Friday, 3 February 2017

‘YAR GATA CE!

BY MIEMIEBEE
PAGE 39
Febuary 2017



   Nan da nan Sadeeyah ta kira Mama as a matter of urgency kan ita da Baba suzo yanzu-yanzu, ta fad’i ko lafiya kuma tak’i. Cike da tashin hankali Mama ta kira Baba yana d’agawa tayi stating, “Alhj kana ina yanzu?”
   “Ina hanyan zuwa kasuwa ne, lafiya?” Ya amsa.
  “A’a wallahi ba lafiya ba ka juyo yanzu Sadeeyah yar Maj-Gen ta kirani kan ita da Mamansu suna gari suna gidan Zeezee haka wai we are needed urgently.”
  “Subhanallahi! Allah yasa de k’alau to gani nan zuwa.”
  “Yauwa kayi sauri please.”

***
   “Mama you are not doing this.” Al’ameen yayi maganan still not believing abinda ke gudana.
  “Ka tsaya kaga aiki da cikawa.”
  “No Mama please drop all this Hjy call them back kice musu su fasa zuwa ni banason tashin hankali, let Zeezee be eventually zata zo tayi learning truth, yarinya ce har yanzu.”
  “Yarinya fa kace Al’ameen? D’an yaron shekara d’aya ma ya iya ya tantace dad’i da rashinsa sekace min zank’aleliyar mata kaman Zainab batasan ya kamata ba? Wallahi k’arya ne raba auren nan za’ayi kowa ya huta ba yadda za’ayi ka kai yarinya Hajj ta tsaya tana maka wannan iskancin.” Ta fada rai a b'ace.
  “Ai Mama ban fad’a miki bane har mota ya sai mata kuma karki d‘au wai k’aramar mota ce, sak irin nasa Ford Jeep d’innan ya sai mata.” Hjy tayi stating.
  “Karki gayamun Sadeeyah!” Exclaimed Mama.
  “Wallahi gashi ki tambayesa, kuma ina da tabbacin ita tace se kalan nashi takeso.”
   “Al’ameen kalleni, kalleni nace!” Ta tsawata masa a hankali ya d’ago kai yana kallonta “ya kukayi da ita?” Shiru yayi not ready to talk, “aww bazaka gayamin ba kenan? Kode asirce ka matar taka tayi?”
  “Mama ni bata asirceni ba, wai ina baki hak’uri bazaki hak’ura ba yanzu? Please kuyi dropping maganan nan I beg of you please.”
  “Kanason in sa6a maka koh? inba asirce kan tayi ba then mesa bakason aga fault nata? Ina maka tambaya bazaka amsani ba? Nace ya kukayi da ita?!”

   “Tace tanason kalan mota na ne inda hali na sai mata thats all bawai forcing d’ina tayi ba.”
  “Lallai yarinyan nan batada kunya, Allah kawo iyayen nata.” Mama tayi maganan unbelievably.
  “Ameen” Sadeeyah ta amsa.
  “Mama please inhar kina sona call them back kice su fasa zuwa, zamu iya mata gyara within us base mun sa iyayenta ciki ba, karmu had’a kanta da parents nata please.”
   “Kai abinda ke damunka kenan? Kaji na rantse yau se an raba auren nan billahillazi.”
  “No Mama please dan Allah don’t do this to me, karki raba aurena da Zainab you know how much I love her.”
  “But she doesn’t love you Al’ameen zuciyarta bata tare da kai kadena wahalar da kanka akan wacce is not worthy of your love.”
  “I believe in US I believe wataran al’amura zasu daidaita tsakani na da ita, its just a matter of time.”
  “Time? Yau da bikinku watanni nawa? Beyi hud’u ba?”
  “Yayi sosai Mama” cewar Sadeeyah “in beyi biyar bama kenan.”
  “Akwai time dayafi wannan ne? watanni biyar da aurenku ko 6ari banji ‘yar nan ta ta6a yiba kome dalili ban sani ba.”
  “Mama wannan kuma wace irin magana ne? Haihuwa kam bana Allah bane?” Al’ameen yayi saurin tararta.
  “Wai Al’ameen in haifeka sannan kake tunanin zaka iya min wasa da hankali? Nace meye dalili?”
  “Nima ban sani ba gaskiya.”
  “Lil Bro why defending her? ‘yar nan ba sonka take ba, she don’t deserve you, she isn’t worthy of your love. Mama wallahi koda nazo kwanaki ba a d’aki d’aya suke kwana ba and that means ita ta koresa daga d’akin tunda batason basa kanta, can you deny it?”
  “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Al’ameen! Amman da hankalika kuwa? Mahak’urci mawadaci amman naka hak’urin yayi yawa, Sadeeyah tell me this not true.”
  “Wallahi it is Mama gashi ai seyayi denying inhar k’arya nake”
   “La’ilaha illallahu! Ni Ameenah naga duniya, kai! Amman da hankalinka kuwa? Ka biya sadakin yarinya sannan tak’i baka hak’k’inka kuma still ka tsaya kana farinta mata rai da gifts? Are you that stupid Al’ameen? What is wrong with you? Dakai nake magana!” Tun daga nan Al’ameen ya kasa fad’in komi again, kansa ya sunkuyar ayayinda masifan Mama da Sadeeyah keta scattering masa k’wal’kwalwa take ciwon kai me tsanani ya rufesa.

