Sunday, 12 March 2017

'YAR GATA CE!

   



*BY MIEMIEBEE*
Page 63
  March, 2017




   _yAs I promised Sweetheart, AUNTY SIS. 5 consecutive pages will all be dedicated to you because you morethan deserve it. No need for long essay because the love is always there, I love you💋 Here's to page one of dedication._





   "Ya Al'ameen, you are nothing compared to Adeel" ta fad'a a fili amman kuma a hankali. "You are not after my body, bazan iya tuna when last muka kwanta da Adeel be nemi hak'k'insa a guna ba, he is just after my body, but you?" tayi maganan tana sake matsowa kusa dashi as if zata shiga cikin cikinsa. "You are not like that, you love me for who I am and nothing more, nad'au this night zaka ce zaka nemi hak'k'inka ashe am mistaking love isn't about sex, love is all about sacrifice and wanting for your spouse what you want for yourself, I love you Ya Al'ameen." Daga nan ta rufe idanunta tajira bacci yayi awon gaba da ita.

   Ko wani Asubah Zeezee na tashi amman banda na yau. Tun da take tana ganin bata ta6a samun peace and tranquillity acikin bacci ba kaman na yau, Ya Al'ameen is just like an Angel to her. Asuban fari Al'ameen ya tashi, ji yayi gabad'aya nauyin mutum akansa, da k'yar ya iya ya miqa hannunsa ya kunna bedside lamb don yadda ta danne sa nan yaga Princess nasa tukunkune a jikinshi tana takan bacci. Hannunta d'aya ta ya6a akan cikinsa ta zagaye dashi, d'aya kuma ta kama collar riganshi da shi tana bacci. He can't get enough of her innocent face, tsayuwa yayi gun yana kallonta, yaushe har ta matso this close to him amman be jita ba? Ganin lokacin Sallah na iya wucesa idan ya biye wa kallonta yasa a hankali ya sauk'e hannunta dake rataye a cikinsa without waking her up. D'ayan hannunta data kama collar rigarsa ne ya kasa cirewa don yadda ta kama gagam.

   K'ok'arin rabawa yake amman ya kasa har seda Zeezee ta tashi in the process. A hankali ta bud'e idanunta ta aza akan kyakkyawar fuskarshi dake nan wane ba daga bacci ya tashi ba. Murmushi ya mata wanda itama ta miyar mishi tare da ja baya kad'an don ta karanci tashi yakeson yayi.
  "I'm sorry" ta furta a hankali.
   "What for Princess?" Yayi maganan tare da barin kan gadon.
  "For being a burden to you last night."
  "You weren't Zainab, last night was great I had a wonderful sleep barin yi alwala." Kai ta gyad'a masa sannan ta bisa da kallo har seda ya shige bayin. Just kawai ta tsinci kanta tana murmushi ita kad'ai ba gaira ba dalili har Al'ameen ya fito bata sani ba. Bak'in Jallabiya yasa sannan yayi gyaran murya "uhm-uhm." Anan ne hankalinta ya dawo jikinta, "good morning My Soldier."
   "Morning My Princess tashi kiyi alwala kiyi Sallah nima zan wuce Masjid."
  "My Soldier can I ask of a favor please?"
  "Sure My Princess ina jinki."
 "Kayi Sallah a gida yau please."
  "But why?"
 "Inason ka jani Sallah one last time kafin kayi tafiyan."
  "Shikenan abinda kikeso?" Kai tayi nodding a hankali, "toh tashi kiyi alwala am waiting for you." Bata tsamman ze amince so easily haka ba, "dagaske Ya Al'ameen?"
  "What My Princess wants she gets it." Dad'i sosai taji ta miqe ta shiga bayi, after a while ta fito ta tarar da Al'ameen rik'e da hijabinta.

   "Gashi sa" yace da ita, wani irin murmushi me sosa zuciya ta sakar masa sannan ta miqa hannu zata kar6a, se ji tayi yaja hannun nata a hankali ya matso da ita kusa dashi sannan ya shiga sanya mata hijabin a hankali, ita ko duk anan ta kasa d'aga eyes nata daga kan shi se kallonsa take cike da adoration. "Can we pray now?" Ya tambayeta. Kai Ta gyad'a mai, "thank you for everything Ya Al'ameen, I love you." Smiling zallah ya mata sannan ya shiga jansu Sallah, wane Sudeis haka take jin muryan Al'ameen idan yana raira Al~Qur'ani. Koda suka idar da Sallan ji take as if tace masa su sake yin wani, bata gajiya da jin muryansa. Sun gama Azkar nasu suka koma suka kwanta kasancewar flight na Al'ameen na k'arfe d'aya ne there's nothing to rush about. From each bed end suka kwanta, "My Princess" ya kira sunanta a hankali.
  "Na'am" ta amsa tare da juyowa tana facing nasa, hannunsa taga ya bud'e mata as if though ya karance mind nata   she can't tell how much she wants to be close to him all the time. Ba tare da 6ata lokaci ba ta matso tare da shigewa jikinsa, rufeta yayi da hannunsa making her feel more at home. "I love you My Soldier."
   "Shh! Sleep okay?" Kai ta gyad'a a hankali daga nan wani baccin ya sake yin awon gaba da ita, Haka Al'ameen ma.

