Monday, 13 February 2017

‘YAR GATA CE!

 
*BY MIEMIEBEE*
Page 48
  FEBRUARY , 2017




Jikinta ba k'wari yana mata ciwo sosai tasamu da k'yar taja luggages nata ta fita dasu tasa a booth. Hamdala ta saki ganin da mai a ciki, ba tare da b'ata lokaci ba tayi shoving kanta cikin motar ta kunna, koda su Adeel suka jiyo qaran motarta basuyi ta kanta ba. Gate na recognising motarta ya bud'u mata ta fice sede kash bata iya tuk'in dare ba bayan nan kuma bata san ina zata dosa ba gidansu Lubiee ne? Gaskiya ba fasali koda Baba baze barta ta kwana mai a gida ba theres no place like home ya kamata iyayenta ne su soma sanin wani hali take ciki, bazata sake tafka sakarcin da tayi da a baya ba, don haka gidan zata wuce sede bata da courage. Parking tayi gaba da layin gidansu kad'an ta shiga rusa kuka sosai, tissue tajawo tare da kunna wutar motar nata ta shiga share jinin dake fuskanta inda Adeel yayi mata jina-jina sede don zafi ta kasa gogewa don haka ta yasar ta kunna motar ta shiga tuqi. Unguwansu dutsan tanshi ta nufa cikin ikon Allah tana driving a hankali har ta isa gida alokacin ana neman wuraren 7:12pm gari be gama yin duhu shar ba. Sam ta kasa fitowa daga motan da k'yar tayi gathering courage ta shiga ciki tana rik'e da medium sized akwatinta. Mama ta tarar a tsakar gida tana zaune bisa sallaya da alama yanzu take idar da Sallah. "Assalamu Alaikum" Zeezee tayi sallamar tsoro na building acikin muryarta.
   "Wa'alaikumus salam" Mama ta amsa cike da zumud'i jin muryan Zeezee. To her suprise ta ganta riqe da akwati kobata tambaya ba tasan korota Adeel yayi ga kuma yadda fuskanta yake duk jini tagun bakinta.
  "Subhanallahi!" Tayi maganan tana dosan gaban Zeezee, kuka kawai Zeezee tasa tare da fad'awa jikin Mama tana kuka me tsuma zuciya, hugging nata Mama tayi tana bubbuga bayanta.
   "Ya isa kiyi haquri bar kukan."
  "Mama ya sakeni kafin nan seda yamin d'ankaren duka."
   "Kiyi haquri Zeezee in shaa Allahu kin rabu dashi kenan har abada wuyarki ya k'are ya isa kukan." Janta Mama tayi suka zauna kan darduma, "gayamin meya faru." Tana kuka tana bawa Mama labarin k'azafin da Ruky Mama tayi mata da kuma yadda Adeel na zuwa ba tare da ya bata chance tayi explaining kanta ba ya rufeta da duka. Sosai Mama ta tausayawa 'yarta. Suna zaune a wajen Mama na ta kan bata haquri Baba da Omar suka dawo from Masjeed. Da hira suna murmushi suka shigo amman Baba na ganin Zeezee ya tamqe fuska shikansa yadda ta sake fad'awa ya basa mamaki amman ya dake, "Hafsah me wannan 'yar iskan takemin a gida? Menace miki batun kawo min ita gida? Ke bazakiyi hankali ba sena sa polisawa sun baki kashi ne komeh? What part of na cireki daga cikin jerin yaran dana haifa don't you get? ban sanki ba Zainab kidena shigo min gida" Ya qare maganan yana watsawa Zeezee dake ta zubda hawaye mugun kallo. Bakinta na 6ari ta soma dacewa "Baba don Allah badon niba kayi haquri ka yafemin abubuwan dana maka wallahi bijirewa umarninka danayi shine babban kuskuren dana afka a rayuwa na, nayi nadama fiye da yadda zaka ta6a tsammani banida kamar ku da Mama inhar ka cigaba da fushi dani wallahi Allah baze ta6a yafemin ba. Baba Adeel dana fifita akanku bisa rashin tunani ya sakeni har saki biyu bayan wulaqanci da azaban daya ta gallamin a gidansa wallahi dana ta6a sanin haqqin iyaye haka yake da koda wasa bazan ta6a take magananka ko na Mama ba bale har umarninku. Baba in baka yafe min ba bazan ta6a iya yafewa kaina ba ka dubi girman Allah ka yafemin Baba don Allah badon niba" ta qare maganan tana kuka sosai.