*~ *~ *~
   In less than 30 minutes su Mama suka sa iso hankali tashe, gaisuwa sama-sama sukayi da Mamansu Al’ameen. “Hajiya you called for us ina fatan lafiya?” Cewar Baba. Zanin Mama Al’ameen ya shiga ja da nufin dan Allah tayi shiru amman ta fisge zanin nata.
   “Inason kafin mu fara komi ku kira min Zainab awaya ko wala Allah zataji magananku ku iyayenta ta dawo gida tunda ta saba fita bada izinin mijinta ba.”
  “Mama please thats enough” Al’ameen yayi pleading a hankali amma kota kansa batayi ba
  “Hajiya ban fahimci inda kika dosa ba” Baba yayi maganan with bewildered look on his face, Mama kanma kasa cewa komi tayi.
  “With time zaka fahimta Alhj, amman nafison ayi komi a gaban Zainab kada kuce sharri akeyiwa ‘yarku.” Tuni ran Baba yahau tafasa waya ya zaro daga aljihunsa a fusace ze kira Zeezee sanin halinsa Mama ta sauk’e hannun nasa “a’a Alhj kabari na kirata da kaina dan Allah nace.” Kai kawai ya gyad’a mata yana wani irin zakin nishi.

  ** _After a while..._
   “Hello Zeezee?”
  “Na’am Mama ina kwana?”
  “Lafiya qalau nace kina ina ne? Ki dawo gida yanzu gani na zo.”
  “Toh Mama I’m on my way.” Tana ajiye wayan tayi sallama da Hajar. Zama shiru sukayi wajen ba wanda ya sake cewa komi seda suka jiyo k’aran bud’e k’ofan Zeezee tana maida k’ofan ta juya taga biggest suprise of her life, idanunta na tozali dana Baba ta tabbatar tana cikin babban tashin hankali yau, meke faruwa? Me tayi? Wayyo nata ya k’are.
  “Kinyi tsaye akan mu bazaki k’ariso bane?” Cewar Baba harshly. Jiki na rawa ta k’arisa parlourn tare da zama a k’asa daga wani angle, cikin sauti me rawa ta shiga gaidasu sede kowa ya amsa banda Baba, nan fa cikin Zeezee ya sake d’aukan ruwa.
   “Masha Allah, Sadeeyah kiyi ma Saje (one of Al’ameen’s soldiers) magana.” Cewar Mama Babba. In a minute taje ta taho da Saje, cike da girmamawa yabisu duka da gaisuwa babu kaman yadda ya gaishe da Al’ameen. Shi kansa Al’ameen is confused me kuma yasa za’a kira Saje acikin family matter’nsu? Bade su Sadeeyah sun had’a baki dashi ba yana kai masu rahoto a kullum ba?