   As early as 9am Zeezee ta tashi, har anan Al'ameen ko bacci yake yi, kallonsa ta tsaya yi sannan a hankali ta zame jikinta daga rungumar daya mata without waking him up. Pecking (light kiss) nasa tayi a cheeks nasa sannan ta mik'e ta nufi kitchen ta shiga had'a musu breakfast. Bayan ta gama ta koma ciki tayi wanka tasa wata royal red gown nata me strapless arm tare da applying light makeup. Sumarta ta taje tayi oiling tayi packing into a bunny style sannan ta k'arisa kan gadon da Al'ameen keta bacci adorably har yanzu. Zama tayi a gefensa tana tunanin ya za'ayi ta tadashi, chan ta kai hannunta kan fuskansa dai-dai kan whole na dimples nasa tasa yatsarta tana wasa dashi, ganin yak'i tashi har yanzu ta sauk'o zuwa light red lips nasa ta shiga bi a hankali da yatsanta, tayi hakan sau uku ana hud'u Al'ameen ya shiga bud'e idanunsa. Murmushi ta sakar ganin plan nata has worked out, yana gama bud'e idanunsa ya fara cin karo da face na Zeezee dake d'auke da beautician smile ever! "Morning My Handsome Soldier" ta mik'a tayi pecking nasa a cheeks nasa. Kallonta kawai ya tsaya yi full of wonder and adoration. "Tashi muje kayi wanka, breakfast is ready."

   "Princess?" Yayi magana finally.
  "Na'am My Soldier."
  "You are looking ravishing."
  "Thank you Sweetheart tashi ko in d'aga ka ne?" Dariya kad'an yayi "can you?"
   "Ma dariya kake? Wait and see." Mik'ewa tayi ta shiga jansa da hannunsa, nishi take sosai tana faman jansa amman ko motsi baiyi se faman dariya yake mata chan ya mik'e da kansa wanda a sanadin haka ta fad'a jikinsa "oops! Am sorry" tayi maganan tana neman tashi daga kan cinyansa.
  "I told you bazaki iya d'agani ba."
  "Maybe saboda ban karya bane banida energy yanzu."
  "Baki yarda ba still kenan?"
  "Eh mana, you are My Baby after all tashi kayi wanka." Mik'ewa yayi at a time, hannunsa ta rik'e sannan ta kaishi har izuwa bakin k'ofan bayin, "your towel is inside, seka fito." Murmushi kawai ya iya mata saboda he can't explain how much he loves her. Kafin Al'ameen ya fito daga wanka har Zeezee ta ciro mishi three quarter wandon da zesa da kuma T shirt me pattern na sojoji. Yana bud'e k'ofan ta d'aga kai tana kallonsa, packs nasa precisely daga bisani tace, "come over Sweetheart" tayi mai nuni da gefenta. Bece komi ba ya k'ariso ya zauna gefenta, "ga cream naka ko in shafa maka?"
  "Haba Princess am I a baby? Zanyi da kaina."
  "Yes mana, you are My Baby, toh shafa ina jiranka." Zama tayi tana kallonsa wane TV ba abinda yafi tafiyar mata da imani like how muscles nasa suke motsawa, suke going up and down idan yana shafa man. Yana gamawa ta mik'a mai kayansa tare da basa privacy. Timing nasa tayi a dai-dai lokacin daya gama sa kayan ta dawota d'akin sannan tajasa izuwa dining table tayi serving nasa. Suna karyawa tana yimai hiran soyayya kala-kala.