    "Saki biyu kacal ya miki ai da yayi uku sannan yamiki dukan da ze kaiki har lahira, nadama kuwa har yanzu bakiyi shiba maza tashi kibar min gida 'yar iska kawai." Shiru Omar yayi gun gabad'aya tausayin Zeezee ya kamasa haka ma Mama daga bisani ta bud'e baki tace, "haba Alhj! Yarinyan nan abar a tausaya mata ne, batada kowa daga Allahnta se mu. Ga takaicin rashin haihuwa gana wulak'anci da azaban da tayita sha gidan miji da kuma kishiya, gana rabuwa da miji dukda ba sonta yake ba amman still ba dad'i sannan kuma ace uwa uba gana iyaye? Ka tausaya mata mana Alhj 'yarka cefa ka korata yanzu ina kakeson taje, gidan mijin nata daya saketa?"
 
   "Koma ina ne taje amman bazata kwana min a gida na ba ai bani nace tun farko ta auresa ba kuma bazan tausaya matan ba and idan kika sake kwatanta 'yar iskan nan da 'yar cikina ban yafe ba. Kija bakinki kimin shiru, ai komin nan da kika lisafo ita ta janyoshi wa kanta wai har zata fifita saurayi akaina ni da rai ne kawai ban d'au na bata ba wallahi for the last time kifita min daga gida inhar kinga kin kwana a gidan nan toh bani raye maza ki fice nace ko sena kira polisawa tukun?" Har qasa Zeezee ta durk'ushe tana kukan cire rai tana bawa Baba hak'uri amman haka yak'i hak'ura yayi turning blind eye, harda zaro waya shi ze kira polisawa. "Ya isa haka Zeezee tashi abinki, Alhj ba seka kira wasu polisawa ba gidanka ne zata fice ma amman kasani ko Allah akayi mai laifi yana yafiya muddin aka tuba."
   "Kina nufin kice min ke kin yarda da tuban wannan munafikar? Sau nawa take kalan tuban nan ta sake komawa gidan jiye? Ta tashi tabar min gida abinda na buqata kenan."
   "Baba wallahi wannan ba kalan tuban dana sabayi da a baya bane, naga rayuwa Baba wallahi na tuba na haqiqa har abada bazan sake take umarninka ba ko mahaukaci kace zaka auramin inhar hakan ze farinta maka rai am ready to do it please believe me Baba banida kowa bayan kai da Mama please." Ta sake fashewa da kuka.
    "Tashi ki fita nace" ya fad'a as if though beji dukkanin abinda tace dashi ba. "Mamana tashi bada haqurin ya isa haka" cewar Mama cike da tausayi. "Ko gidan Mariam ne kiya je ki kwana amman Alhj kasani ba haka akeyiwa yaro ba kuma tun farko da baka d'aura Zeezee akan gur6arcacciyar tarbiya ba da duk hakan be faru ba kasani you are partially to blame for all these."
   "Ki fad'i koma me Hafsah and ba gidan Mariam da zata inhar kikaje kika kwana a gidan wani nawa wallahi kisani Allah ya isa ban yafe ba" jin haka Zeezee ta sake sa wani kukan har wani sama-sama nishinta ke dan kuka, bata ta6a sanin Baba ze tsaneta haka ba tabbas tayi kuskure a rayuwarta. "Kifita nace!" Tana kukan ta shiga jan akwatinta "ki wuce gidan k'awata Mrs Muktar zanyi mata magana." Mama ta sanar da ita tana mejin zafin abinda Baba yake sekace bashi ne silan komi ba.
   "Sede taje chan d'in kam 'yar iska kawai ai kad'an kika gani wallahi, duniya kad'ai ta isheki."
   "Toh Mama nagode, Baba kaikuma bazan gaji da baka haquri ba I pray one day we will be the US we used to be before" tace sannan tafice cikin motarta ta koma inda ta sake bud'e sabon dandalin kuka me tayi ma kanta haka? Shikenan ita haka zata qare rayuwarta da fushin mahaifinta akanta? Tayi a k'alla minti biyar agun sannan daga bisani ta tada motarta ta nufi gidan Mrs Muktar dake unguwansu inda already dama tana jiranta Mama ta riga ta sanar da ita komi.