   “Good ina son dukkannin ku nan kubani aron kunnuwanku wannan” tayi nuni da Zeezee da tuni cikinta ya sake tsabagen rud’ani “Zainab ce matar Al’ameen d’ana. Inason Alhj kaida Hjy Hafsah ku kalli Al’ameen ku kuma kalli Zainab ku gayamin inji cikinsu waya k’ara weight bayan aurensu da akayi wanda ke neman watanni biyar.”
  Mama kad’ai ce ta d’aga kai ta kalli Al’ameen banda Baba dake ta bin Zeezee da dirty look tun beji dalilin dayasa aka tarasun ba yasan rashin hankali tai. Se anan Mama taga kalan fad’awan da fuskan Alameen yayi whereas Zeezee kuma ta k’aru, ita daman tasan Zeezee na bawa Al’ameen wahala proof ne kawai batada.
   “Hjy its crystal clear Al’ameen ya fad’a ba laifi.” Mama ta fad’a finally.
  “Good base na sake nanata muku ba, you guys are aware yaron nan ya kai Zeezee hajj koba haka ba? Kuma inba wai yana sonta bane baze ta6a asaran sama da miliyan biyu akanta ba am I right?”
  “Hakane sosai ma” Mama ta amsa ayayinda Baba ya gyad’a kai “Al’ameen na son Zainab sonda bana tsamannin akwai d’a na mijin da zeyi mata irinsa. Tun da nake da Al’ameen ban ta6a ganinsa acikin damuwa ba se alokacinda yakeson Zainab, abun mamaki anan shine kalan abubuwan da Zainab take yima Al’ameen d’ina har yasa ya zube haka, tun bayi bin abin a zuciya har ya fara damunsa wanda ba haka nasan Al’ameen d’ina ba kaima Alhj kasan halinsa tunda kuna zumunci.”
  “Sosai Hjy ki gayamin me wancan ‘yar iskan tayi.” Cewar Baba.
  “Alhj calm down dan Allah inma zakayi mata fad’a kabari se munje gida” Mama tayi maganan yadda Baba kad’ai ya jita.
  “Abubuwan da tayi kuma take kan yi suna da yawa tunda ta samu Al’ameen me hak’uri take iya son ranta a gidan nan, tunda akayi musu aure bata ta6a aza mai girki yaci ba, tana fita bada izininsa ba, be ta6a gaya mata magana tayi ba gar da gar take zaginsa tana gaya mai magana iya son tanta, bata ta6a had’a kwanciya dashi ba ga kuma wayan da  takeyi kullum da sauarayinta wai shi sunansa Adeel, yanzu haka fitan ta yau Al’ameen baida masaniya. Mota tace se irin wanda yake hawa takeso haka yaron nan ya sai mata amman ta saka mai da butulci irin wannan? Don ita yaro na gabad’aya ya zube ya sauya kamanni, it isn’t fair! Just recently taje taci bashin 500k gun k’awarta badon komi ba don ta 6atawa Al’ameen suna a gari, haka tasa k’ananun yara wanda basu kai ba suka zo suna gaya mai magana iya son ransu kan ya bari matarsa tana cin bashi a waje wanda ba haka bane. White gold na ‘yar nan be 6ata ba tamai k’arya ya 6ata haka ya sai mata sabo ta samu ta siyar da tsohon toh ni wallahi gaskiya ina raye bazan bari a cutar min da d’a ba. Na kiraku nan ne badon komi ba se dan ayita a gabanku ta k’are am cutting off this marriage Al’ameen baze cigaba da zama da Zainab ba tana cutar dashi tunda daman ba sonsa take ba tanada saurayinta wanda takeso as said.” Ta k’are maganan anger na building within her.
   “Inalillahi wa inna ilaihi raji’un!” kad’ai Mama da Baba ke ambata, they are both totally speechless wannan rashin hankali dame yayi kama? Tun auran Mariam da Yasmeen in-laws nasu basu ta6a kiransu suka masu magana akan halayensu ba se Zeezee da dududu auran ta befi watanni biyar ba? Gabad’aya Zeezee ta kasa cewa ko uffan wajen all she knows is that nata ya k’are dan yankata Baba zeyi tun anan ta shiga rera kuka a hankali. Al’ameen kuwa tun da Mamanshi ta fara magana bece ko uffan ba infact tunda su Mama suka shigo ya gaishesu be sake d’aga kansa ba.

   “In kuma har baku yarda ba inada proof, Saje kunna audio’n.” Cike da mamaki Al’ameen da Zeezee suka d’ago kai suna kallon saje wani audio kuma? Suka tambayi junansu a zuciya se yanzu suka gano Saje ne source of all informations da Mama ta samu batun zaman aurensu wannan na nufin akwai recorder’n daya ajiye a d’akin Zeezee dakuma parlour kokuwa kullum yana eavesdropping ta window anytime yaji Zeezee akan waya seyana recording, this is serious!
 
   “I’m very sorry Sir, please forgive me for intruding, it was an order from your Mother” Saje yace da Al’ameen sannan ya kunna audio’n seji akayi muryan Zezee na tashi tana waya da Adeel ba a samun jin abinda Adeel ke fad’a se nata love words d’in har inda take sake ce mai budurcinta nasa ne kad’ai seda ya fito. Yana k’arewa aka sa na wanda take cinikin white gold nata Baba be gama jin audio’n ba zuciyarsa ta gama tafasa a zuciye ya miqe kafin Mama tace zata taresa yahau kan Zeezee tare dayin wani d’an banzan ball da ita seda gun ya 6ullo take. Wani irin rikicaccen ihu cike da azaba ta saki hakan yasa Al’ameen yayi saurin miqewa ya jata a yayinda Saje ya ja Baba baya shima yana me basa hak’uri, idon Mama kuwa tuni suka kad’a sukayi ja wannan wace erin rayuwa ce? Shin se Zeezee ta bata heart attack tukun zata huta? Cikin wani irin dishasshiyar murya numfashi na seizing Baba ya shiga magana.

   “Al’ameen ka saki yarinyan nan ka saketa nace! Shi saurayin naki Adeel ko wa yake shi zan bashi sadaqar ki amman kisani Zainab bazaki gama da duniya lafiya ba na rantse miki.”
  “Subhanallahi Alhj calm down please karka illata ta hakan baida amfani” cewar Maman Al’ameen a yayinda su Sadeeyah suke basa hak’uri.
   “Wallahi seya saketa kunji na rantse seya saketa. Ai auran Al’ameen gata ne a gare da wannan ‘yar iska la’ananniyar, da kai nake Al’ameen maza ka d’au takardan sakinta ka rubuta mata shi yanzun nan kuma ba saki d’aya ko biyu nake so ba uku-” tari ya shiga yi sosai, “saki uku zaka rubuta mata, ita wai saurayinta har yanzu tafi fifitawa akan kowa ba? Shi za’ayi mai sadak’ar ki wallahi bazaki gama da duniya lafiya ba Zainab” Baba yayi mata baki again. Salati Mama ta hauyi sabida shi kad’ai ke fitowa a bakinta, har anan Zeezee na abayan Al’ameen tana rusa kuka.
   “Alhj calm down please kaga har numfashinka na neman d’aukewa” cewar Maman Al’ameen “nima na goyi bayanka ayi sakin nan amman ba uku ba, saki d’aya ma ya wadatar tunda dan a hora Zainab ne.”
  “Wallahi uku za’ayi bazan yi rantsuwa a iska ba, kuma ko ke kad’ai ce ‘ya a gareni na yafeki Zainab na cireki daga cikin jerin ‘ya‘yan dana haifa ko a lahira kika ganni ki canza hanya. Ni? Ni zaki nemi ki 6atan suna a idan jami’u ki tozartani, na d’au miji me hankali da hak’uri kaman Al’ameen na baki amman ki tauye masa hak’k’i bayan nan ki ringa waya da saurayi a gidansa kinayin abinda kika ga dama? Bazan ce zan miki duka ba dan wallahi-” ya tsaya yana tari sosai a yayinda idonsa suka kad’a sukayi ja wur “ya isa haka haka Alhj dan Allah kayi hak’uri” cewar Saje har anan Mama datake zaune jugum a kan kujera ta kasa fad’in komi ko motsi ta kasa seda taji fad’uwan abu rigijib! A k’asa. Take dukkaninsu mutan wajen suka kai dubansu ga inda sukaji k’aran, sumemmen jikin Baba suka gani, innalillahi wa inna ilaihi raji’un kad’ai ke tashi a wajen “Alhj!!!” Mama tasa wani erin d’ankaren ihu tare da rugawa a guje ta nufi kan Baba ta aza kansa a cinyarta tana hawaye sosai tana tapping kumatunsa sede sam bayi motsi, nishinsa ma wani sama-sama yake fita. Nan da nan duk sauran suka nufi wajen banda Zeezee dake sprawled a k’asa tana kukan cire rai daga inda take. “Ta kashemin miji, ta kasheshi wayyo Allah na! Na mutu na lalace!!” A 360 aka kinkimi Baba se Teaching Hospital gabad’aya hankalin kowa ya matuk’ar tashi, Mariam ma tuni Omar yasanar da ita ta taho ba shiri a corridor’n emergency room da Baba ke ciki ta tarar da kowa da gudu taje ta rungume Mama datayi jugum wajen banda hawaye ba abinda takeyi, kuka suka shigayi a tare a yayinda su Sadeeyah ke basu hak’uri daga bisani Mariam ta d’ago kai tare da watsa wa Zeezee dake tsaye acan ita kad’ai tana kuka harara. Kamar a kyaftawan ido ta risketa tare da bata wani irin hot slap cike da tsana da haushi, wajen Zeezee ta riqe da k’yar tana hawaye endlessly kafin ta farfad’o daga marin Mariam ta k’ara mata d’aya a other side d’in. Da wuri Omar yajata baya a yayinda Al’ameen ya kare Zeezee “kin kyauta kenan? Kin kashe mana Baba kin kyauta? What kind of a sister and a daughter are you Zainab? Wallahi kisani inhar wani abun ya samu Baba none of us your family will forgive you, bazamu ta6a yafe miki ba” ta k’are maganan tana kuka sosai, rungumeta Omar yayi yana bubbuga bayanta.

   _45 more minutes..._
  A dai-dai nan ne red globe dake a bakin k’ofan da Baba ke ciki ya mutu and within second counts k’ofar ya bud’u tare da bayyano da wani Dr. daga ciki. Kusan a tare dukansu dake wajen suka nufa gun Dr’n da gudu kowa da abinda yake tambaya which is none other than ya jikin maras lafiyan yake banda Zeezee dake baje a k’asa achan inda Mariam ta tsinka mata mari tana kukan cire rai. “Calm down okay? Ku kwantar da hankalinku haka in shaa Allahu ze samu sauk’i we pray so.” Salati ne ya biyo baya, “Dr. Ka gaya mana meke damunsa dan Allah, am his wife please tell me wani hali mijina yake ciki dan Allah karka 6oye mana wani abin dan Allah nace” Mama ta k’are maganan tana jan hanci.
   “Toh muje office d’ina tunda kece matar tasa please.”
  “No Dr. I can’t wait till then duk nan family ne ka gayamana wani hali yake ciki please.”
  “Yes Dr please” cewar Omar da Mama Baba. Clearing throat Dr yayi “kaman yadda kuka sani shi patient d’in nada hawan jini ko?”
  “Eh amman rabuwan jinin nasa daya hau ya jima Dr.” Mama ta amsa immediately.
   “Yasamu heart attack ne wanda a dalilin haka yayi leading masa to heart failure-”
   “Heart failure?!” Sukayi exclaiming in unison. “Dr dan Allah karka cemin ya mutu I can’t afford to lose him” jan Mama Mariam tayi a jiki tana bubbuga bayanta.
  “Calm down be mutu ba mun bashi kulawan gaggawan daya kamata yana bacci yanzu in shaa Allah zuwa anjima ze farfad’o sede inason jin meya jawo attack dayasa har heart nasa yayi failing, saboda munyi all tests is not as if yana suffering from wani infection ko disease kokuma yana shaye-shaye.”
  “Baya shaye-shaye Dr. ‘yar sa ce ta tsinka mai zuciya abinda ya faru kenan” Mama tayi explaining in a crying tone.
  “Shikenan Hjy kibar kukan haka in shaa Allah mijinki ze samu waraka zamu d’aurasa akan diuretics da cardiac drugs sede yazamo dole abar breaking masa sad news kuma if possible koda ya tashi kar kushiga cikin d’akin nasa da ita ‘yar nasa data jawo mai attack d’in sabida by just looking at her zuciyan nasa tana iya tsinkewa again.”
  “In shaa Allah Dr. Mungode mungode sosai” Maman Al’ameen ta amsa.
  Komawa duk sukayi suka zauna atleast Baba be mutu ba yanzu, har anan ba wanda yayi takan Zeezee.