    Wajajen 12noon Al'ameen yasa Saje ya fito mar da akwatinsa, tun anan fa mood na Zeezee ya sauya, bata son tafiyarsa saboda she don't wanna miss him. 12:15pm Al'ameen ya shirya tsaf cikin uniform nasa, Zeezee na zaune akan gado fuskarta ba walwala ko kad'an. Har gabanta ya k'ariso sannan ya miqa mata hannunsa nufin tayi grabbing, kaman da baza tayi ba se kawai ta sa nata ciki, a nitse ya mik'ar da ita. "My Princess why the sad face?"
  "I don't want you to go" ta fad'a sincerely.
   "And why?" Kai ta d'ago tana kallonsa "because I don't wanna miss you Ya Al'ameen, it's infectious to me." Ta k'are maganan wane zatayi kuka, "shh! Don't cry please, we'll keep in touch Princess, kuma ai ba tafiya zanyi kwata-kwata ba maybe nan da 2 weeks na dawo." Kuka kawai tasa, "har two weeks Sweetheart ? Kuma shima maybe ne? Ya kake so in rayu ba kai Ya Al'ameen?"
   "Bana son ganin kukan nan" hannu yasa ya share mata hawayen nata, "in shaa Allah in two weeks time zan dawo."
  "Promise me Ya Al'ameen."
  "I promise Princess." Hugging nasa tayi tana me cigaba da kuka "I love you so much Sweetheart, please don't take long ka dawo kaji?"
  "Naji Princess I won't in shaa Allah but first kibar kukan nan."
  "I can't." Lalashinta yayi tayi har seda tayi shiru sannan ya d'agota daga jikinsa, "smile toh." Kai tayi saurin kad'awa, "please mana Princess I badly need that smile."
  "I badly need you also."
  "I love you Princess, I love you so much." Dad'i sosai taji wanda bata san lokacinda ta shiga smiling ba, "thats My Woman!" yayi exclaiming duban rolex agogon hannunsa yayi yaga its getting to 12:30 ga flight nasa 1pm ne. "I should get going" hannu yasa a pocket nasa ya zaro bundle na N100 "gashi ki rik'e wannan."
  "Nayi me dashi My Soldier?"
  "Ki rik'e incase any needs arises."
  "Yayi yawa, balle ma I don't need any cash, komin da nake buk'ata akwai keep your money kaji?"
  "I insist ki kar6a ba fata ba but something bad might happen to you buk'atan kud'i kuma yayi rising."
  "Toh ka rage yayi yawa."
  "Princess bana son muna musu" akan gado ya wulla mata "gashi, se munyi yawa toh, I love you make sure you take care of yourself kinji? You are free to go anywhere you want na baki izini saidai don't stay late at night, okay?" Yana kaiwa nan ya sauk'e hannunta dake cikin nasa a hankali sannan ya juya, be kaiga fara tafiya ba Zeezee da hawaye ya cike dam a idonta ta kama hannunsa tare da juyo dashi.

    Lips nasu kawai tayi crashing akan na juna ta shiga kissing nasa with all that she got not minding a sh*t. Hannayenta ta zagaye a wuyansa, kissing him the more a yayinda shi kuma a hankali ya zagaye hannayensa a tiny waist nata tare da bending height nasa kad'an giving her more access. Moving in sync with each of her move yake, he didn't make any move rather following nata kawai yake. Sun d'au tsawon lokaci a haka sannan a hankali Zeezee ta sake shi tare da hugging nasa gam-gam wane za'a k'watan mata shi. "I love you more My Husband, you are the most sweetest thing that has ever happened to me. Allah ya kare min kai ya kaika ya kuma sake dawo min da kai lafiya, safe and sound. Allah ya raba ka da dukkan wani sharri da masu sharri, may you live long and prosper, your Wife and also your Princess loves you way much." Hugging nata back yayi yana me sake jin sonta na shigansa, "ameen My Princess thank you so much." A hankali ta raba hug d'in sede har yanzu bata sake kallon cikin idonsa ba, ita kanta bata d'au zata iya kissing nasa as how she did ba, atleast kissing him was worth it, his lips are sweeter than that of Adeel's. "You should go kar kayi missing flight naka" tana fad'in haka ta juya mishi baya da wuri don bata son yaga kalan hawayen da takeyi, shima he can't take her crying anymore kuma yasan muddin ya cigaba da tsayuwa anan kukan ze cigaba da sata, "I love you Princess" yayi whispering mata sannan ya fice.