   Wuraren k'arfe sha d'ayan dare Mama dake bacci ta farka don gyara kwanciyanta se ganin Baba tayi zaune bama alaman bacci a idonsa. Alhj? Ta kirasa. Sede sam be amsa ba kasancewar yayi zurfi cikin kogin tunani. "Alhj!" Tad'anyi tapping nasa. Se anan ya amsa da "na'am" ad'an firgice not paying attention to her.
  "Lafiya?" Ta tambaya.
  "Lafiya" ya amsa sama-sama.
  "Toh meya hanaka bacci?"
   "Babu komai koma baccinki."
  "Hm dade kabar 6oyewan ka fad'i gaskiya. Tunanin Zeezee kake koh ba haka ba? Ai kai kanka kasan baka kyauta mata ba 'yarka cefa ta cikinka. Dubi yadda ta tuba amman kace bazaka yafe mata ba da gidan ubanta amman se inde na turata gidan k'awata taje ta kwanta."
    "Ni bance miki tunanin ta nake ba saboda haka ki dena kawo min zancenta."
  "Its written all over your face Kade yi a hankali kasan me likita yace maka game da tunani dayawa in jikin ka ya tashi ba ruwana." Ba tare da ya sake cemata uffan ba  yaja bargo ya rufe kansa sede sam ya kasa bacci tunanin ina zaisa kansa a idanun jama'a yake danko da kunya ace yarinya 'yar 18years aurenta biyu duk sun mutu wai kuma da iyayenta akanta, da tunanin haka bacci 6arawo ya sacesa.

      >*^>*>
     Washegari a gidan Adeel.
   Kasancewar yau ba school se bacci Adeel da Ruky'n sa suke sha. 11:47am kamar yadda suka saba tashi yau ma sukayi, bayan sunyi wanka suka fito tare as always dama se su tanadar da breakfast nasu Zeezee ta had'a musu amman yau kan dining wayam ba komai. Dukansu sunji wani iri a jikinsu daga bisani Adeel yace, "muje mu siyo breakfast ko zaki zauna a gida inje na dawo?"
   "Kaje ka dawo Babe bana jin zan iya fita." Pecking nasa tayi a cheeks sannan ya fice.

   ***
   Tun da Baba ya tashi yau ba aikinsa se tunani Mama tayi mai magana kan ya rage tunanin saboda lafiyarsa amman yaqi jinta. Duka yayyun Zeezee Mama ta kira ta jaddada musu halin da Zeezee ke ciki. Yasmeen da tausayi sosai ta tausayawa Baby Sis nata banda Ibraheem da har yanzu haushi abinda Zeezee tayiwa Mama da a baya yake.
     Tun dawowan Zeezee gida take gidan Mrs Mukhtar tana zaman iddarta, da safe zata tashi tayi assisting nata aiki kasancewar batada me aiki, shara, wanke-wanke da shirya yara school duk Zeezee keyi har girki ma. Inba aiki take ba toh tana maqale a d'aki tana kuka. Abubuwa sun kasa dai-daita tsakaninta da Baba yau da dawowarta gida sati biyu kenan amman sau d'aya data sake komawa dan basa hak'uri haka yayi mata kaca-kaca har ciwon sa seda ya kusan tashi tun daga wannan rana Mama ta bawa Zeezee hak'uri ta kuma haneta da sake visiting home.  Addu'a de Zeezee bata fasa ba batada burin da ya fiye mata Baba ya yafe mata.

   Ta fannin Adeel da Ruky kuwa daman shi Adeel ba ma'abocin siyan abincin waje bane Allah-Allah yake Ruky ta kare exams ta soma masu girki. Cikin ikon Allah suka gama, yau Thursday Ruky na zaune kan kujera a parlour wuraren k'arfe 12 na rana Adeel ya dawo daga d'an fitan da yayi ransa a murtuk'e gabad'aya ba komi kuma ya haifo da hakan ba illa duban bank acct nasa da yayi yaga is low, shi kansa mamaki yasha duk uban kud'in dake ciki ace ya k'are besani ba shi kud'i suna ne. Kuma bayan kashe-kashen da yayita wa Ruky ba dole ba. "Baby sannu da dawowa" tace dashi a hankali. Kujera opposite da ita ya zauna tare da jan wata doguwar tsuka, da mamaki ta tsaya kallonsa "tsakin meh kuma? Did I say something bad? Am hungry ina lunch d'ina." Wani kallo ya galla mata ransa a mugun 6ace sannan yace, "yana kitchen ki tashi ki girka mana nima yunwan nakeji."
   "Kamar ya na girka lunch? Ba siya mana kake kullum ba?"
  "Kud'in gabad'aya ya qare kin huta aiko? Mschw!"
  "Kamar ya kud'i ya qare Baby? Kana nufin ba komai a bank acct naka?"
  "Eh mana bayan siyayyan danayi ta miki ba, komi ya qare ba abun arzikk bane ya rage."
   "Toh ka tambayi Mami mana."
  "In tambayi Mami? Na miki kalan me maula ne? Karki 6atamin rai please" ya fad'a a fusace.
  "Kamar ya kada na 6ata maka rai? Nice de zan ce karka 6atan rai. Meaning what yanzu bakada kud'i ni zan fara girki kenan akan shara dakuma mopping danake duk akan wannan cikin?" Tayi pointing cikinta.  
   "Sosai ma kuwa Zeezee da takeyi ba mutum bace ita? Ko sata kikeso nayi na  kawo me dafa abinci dame aikin?"
  "Ba sata ba amman de ka nemi abinyi ko aiki ne kana iya applying."
  "Aiki? Nine zanje miki aiki? LOL Ruky you are funny."
    "Dariyanka ko ze koma kuka Adeel, bikin friends d'ina twins ya taso kake min zancen bakada kud'i dame kakeso naje bikin nasu?"
   "Lallai fa Ruky!" ya kalleta cike da mamaki "da bakina zaikije, kinji? banida kud'i and all you can think of and worry about is auren god damn friends naki? Bakiya tunanin in abincin mu ya qare aina zamu samu sabo?"
  "Wannan kuma ai ba damuwana bane tunda kaine magidancin bani ba all am adamant of is that in ba kud'i there will be trouble don wallahi ban iya rayuwan talauci ba."
  "Zako ki koya." Ya fad'a yana bata nasty look.
  "Wallahi a'a tun wuri kasan nayi dani ba fa yadda za'ayi ace mace me ciki kaman ni zatana girki shara da sauran tarukuccen aiki" a ranta tace dama ban d'aura sharri wa Zeezee ba wallahi da yanzu ita zatana min komi.
   "Yanzu tashi and get us something to eat" ya buk'aceta.
  "Mekuwa? Kaje ka siyo mana de."
  "Banda kud'i nace miki kuma ma bayan nan nagaji da siyan abincin waje. "Purse nata dake gefenta ta d'aga tare da zaro 5k "gashi kaje ka siyo mana toh tunda bakada kud'i" Bata ma ishe sa da kallo ba uwarsa ma gabad'aya bayi tambayan ta kud'i bale matarsa "ni kike bawa kud'i?"
  "Kace baka da shi." Ta amsa atake.
  "Meaning? Ajinki you can give me donations ne? This should be the first and last koda wasa kada ki sake cewa zaki bani kud'i banaso."
   "Sekaje ka siyo mana ai toh."
  "'Ke al'ada hannunki ke da bazaki girka ba? Yau watannin ki nawa a gidan nan kin ta6a aza tukunyan girki ne? Ba Zeezee kullum keyi ba? A rashinta kekuma meye amfaninki?"
 
  "Nide wallahi ba abinda zan girka saboda banida lafiya."
  "Kikace meh?"
  "Ba abinda zan girka" ta sake nanata kanta.
  "Har in saki aiki kice bazakiyi ba?"
  "Ai akan gaskiyata nake wallahi inhar kanason zaman lafiya tun wuri kaje ka nemo mana me aiki da zatana taimaka mun."
  "Lallai ki sake tunani Ruky, shekaran Zeezee d'aya da watanni a gidan nan ban ta6a d'aukan mata me aiki ba saboda haka kema ba me aikin da zan d'auko miki esp ma yanzu da banida kud'i kiji ki sani."
  "Lallai kuwa cin abincin Mami ya kamaka."
   "Sa'anki d'aya Ruky abinda ke jikinki-"
  "Da meh?" Ta tambaya tana zaro mai idanunsa cike da raini "duka na zakayi yadda kayima Zeezee? LOL wai akace ido wa ka raina yace wanda nafi gani kullum, kaima kasan ni ba kalan matan da mazaje ke duka bane haka kawai dan ka ibo buhun talaucinka bazaka zo kana sauqemin aka ba ehe!" Tana kaiwa nan ta miqe da k'yar ta nufi d'akinsu tare da sa lock, binta Adeel yayi a fusace yana rattling door in amman taqi bud'ewa. Ba kalan surutun da beyi ba taqi da Zeezee ce da shi kansa besan kalan dukan da zeyi mata ba.
 
  *~ *~
   Abu fa kaman wasa al'amura se kuncewa suke tsakanin Adeel da Ruky Mama har yau taqi aza tukunyan girki musu haka baida kud'i amman dan dolensa seya siyo musu abinci kokuwa tace zataje ta cire cikin sanin how desperate he is ya zama Father yanzu. Gabad'aya ya rasa damuwan Ruky ko dan taga tana d'auke da juna biyu ne oho bayi ta6a sata aiki tayi. Besan meh ba sekuma ya soma missing Zeezee yanzu. Dukansu suna matuqar missing Zeezee a 6oye sede ba kaman yadda Adeel keba, he just misses everything about her. Shifa be ta6a sani bane amman Zeezee tafi Ruky iya komi he really wants her back.

   *****
    Cikin ikon Allah Zeezee ta gama zaman iddarta a gidan Mrs Mukhtar har rana me kamar na yau fushi da ita Baba yake gashi seya yini yana tunanin Zeezee which is very bad for his condition. Sosai Mrs Mukhtar takejin dad'in zama da Zeezee. Anan ne watan haihuwan Ruky ya kama tun tashiwarta da safe bayanta keta azabartar da ita, gashi jiya suka haura sama da Adeel sukayi fad'a kaca-kaca ita seya bata kud'in ashoben bikin friends nata, shikuwa jiya yayi spending last kobonshi ya siya musu dinner kud'in daya rage a gunsa shine na hospitality'nta. Tana miqe a qasa tana aikin juye-juye Adeel ya fito daga bayi gabad'aya haushinta yakeji. Koda ya ganta beyi ta kanta ba, da ihun nata ya ishesa ne yace, "ke wai meh haka? Akanki aka soma yin ciki ne?"
   "Adeel baya na wayyo zan mutu!" A ransa yace ki mutun mana ko zan d'an sha iska nima.
  "Adeel dan Allah ka kaini asibi-" bata idda maganan ba water'nta yayi breaking se anan Adeel ya miqe cikin hanzari ya d'ago maternity bag nata sannan ya cinci6eta se asibiti suka nufa. Achan akayi labour room da ita, tunda tasan kanta bata ta6a jin azaba kaman na yau ba. Bayanta wane ze 6alle dan ciwo gabad'aya tafita daga hayyacinta.

   Iyayenta Adeel ya kira ganin har tayi 5 good hours bata haihu ba. Azaba kan azaba shima Adeel gabad'aya ya kid'ime se gani yake kaman Ruky zata mutu tabarsa, ya zauna a labour room d'inma ya kasa se safa da marwah yake a corridor na d'akin. Ganin taci har 8 hours bata haihu ba likita ya yanke hukuncin yimata CS da k'yar Mami ta samu Adeel yayi signing papers d'in. Itace ma zata biya kud'in aikin danko Adeel bayida gashi da shegen pride ya kar6i kud'in da take basan ma yaqi na aikin ma don bayida nayi ne. Ana biyan kud'i akayi da Ruky Mama OR kafin nan seda Ruky ta nemi da akira mata Adeel.
   Hannunsa ta riqe da nata tana kuka sosai, "Adeel if today should mark my last day don Allah kaje kasamu Zeezee on my behalf ka bata hak'uri please ta gafirceni" Ta qare maganan kalamunta basu fitowa sosai.
   "Hak'urin me Ruky what are you talking about?"
   "Adeel I lied to you, sharri nayi mata koda wasa Zeezee bata ta6a ta6a lafiyar jikina ba bale hartace zata kasheni."
   "What?!" Yayi exclaiming tare da jan hannunsa daga riqon datayi mai. "What gibberish are you talking about?"
  "Adeel nasan nayi laifi babba banason na mutu da haqqin Zeezee a kaina don Allah ka bata haquri, ban sani ba ko bazan sake fitowa daga OR d'innan ba please."
   Wace irin munafuka ce ke? Kisani koda Zeezee ta yafe miki ni bazan yafe miki ba" yana kaiwa nan yafice a fusace not minding the calls she's sending him haka tana kuka sosai aka wuce da ita OR a yayinda Adeel ke haraban asibitin ya zauna gu guda hannunsa duka biyu manne a fuskansa. Kallo d'aya za a masa a gano yana cikin tashin hankali. "Why?" ya tambayi kansa "why didn't I listen to you also na yanke hukunci? Zeezee ashe you meant it time da kikace zan nemeki wataran nayi kuskure na sakan ki danayi Ruky ya kamata na saka ba keba. I'm so sorry Zainab" tunanin Zeezee yacigaba dayi instead of na matarsa da rai ke a hannun Allah.

  1 hour later Dr'n da yayi wa Ruky Mama aiki ya fito daga d'akin nan Mamanta da shima Adeel da suke zaune a corridor'n suka dosa gaban Dr'n. Mahaifiyar Ruky ce ta tambaya "Dr how is she? Was the operation successful?"
   "Alhamdulillah lafiyanta k'alau shine babba." Ya amsa.
  "Alhamdulillah" ta sake cewa da "ya baby'n nata kuma fa Dr?" Har anan Adeel beyi magana ba inbanda tunanin Zeezee ba abinda yakeyi. Kai ya kad'a tun daga nan Adeel ya gano baby ba rai.
  "Am sorry mun samu mun ciro baby saidai ba rai tun a ciki ya koma ga mahaliccinsa Allah baku haquri I'm sorry kuna iya shiga ganinta excuse me please." Sam komawan baby'n be bawa Adeel mamaki ba saboda yasani bayan abin da Shida Ruky suka tayiwa Zeezee dole hakan ya faru. "Adeel kayi shiru, bakaji me Dr yace ba?" Cewar Maman Ruky.



*MIEMIEBEE       Team #YGC!*
Beeenovels.blogspot.com
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„

18 comments:

Unknown said...

Mungode sis, Allah ya kara basira

Unknown said...

Adeel kaima kada Allah ya baka haihuwa, yanda ka lalata ma zeezee mahaifa kaima kada kasamu yaron kanka.

Unknown said...

Allah ya hanemu da daukan hakkin wasu dan hakkin mutum babban jaraba ne, inde kadau hakkin wani kaima Allah baze barka ba kuma baze yafe mka ba harsai wanda ka aikatawa ya yafe mka ....yakamata mu dauki darasin rayuwa babba
Muna godiya sosai miemie Allah biyaki

Ilyasu Ibrahim Ilyasu said...

Wow Allah ya Kara basira, Allah kuma ya hane mu da halin cutar da matan mu, Miemie Allah ya Kara basira.....tnx

Ilyasu Ibrahim Ilyasu said...

Wow Allah ya Kara basira, Allah kuma ya hane mu da halin cutar da matan mu, Miemie Allah ya Kara basira.....tnx

Unknown said...

Enter your comment...tnx a lot

Unknown said...

Enter your comment...thank you sister

Sabiyyah Affandi 🌹 said...

ZEEZEE kici gaba da addu'a. Baba zai zo yayi accepting naki back. As for those scandalous-idiots,(Adeel&Ruky)...don't worry ZeeBaby fate is dealing with them the way they ought to be dealt. I'm glad things are turning up-side-down.

Sannu da kokarin nishadantar da mu Miemie...Allah shi k'ara basira. Allahumma. Ameen

Unknown said...

Munanjiranki de miemie

Unknown said...

MIEMIEBEE pls we r waiting.

Unknown said...

Ya miemie where u deyyyyyyyyyyyyyy!!!!!!!!!!

Unknown said...

Enter your comment...wow I must say I can't wait for d next chapter to be updated...plss don't keep us waiting....nd wish to tell I reallyenjoyed like all ur books Cox am actuallyur great fan even in wattpad.....

Unknown said...

sisto..dix suspense z killing me ooo....

Unknown said...

Hba miemie dan Allah kina mna kullum mana kaman da ko bada yawa atleast mun huta kema ki huta da hayaniyar mun😣😣😣

Unknown said...

Gsky I'm really enjoy ur novel but gsky kwana 2 yana hanani karatu.

Unknown said...

And y can t u make it a a book bcoz of some issues

Unknown said...

Pls need ur on INA TARE DAY ITA. wlh munyi loosing page 51 to 65 please any u got please ataimakamin so u shall send true this number 08141588795 name:- sani musa please need ur helps

Unknown said...

I enjoy dis more ink to our pen bravo plx baba ya yafewa zeezee kafin ya mutu