   _20 more minutes..._
  Alokacin har Mama Baba da Sadeeyah sun koma gida, Nurse ta sanar dasu Mama kan Alhj ya farka, godiya dukkanin su sukayi wa Allah sannan Mama kad’ai ta shiga d’akin, hawaye tasoma zubarwa wane lalacaccen famfo ganin har oxygen seda akayi supplying wa Baba. A nitse ta k’arisa wajen taja kujera ta zauna, “Al... Alhj?” Hannunsa yakeson d’agawa amman ya kasa data gano hakan seta d’aga ta had’a da nata “Alhj Allah ya baka lafiya, Allah baka lafiya Alhj” cikin wani dishasshiyar murya ya amsa da “ameen kukan ya isa haka, Al’ameen ya saki Zainab?” Abinda ya fara tmbaya kenan.
   “Alhj kabar damuwa da zancen Zainab its not fit for your condition.”
  “Ki gayamun ya saketa?”
  “Ya saketa Alhj” tamai k’arya ganin hannunsa ya soma shaking.
  “Hafsah nayi nadama, nayi nadaman maida Zeezee *_‘YAR GATA_* gata bashida wani amfani, tabbas da naji maganarki da a baya da duk hakan be faru ba, ina alfahari da Mariam da Yasmeen Allah ya cigaba da musu albarka.”
  “Ameen Alhj duk wannan ba abinda zaka damu kanka dasu bane yanzu, lafiyanka ne a gaba su Mariam suna nan kanason ganinsu?”
  “Eh ki shigo min dasu” sauk’e hannunsa tayi a hankali taje ta kira su Mariam inda ta sanar da Al’ameen komin rintsi yacewa Baba ya saki Zeezee saki uku kaman yadda ya buk’ata. Bayan Mama suka bi suka shiga ciki da gudu Mariam da Omar suka nufi kan Baba suna kuka sosai a yayinda shi kansa yake hawaye, “‘ya‘yan albarka ku yafemin, ku gafarceni na rashin adalci danayi a tsakaninku ku yafemin please.”
   “Baba dan Allah kabar neman yafiyanmu ba abinda ka mana mude fatan mu Allah ya baka lafiya” cewar Mariam
   “Sannu Baba” cewar Al’ameen “Allah ya baka lafiya”
  “Ameen” Omar da Mariam suka amsa.
  “Al’ameen nagode Allah saka maka da alkhairi.”
  “Ameen Baba bakomai.”

   *** Tsaye Mama ke a bakin k’ofar d’akin Baba tana bin Zeezee dake ta kuka har a yanzu da harara, wani wutan tsanan Zeezee ne ke ruruwa a zuciyarta. Jiki na k’yarma Zeezee ta doso inda Mama ke tsaye tare da kneeling a gabanta tana kuka me tsuma zuciya, “Mama dan Allah kiyi hak’uri, kiyi hak’uri dan Allah na tuba bazan sake ba.” One more dirty look Mama ta watsa mata sannan ta bar mata gun tare da shigewa d’akin domin batajin zata iya mata magana.



*© MIEMIEBEE     ™YGC!*
www.beeenovels.blogspot.com
๐Ÿ‘„๐Ÿ‘„๐Ÿ‘„๐Ÿ‘„

1 comment:

Unknown said...

Tnkz We Ar Grtful