa we..." se yayi shiru.
  "Toh yau kuma fa? Gobe fa? Ni wallahi bazan iya ba I need you" ta k'are maganan as if though zatayi kuka.
 "Princess the more kike cewa bazaki iya ba the more bazaki iyan ba, yi hak'uri kinji? Yi hak'uri Princess kije gida gun Mama."
 "Eh saboda ka samu more reason to stay in Abuja ba."
 "Oh God Princess! Toh shikenan kiyi zaman ki a gida."
  "Saboda inyi ta missing naka ba? Dad'i kake ji idan kaji nace am missing you."
  "God help me" ya fad'a tare da dafe goshinsa. "Do whats suit you toh."
   "Saboda you don't care ba no problem zanje in samu Mama."
   "Wai Princess senayi miki kuka tukun zaki san ina missing naki over ne? Kisani I miss you more fah, kawai bana nuna miki ne saboda bana son ki shiga damuwa." Sekuma ya bata tausayi.
   "Toh I'm sorry."
  "I should be the one who's sorry, kinyi hak'uri?"
  "Nayi My Soldier ai baka laifi." ta fad'a tare sakar mai da murmushi.
  "Thats My Woman so zaki gun Maman ne?" Kai ta gyad'a "okay toh in kinje ki gaishe min da ita kinji?"
  "I'll."
  "Yauwa Princess I love you okay?"
 "I love you too" tayi mai blowing kiss.
  "Take care of yourself for me."
  "I'll semun sake magana" tace dashi tare da katse vid call d'in.

   Akwatinta ta shiga shiryawa wanda tana gamawa ta kira Mama don sanar da ita da zuwanta. Abinda Mama ta soma tambayarta ne ya mugun bata mamaki. "Ya tafi kenan?" Sak abinda Lubiee ta tambaya itama, shiru Zeezee tayi mamaki kwance a kan fuskarta "kin min shiru nace ya tafi kenan?"
  "Mama-"
  "Baki amsani bafa Zeezee." Ta katse ta.
  "Eh ya tafi." Ta fad'a a hankali.
  "Ba shakka, se in Ya Al'ameen yayi tafiya ne kike sanin sauran mutane suna raye koh?"
  "Mama me kike fad'i wai?"
  "K'aniyanki duba wayanki missed calls nawa na miki?"
  "Mama yaushe?"
  "K'aniyanki nace, ace ata kiran mutum bayi picking waya! Aljannah kike bawa Maj-Gen d'inne?"
  "Mama kinsan bai cika zama ba, idan ya dawo kuma... kuma..."
   "Kuma akace ki dena picking calls ba."
  "I'm sorry, ina yini?"
  "Lafiya ya mijin naki?"
  "D'azu da safe ya wuce."
  "Ayyah, ya gida toh?"
 "Alhamdulillah ya Ya Omar?"
  "K'alau yake."
  "Uhm Mama nace zan zo gida."
  "Lafiya dai ko?"
  "Eh lafiya, Ya Al'ameen ne yace zan iya zuwa saboda ze d'an jima wannan tafiyansan kinga nima sena d'an leqa islamiyya."
   "Toh ba matsala kina iya zuwa."
  "Toh gani shigowa."
  "Yauwa sekin zon." Ahaka sukayi sallama. Tsaf ta d'au wanka ta koma gida inda ta sauk'a a d'akinta, sharewa tayi, tayi mopping da kuma 'yan goge-goge sannan tayi joining Mama a kitchen suka had'a dinner. Bayan Sallan Maghrib ta had'a wa Omar dinner'n shi kan table takai mishi site nasa. Knocking tayi a hankali ya buk'aceta data shigo. Akan centre table ta ajiye masa "sannu Zeezee thank you."

  "You're welcome Ya Omar, me kakeyi haka?"
  "Aiki am about to finish though."
  "Ohh!"
  "Yeah, me ya kawo ki gida kuma?"
  "Sweeth-" da sauri ta ko6e bakinta "sorry I mean Ya Al'ameen yayi tafiya kuma ze jima wannan karan yayi suggesting inzo nan."
   "Oh baby sis manya, su Sweetheart."
 "Kai Ya Omar halin kannan na nan deh."
  "Me za'a fasa? Ya kike toh?"
  "Lafiya ya aiki?"
  "Alhamdulillah."
  "Kizo ki zauna mana kinyi tsaye achan sekace soldier, ko auran Soldier'n yasa kema kika fara aikinsu?" Murmushi ta saki sannan taje Gefensa ta k'arisa ta zauna "wai kai Ya Omar yaushe zaka kawo mana sister in-law namu?"
   "Very soon Mama bata sanar dake bane?"
  "Nahh."
  "She did mana ranan tace min ta kiraki."
   "I think maybe shine lokacinda ban d'auka d'innan ba."
  "Yauwa!" Yayi exclaiming "wai ma ina kike ajiye wayanki ne? I called you also kusan sau biyu baki picking."
  "Ya Omar bazaka gane bane."
  "Ohh wato in mijinki na gari baki da time na kowa se nasa abee?"
  "Eh mana" ta amsa tana murmushi as if Al'ameen na gabanta.
 "Da kyau kin ko yi missing, se bikin ya matso zakisan amaryar."
  "Haba mana Ya Omar."
  "Don't even beg me."
  "Kar ka fad'an zan rok'i Mama ta gayamin."
  "Ai nace mata karta sanar dake thats your punishment." Ta bud'e baki zatayi magana wayan Omar dake kan table ya shiga ruri kafin tace zata duba wake kira har ya d'aga amman sede taga picture Identity na wacce ke kiran kamar tasan ta, wacece toh?
   "Hello Babe, I'll call you later ina tare da talkertive d'innan yanzu, I love you." Da sauri ya kashe gudun kar Zeezee ta jiyo muryan Babe tasan.
  "Toh yanzu dan rashin mutunci nice talkertive d'in Ya Omar? Kuma ma tsaya kaman nasan Babe nakan nan. D'an samin hotonta ingani please."
  "Ai kaman na miki revealing identity nata kenan."
   "Tsaya ma wallahi na santa, Lubiee ce?"
  "Lu waye?" Yawani yamutsa fuska "wace Lubiee kuma?"
  "Lubiee my best friend."
  "Omg!" Yasa dariya "you expect me to date your friend haba! Wuce nan ai."
  "To wacece?"
  "Bazan fad'a ba."
  "Ma wallahi itance kaman pic nata na gani tanada same pink mayafin nan."
  "Silly reason, Lubieen taki kad'ai ce me Pink veil?"
  "Ba ita bace amman-"
  "Abeg Zeezee free me, ni ba abinda ze kaini dating friend naki to talk more of marrying her."
  "Toh wacece please ka gayan."
  "Nak'i." Rok'onsa tatayi amman yak'i sanar da ita, se kusan to 10 sukayi sallama ta koma site nasu da Mama, she really enjoyed spending time with Omar. D'akin Mama tajeta inda ta tarar da ita tana waya da Ibraheem.

  "Mama please ki bani wayan idan kun gama" ta fad'a alokacin da ta zauna gefen Mama. Wani dirty look Mama ta bita dashi "pleaseee" ta maraice fuska "inason inji ya takwarata take ne." Seda su Mama suka gama hirarsu da Ibraheem sannan ta miqa wa Zeezee wayar. "Halo Ya Ibraheem."
  "Mara mutunci ba."
"Kaman ya mara mutunci Ya Ibraheem?"
  "Eh mana kin ta6a d'aukan waya kin kirani kinji ya takwararki take ne tunda Ya Al'ameen naki ya dawo dake d'akin ki?"
  "Laaa Ya Ibraheem ba haka bane wallahi, takwara na kullum tana raina na bawa Ya Al'ameen sak'o ma yakai muku yau ya wuce Abj shima."
  "Toh ya kike?"
  "Lafiya ya Aunty Fatee, Maamah da Sweetheart d'ina?"
  "Lafiya k'alau takwaranki se kuka gabad'aya ta ramar min da Fateemah ta."
   "LOL nide takwarana na sani a kula min da ita, da Aunty Fatee ta yaye ta da seku kawo min ita hutu."
   "Uhm, hakan za'ayi nakega idan aka yayetan."
  "Yauwa ka gaishemin da Aunty Fatee."
  "Toh zata ji goodnight."
   "Sleep well" ta katse wayan. "Ashe shima baki ta6a kiransa ba" Mama tayi maganan tana mata wani kallo.
  "Mama ba haka bane fa."
  "Naji toh ficemin a d'aki bacci nakeji."
  "Yauwa Mama da Allah wace matar da Ya Omar ze aura?"
  "Aiko ban fad'a, yace kar na fad'a miki tunda ya kiraki musamman don sanar dake kika k'i d'agawa."
  "Mama please mana" nan ma rok'an Mama tata yi amman Mama tak'i sanar da ita haka don dolenta takona d'akinta inda ta watsa ruwa ta haye gado ta kwanta tare da kiran Al'ameen nata suka ta hira har seda ta fara gyangyad'i.

***
   Life moved on, rayuwar Zeezee a gida na mata dad'i sosai sede be kai mata kaman idan TANA TARE DA Ya Al'ameen ba. Da safe zatayi duk kan ayyukan daya kamata da yamma kuma ta wuce islamiyya. A weekends kuwa ta d'auko Ramlah da Ummie. Ita da Al'ameen nata whenever they are less busy suna kan video or audio call, a kullum dad'a fad'uwa tarkon soyayyan juna suke.
   Sati uku Al'ameen ya d'auka amman bayi ma zancen dawowa nan fa hankalin Zeezee ya tashi ita ta gaji she wants him back. Yau da daddare bayan ta kwanta ta kirasa suka gaisa sannan take tambayarsa yaushe ze shigo.
   "Princess har zama gun Mama ya isheki ne?"
  "Eh mana ni zama da kaine kawai bayi gundira ta."
  "Uhm toh Princess ki k'ara hak'uri kinji?"
  "Ya Al'ameen kullum shikenan ni cikin hak'uri, rabo na da kai fa 3 weeks akwai hak'urin daya fi wannan neh?"
  "Babu Princess amman ya muka iya? Haka schedule na job d'ina yake."
  "Ni toh ka fasa aikin mana, am not after your money Sweetheart am after you, kai nakeso kuma ko a talaka kake ahakan zan cigaba da sonka."
  "LOL I know Princess amman thats not possible kema kinsani ai, I'll see zuwa next week idan zan iya shigowa."
   "Nasan ma ba shigowan zaka yi ba kar ma nasa rai nazo na zama disappointed."
  "I'll make it up to you Princess I promise."
  "I hope you do, I love you."
  "I love you too, get some sleep kinji?"
  "I'll and you too seda safe."
  "Allah bamu alkhairi" yace tare da katse wayan.




*MIEMIEBEEE.     Team #YGC! 🎀 *
  Beeenovels.blogspot.com
👄👄👄👄👄👄

4 comments:

Unknown said...

Tnx sis, more grace to ur elbow.

Unknown said...

More grace to ur elbow swthrt.

Unknown said...

Abin mu dasss, Ya Ibrahim and Lubeeyn Zeezee. Wai wai wai, Allah ya kara basira sis, more grease to ur elbow.

Unknown said...

I'm too eager to see the next post, still waiting for the next page sis. Allah ya kara basira, Allah kuma ya bar mu tare.