   Wani kukan ma se da taji an tada engine na motan Al'ameen. Bajewa tayi kan gado tana kuka sosai wane zata cire ranta, never once have she ever imagined that she'll love Al'ameen like this. Sam ta kasa dena kukan, drawer'n gefenta tasa hannu ta zaro wedding album nasu nan ta bud'e ta shiga viewing tana me sake wani sabon kukan, a haka ne har bacci 6arawo ya saceta. Se kusan after 2pm ta tashi tayi alwala tayi Sallah ta kuma ci abinci. Wayarta ta d'aga don kiran Al'ameen inda ta tarar da two missed calls nasa, take tayi calling back wanda shima se a karo na biyu ya d'aga kasancewar bai kusa.
  "My Princess" ya fad'a cike da k'auna.
  "Na'am My Soldier" se kawai memory'n how tayi kissing nasa ya soma dancing a kanta, kissing him was the best feeling ever.
  "Nad'au kinyi fushi dani ne ai."
   "Ai baka laifi bale nayi fushi da kai Sweetheart, how was your trip?"
  "Alhamdulillah kin bar kukan yanzu ko?"
  "Nabari but I'm missing you already."
  "I know and me either, kinci abinci?"
  "Eh kai fah?"
  "Also, meh kikeyi yanzu?"
  "Babu, yanzu na idar da Sallah."
 "Princess se pass 2 kikeyin Sallah, why?"
 "Ba dagangan bane I slept over shiyasa bazan sake wasa da Sallah ba."
   "Yauwa Princess, I'll be heading to a meeting yanzu, take care okay? I love you."
  "I love you more." Kiss ta mai blowing a wayan "muahh." Yana murmushi sosai yace, "thank you" tare da katsewa. Through out a gida Zeezee ta yini, waya da Lubiee kawai suka tayi kafin ta kwanta around 10pm ta gwada layin Al'ameen inda ta mai har two missed calls be d'aga ba kasancewar kansa yayi zafi da aiki. Taso jin muryansa kafin ta kwanta amman hakan be yuwu ba don haka ta mai sending message as follows,
    _My Handsome Soldier, just called to check up on you before going to bed, my bed is empty without you. Your Princess miss you badly, take care I love you._ takai 10mins rik'e da wayan tana jiran reply nasa amman shiru don haka kawai ta kashe wuta ta kwanta.
   Ba Al'ameen ya sake sa wayansa a ido ba se 12am dayazo kwanciya missed calls nata da text mssg ya tarar, har ya shiga dialing numbanta amma ganin pass 12 na dare kawai ya katse yace ze bari se gobe kar yayi interfering wa baccinta. Da Asubah bim ake sanar dashi zasu koma Abuja, tafiya ba shiri gabad'aya ya mantar dashi da kiran Zeezee daya keson yi, itako batayi zuciya ba dukda rashin calling nata back da Al'ameen beyi ba ta sake yi mai wasu two missed calls d'in yau da safe had'e da good morning text message. Aiki ne sosai ya rik'e Al'ameen se a daren ranan ya samu time na kansa, baccin bala'i yake ji amman yasan he needs to hear from his Princess ya take. Kiranta yayi har kusan 3 missed calls amman tak'i d'auka by now tayi zuciya itama.

   Facetime Video call ya shiga mata wanda shima se kusan a karo na uku ta d'aga, nan ma k'eyarta ta juya mishi wai baze kalli face nata ba tunda yake shareta haka.
 "Haba Princess turn mana."
  "O'o" tace still backing him, "missed calls nawa na maka se yanzu kaga daman kira na, kasan yadda hankali na ya tashi kuwa?"
  "Princess am sorry give your Soldier a chance to explain kinji?" Nanma kafad'a ta buga "please Princess I want to see that beautiful face" yayi maganan tamkar zeyi kuka jin haka ta juyo da wuri, anan ya samu daman kallonta shima, fuskarta na d'auke da light makeup "wow! You are looking spectacular, I'm missing you Princess."
   "Nasan nice kawai ke missing naka, kaida tunda ka tafi sau d'aya ka kirani."
 "Princess kema kinsan I won't do that on purpose." Explaining komi dallah dallah yayi mata wanda ta fahimce sa sosai itama ta kuma basa hak'uri game da saurin fushin da tayi. Lovey-dovey hira suka ta sha seda taga Al'ameen na gyan-gyad'i sannan ta barsa ya kwanta. Kaman yadda ta saba tun tafiyarsa, yau ma ta d'auko shirt nasa ta sak'ala a hancinta tana shaqan daddad'an turaren jikinsa har tayi bacci.

   Haka kuma rayuwarsu ta cigaba da kasancewa anytime Al'ameen is less busy ze kira Zeezee ko yayi mata video call suyita hira, a kullum dad'a son juna suke barin ma Zeezee da take ganin bazata iya rayuwa idan ba Al'ameen ba. Idan ta gaji da zaman gida se ta leqa gida chan gun Mama kokuwa gidansu Lubiee, last weekend ta d'auko su Ramlah suka taya ta yin weekends.
   Yau ne cur two weeks da Al'ameen yace zeyi ya cika, tun jiya Zeezee ta kasa samun sukuni she can't wait for today, da safe yau ta kirasa bayan su gaisa sun gama gaya ma juna how much they miss each other take tunasar dashi batun yau fa yace ze dawo. Anzo gurin yace a ransa domin yasan dawowansa wannan satin ma baze yuwu ba balle wai yau, shine kaman babba yanzu manya biyu zuwa ukun da suke gabansa duk an sauk'e musu aiki shi ke komi, its damn hectic.
  "Hello Sweetheart kayi shiru fah."
  "Princess." Daga yadda ya kira sunanta ta gane he can't make it.
  "Princess I'm so sorry." Kuka kawai yaji tasa ta cikin wayar, "Ya Salam! Princess please cut it out, kukan me kuma kike? Ya isa please, I'm sorry I can't make it this week kiyi hak'uri kinji? Aiki ne yamin yawa."
  "Its okay" kad'ai tace masa sounding disappointed sarai yasan its not okay kawai ta fad'a ne.
   "I know its not kiyi hak'uri kinji? I miss you also."
  "Shikenan."
  "Princess you are still mad, I can sense it."
  "Am not" ta k'arya tasa.
  "Tell me you love me if you are not toh." Shiru tayi danko she is really mad d'in, ta gama sa rai yau ze dawo kuma yace aiki ya rik'e shi? Bata so haka ba. Hak'uri yata bata da k'yar ya samu ta hak'ura suka ta6a hira kad'an sannan yayi excusing kansa. Mama Babba ta kira suka gaisa sannan Hjy Sadeeyah.

   Sati uku Zeezee ta kwashe bata sa Al'ameen nata a ido ba in bade Video call sukayi ba, she miss him so much. A ranan daya kamata ya shigon ma be samu dama ba, kuka Zeezee tayita mar da suke Video call bayan daya sanar da ita cewa he can't make it ranan. Ba irin hak'urin da be bata ba amman tak'i hak'ura haka tayi mai fushi bata sake kiransa ba.
   Hakan ba k'aramin damun Al'ameen yake ba, squeezing time nasa yayi sosai ya samu ya zak'ulo hutun sati d'aya zuwa biyu haka wanda yak'i sanar da Zeezee yana son suprising nata. Ko ya kirata yanzu bata zagewa tayi mai hira as before shiko bai gajiya da bata hak'uri, se daya k'ara three more days akan actual date daya kamata ya dawo sannan ya samu ya kammala abubuwan da yake gabansa. Zuwan bazata yayi mata ko kad'an be nuna mata a yau ze shigo gari ba.

   Tun tashiwar Zeezee yau tayi wanka ta gama ayyukanta ta kwanta a parlour tana kallo, chan da kallon ya isheta tayi tunanin zuwa gidansu Lubiee. Tsaf ta shirya ta fice, da misalin k'arfe uku Al'ameen ya shigo gari, 3:30pm dot ya masa a gida, ciki Saje ya shiga masa da akwatinsa. Ganin ba motan Zeezee Al'ameen ya tambayi me gadi inda yake sanar dashi just now ta fita gidan k'awarta Lubiee amman tace she won't take long. Kai yamai nodding sannan ya shigo ciki inda ya tarar da ko ina tsaf ba dotti ga kuma k'amshin turaren wuta, kayan jikinsa ya rage ya watsa ruwa ya fito parlour yayi zamansa. Around 4:30pm Zeezee ta dawo gida inda tayi parking daga waje-wajen parking lot shikuma driver can cikin garriage yakai motan Al'ameen hakan yasa Zeezee bata gani ba. All exhausted ta bud'e k'ofa ta shiga ta sake miyarwa, mutumin data gani zaune akan kujera a gabanta ne ya mugun bata mamaki tare da jefata cikin wani irin farin ciki.
  "Ya Al'ameen!  My Soldier!" Tayi exclaiming sunansa unbelievably. Miqewa yayi a nitse yana sanye da vest da free sized black sports trousers. Hannunsa ya bud'e mata "My Princess" ya kirata cikin zazzak'ar muryansa.  Yasar da handbag natan tayi ta ruga a guje taje tayi hugging nasa.




*MIEMIEBEE.     Team #YGC!🎀*
  Beeenovels.blogspot.com
👄👄👄👄👄👄

No comments: