BY MIEMIEBEE
PAGE 16
*December, 2016*
“In kin fasa, banje na ta dake Sallah kika k’i tashi ba? Fice min daga d’aki da Allah!” tsaye tayi gun tana mata mugun kallo ledan bread dake gefen ta Mama ta d’aga ta wurga mata “ficemin nace!” Kuka Zeezee tasa ta nufi d’akinta ta kira Baba a waya tana kuka cike da tashin hankali ya tambayeta ko lafiya nan ta irga masa komi. “Haka suka yi maki? Kai wa Maman naku wayar” ai atapir Mama tace bazata amsa wayan ba saboda tasan ita ta tada Zeezee itace tak’i tashi “Hafsah fa ina jinki amshi wayan nace!”
“Wallahi bazan karb’a ba duk Alhj kabi ka b’ata yarinya se aukin rashin kunya nan gaba aka tayar da ita zata tashi ai.”
“Aww haka kika ce koh?”
“Eh ai hakan ne.”
“Da kyau, Zeezee...”
“Na’am Baba” ta kashe speaker.
“Bari in na dawo zanje in samu teacher’n naku in shaa Allah ze baki makeup d’in shi kuma Ibraheem zan kirasa bar kukan haka kinji K’anwata.”
“Toh Baba nagode ba-bye” yana katse wayan ya kira Ibraheem ya dinga balbalesa da masifa. Da azahar Mama ta shigo d’akin Zeezee ta tarar da ita mik’e kan gado tasa earpiece a kunne tana jin music tana kad’a kai.
“Laa’ilaa! Kid’a kikeji haka?” Earpiece d’in ta zare “ni wayace miki wak’a nakeji shikenan mutum be isa yasa earpieace ba ace yana jin wak’a.”
“Toh me kike ji dashi?”
“Voicenote aka turon a whatsapp nake playing.”
“Yayi kyau mik’e kije ki share min d’aki ki kuma gyara kan gado kiyi mopping zan shiga nan mak’ota.”
“Toh ba Baaba tazo ba”
“Baaba bata da lafiya bazata iya duka aikin ba.”
“Ni wallahi da erin wannan aiki gwara an sallameta mutum sekace me aids kullum batada lafiya-” kafin ta hankara taji sauk’an mari fas! A bakin ta, “ki iya bakinku kina jina koh?”
“Allah ya-”
“Mawa?” Mama tayi saurin katse ta dama cike da ita ta ke, nan ta rufe ta da duka seda tayi mata lik’is sannan ta barta “marasa kunya kawai kuma ki kira Baban naki yanzu ki cemasa nayi maki duka kiga in bansa Omar ko Ya Ibraheem sun k’ara miki ba.” Kuka sosai Zeezee ke tsakaninta da Allah ana cikin haka Omar ya dawo gida inda yaji hanayaniya ya zarce “ya haka Mama? Meke faruwa?”
“Barni da maras kunyan nan Omar zan fita ka tabbata ta share min d’aki tayi mopping in bahaka ba kamata dukan tsiya nina baka izini.”
“An gama Mama sekin dawo” nan ya dawo da kallonsa kan Zeezee dake harararsa “me kike jira har yanzu da baki mik’e ba?” Bayan fitan Mama yasa Zeezee gaba taje ta d’au tsintsiya ta shiga sharan cuwa-cuwan data saba duk ta tuttura dottin k’arkashin gado tanayi Omar na mata dariyan mugunta itako se zaginsa take a ranta.
Da La’asr Yasmeen ta dawo gida taci broke kona kati bata da, remembering tanada 2k gun Zeezee ta mik’e taje ta sameta a d’akinta oya ke bani 2k na, ai ba haka mukayi dake ba.”
“Ai nice zan ce ba haka mukayi dake ba, ce miki nayi se Baba ya dawo.”
“Lallai kuwa! Yaushe mukayi haka dake? Kinsan yaushe ze dawon nema? Kiban kud’ina Malama”
“Seki d’auken ai tunda nima kud’i ne” tana kaiwa nan ta juya mata baya. K’arisawa cikin d’akin Yasmeen tayi ta wanke ta da mari a baya “Allah ya isa kuma bazan bada kud’in ba.”
“Haka kika ce?”
“Eh” kafin ace me suka b’arke da fad’a tun daga d’aki Mama takejin hayaniya “ya haka? Meke faruwa?” Tayi maganan tana k’ok’arin rabasu, ko a babu Zeezee taci k’aniyanta da k’yar Mama ta samu ta raba sun “wai kashe kanku kukeson yi neh?”
“Mama wallahi kice ta biyani 2k na” cewar Yasmeen tana huci.
“Meya faru tukuna?” Nan Yasmeen ta labarta mata komai bayan da Mama ta gama jinta tace, “toh kema meya kaiki baiwa wannan bashi? Sekace bakisan halinta ba.”
“Wallahi tsautsayi kuma ma seda ta rantse kafin na bata.”
“Oya Zeezee nasan kinada kud’i pay her back her money.”
“Aiki nake da zan samu kud’i ta bari Baba ya dawo.”
“Sarai nasan kina saving break money naki ki d’au dubu biyu ki bata or else.”
“Or else what? Zaki cire mata daga cikin pocket money na da Baba ke baki?” Tayi maganan unbelievably.
“Tabbas! Tun wuri ki d’au kud’inta ki bata.” Kuka Zeezee tasa “wallahi Allah ze sak’a min ni se Baba ya dawo na bata.”
“Taho muje Yasmeen na baki a pocket money’n ta.” Ba kalan darun da Zeezee batayi ba amman hakan be hana Mama d’au dubu biyunta ta bawa Yasmeen ba, yini tayi ranan tana kuka gashi kota kira line na Baba bai shiga.
The following day tasa alarm nata da kanta ta tashi, koda taji Mama na knocking k’in amsawa tayi bayan ta gama shirinta ta fito ta leqa dining wayam taga ba breakfast nata daman aikin Yasmeen ne had’a mata breakfast Baba yayi appointing nata.
Gbam! Gbam! Gbam! Knocking take bisa k’ofan d’akin Yasmeen wane zata b’alla, sauti cike da gyangyad’i tace “wallahi kika sake knocking kinji na rantse zaki school kina kuka yau.”
“Sekisa d’in ai muga iskanci kawai ina breakfast d’ina?”
“Cook d’inki ce ni da zaki tambayen?”
“Eh mana ai aikin kine Baba yasaki kina min breakfast.”
“Toh banyi ba yau saboda Ya Ibraheem yace baze karya ba danke kuma bazan yanke bacci na ba.”
“Kutcee! wallahi bari Baba ya dawo zakiga!” Kitchen ta nufa ta fiddo da three eggs da nufin soyawa sede sam ba ta iya ba at last ta k’ona k’wan itama ta k’one a hannunta a takaice da coco pops tayi breakfast ranan sannan ta koma d’aki tagama shiri ta nufi na Mama dan amsan break money’nta.
N200 d’in ta d’aga kan chess of drawer “Mama” ta kira sunanta “meh?” Ta amsa not minding ta juya. “Ance fa mu sayi Evergreen solution na junior waec namu.”
“To ba seki jira Baban naki ya dawo ya baki ba.”
“Ai bansan ranan dawowan sa ba kuma yaune deadline d’in.”
“Yayi kyau seki tambayi Ya Ibraheem.”
“Ni wallahi a’a nasan ba bani zeyi ba kibani in tafi please zan yi latti” se anan Mama ta mik’e zaune ta juyo tana kallonta “wai ma tsaya anya ba k’arya kike ba? Anya kuwa ance kusai textbook d’in?”
“Eh mana da zan miki k’arya ne.”
“Nawa ne?” ta tambaya finally tare da mik’ewa.
“N2,000 ne.”
“Ke wai ni zaki raina ma wayo? Wato jiya dan na cire 2k daga kud’inki shine kema zaki dampareni koh?”
“Allah ma sheda nane kibani wallahi kona kira Baba na sanar dashi.”
“Inma k’arya kike keda Allan ki” nan ta mik’a mata 2k d’in kwatsam ta amsa ba godiya “dawo, dawo nan.”
“Menace miki duk lokacinda aka baki kud’i?”
“Inyi godiya” tayi maganan tana sa kud’in cikin jakarta.
“Mekuma kikayi yanzu?”
“Toh kud’in kashewa ne kika bani? Bana school bane? Kuma naga in nayi karatun kema ze amfane ki mena godiyan?” Buge bakinta Mama tayi da k’arfi seda ya fashe ya soma jini take idonta ya ciko da hawaye “karki iya bakinki ki koyi kalmasa kalamunki kiga kullum inban riga bige bakin naki ba, kiyi godiya ko kiban kud’ina?” Shiru tayi chan tayi mumbling “nagode” sannan ta fice rai a dak’ule “Allah ze sak’amin kuma ko a babu na amshi kud’ina wallahi ba Evergreen da zan siya” garriage ta nufa tana jiran fitowan Ibraheem ayayinda bakin nata ke tayi mata rad’ad’i idanunta kuwa se cikowa suke da hawaye. 3 minutes more Ibraheem ya fito kallo d’ai ya mata yagano da akwai matsala “meh haka kuma kike wani turo baki?”
“Ba Mama bane ta bigen a baki na.”
“Eh ai dai-danki kenan bake rashin kunya ba.”
“Ni tunda ba sannu zaka cemin ba save your wa’azi ka bud’e motan.”
“Meh kikace?” yayi maganan in a serious tone.
“Nace kad’an bud’en motan kar nayi latti.”
“Da yafi maki kam.” Bayan sun isa school d’in kafin ta fito daga motan ya kashe mata warning “sauran kuma idan nazo d’aukanki ki shanyani like the other day kiga abinda zan miki yau” bata ce komi ba seda taga yaja motarsa tace, “mugu kawai” sauk’an mari tajiyo abayanta cike da tsiwa ta juyo ready to insult who ever it was kawai setaga Lubiee.
“Ohh Lubiee!” Ta fad’a a bit startled.
“Ahhhh! ‘yan mata yau ma a tare muka iso kenan! Ya haka meya sameki a baki?”
“Hmm sekin tambaya ne? Mama ce mana anga Baba baya gida kowa secin zali na yake wallahi Allah ze sak’a min.”
“Me kikayi mata?” Lubiee tayi tambayan tana dariya.
“Hmm kede bari! I’m taking you guys for a treat today” nan ta curo 2k d’in ta nuna mata.
“Wannan ba kud’in Evergreen da akace mu saya bane?”
“Wannan kud’in kashewa zan ba Evergreen da zan sai se Baba ya dawo zan sake tambayarsa” nan ta labarta wa Lubiee abinda ya faru jiya alokacin har sun isa class suna zaune.
“Chab! Lallai Zeezee baki jin tsoron Allah, kina wuta ina binki da nuclear bomb!”
“Ke bazaki gane bane ‘yan gidan namu ne seda haka wallahi kawai dan Baba yafi sona suke min bak’in ciki shima Ya Ibraheem sena tambayeshi kud’in”
*** During break Zeezee ta had’a friends nata both maza da mata ta kaisu school kiosk nasu tayi musu siyayya kowa se hailing nata yake ana tashi taje ta tsaya bakin gate yadda zata iya hango motan Ibraheem koda yazo, bada jimawa ba yazo ya d’auketa suna isa gida ta zarce ciki Baba A’ee da Mama ta tarar zaune tsakar gida suna shan iska daga lungu guda “sannu Mama” tace sama-sama “sannu Baaba.”
“Zo nan!” Mama ta kirata, ba gardama tajeta “gani”
“Baki iya gaisuwa bane kokuwa bakiga Baaba bane?”
“Ba nace mata sannu ba? Ko beyi ba?”
“Sannu gaisuwa neh?”
“Nikam da Allah daga dawowan mutum ko abinci beci ba ahau shi da surutu ina wuni Baaba shikenan?”
“Ki cigaba kinji wallahi ba inda rashin kunya ze kaiki sannan kuma ina reciept na textbook da kika siyan?” Kai tahau sosawa tana tunanin wani k’aryan zata had’a “ehemm dake fa nake ina receipt d’in?”
“Ji Mama sekace school fees aka biya da za’a bada reciept.”
“Uhn-uhn fah!”
“Toh kije makarantar mana ki tambaya in baki yarda ba ni yunwa nakeji” tana kaiwa nan ta bar gun.
“Oh!” Baaba da tun shigowan Zeezee bata iya tace komi ba ta sauk’e ajiyar zuciya “abinda Zeezeen namu ta koma kenan muna ji muna gani? Gaskiya Alhj be kyauta ba ko kad’an kuma kema da naki Hafsah bazan b’oye miki ba.”
“Kamar ya da nawa Baaba? Da ace ita kad’ai ce ‘ya a gabana se ya damen amman inada wasu hud’un wanda ko a ina nasan za’a yaba da tarbiyyansu wallahi ko Allah baze kamani ba, nayi magana har na gaji, tun yarinyan nan bata kai haka ba nake yiwa Alhj wa’azi amman never once did he ever listened to me, me zanyi toh? Akanta sena lalata rayuwar aure na? Inma zanyi sena bari sena aurar da Yasmeen. Ai munanan tare wallahi wataran Alhj seyayi kuka da hawaye akan Zeezee tunda ya miyar da ita *_YAR GATAN_* da batada flaws.”
“Amman haka zaki zuba ma ‘yar da kika haifa ido tana lalacewa?”
“Toh ya kikeso inyi? Daman duk inda aka tara mutan arziki ba’a rasa na banza cikinsu, haka haihuwa ma wata nata gabad’aya haihuwan ma na asara tayi ba na arziki cikinsu kuma bawai Allah yayi hakan bane dan bayi sonta sedan ya jaraba ta, ni kuma da Allah yaban har hud’u masu hankali da tarbiyya se ink’i gode masa nayi hauka sabida d’aya ta tab’arb’are min? Wannan ma jarabawace kinsan kalan halin Alhj towards Zeezee a banza bazasu samin hawan jini ba wallahi is better in fita daga harkansu khalas! Muna nan shi da kansa wataran zeyi regretting ba shi kad’ai ba harta ita.”
“Allah shige mana gaba toh ya ganar dashi gaskiya since before its late.”
“Ameen deh da yafi mai dan wallahi in Zeezee ta cigaba da haka banga na mijin da zezo ya iya da ita ba.”
★*★*★*★
_A week later..._
Sosai Zeezee ta gogu da bak’in wahala cikin sati biyun da tayi ba Baba, muguntan yau daban na gobe daban take samu gun yayyunta gashi ko uffan Mama bata ce musu, ita kuma ko yankata zasuyi bakinta baiyin shiru, Allah Allah take Baba GATAN ta yadawo. A hanyan dawowa daga Lagos to Bauchi armed robbers (‘yan fashi) suka tari motocin d’iban kayan Baba guda biyu daya cika su dim da kayaki suka gudu dashi basu barshi da komai ba. It was such a great lost saboda gabad’aya kud’in account nasa yayi emptying yayo wannan siyayya, abinda yarage a account d’insa sam baida yawa ko kiran Mama ya sanar da ita wannan k’addaran da Allah ya turo mai ma be iya yayi ba sede still kamar yadda Allah yace kowacce k’addara na tare da sauk’i, Allah yayi armed robbers basu k’wace mai motan dayake ciki ba Subhanallahi! What a great lost.
_Three weeks later..._
A takaice kusan rayuwan kowa ya soya a gidan especially na Zeezee da batasan meye k’addara ba balle ta rungumeshi, wai ahakan ma don da taimakon Ibraheem da Mama atimes. Gatsau! Kamar yadda ta saba shiga d’akinsu Mama ba sallama ta fad’a yau ma, direct wajen sa ta nufa, “Baba a canza min waya Abban Lubiee ma ya canza mata nata”
“Zeezee ina zan samu kud’in da zan sai miki sabon waya? Aiint you aware of what happened to me? Na rasa komi fa Zeezee, ki cigaba da sani a addu’a Allah maido min da arzikin da yafi wancan ba waya ba ko jirgi kikeso zan sai miki.”
“Har se yaushe kenan Baba? Haka zan yita zama da akwalan waya?”
“Zeezee sata kikeso inje inyi ne in sai mikin? Kema kinsan inda akwai zan saya miki ko bakisan babu bane?”
“Ni wallahi a canza min waya” nan ta hau bubbuga k’afa.
“Zeezee nace babu kiyi hak’uri mana ke bakisan in babu bane?”
“Ina kuwa ta sani?” Mama dake zaune kan Sallaya tayi maganar bayan sauraronsu datayi, “yarinya tun tana ‘yar k’arama ka saba mata da getting whatever she wants whenever she’s in need, never once did you showed her akwai state of emergency, baga irin ta ba yanzu yarinya is thirteen (13) years old amman batasan meh ake nufi da babu ba, kad’an ka gani ai wallahi. Malam bahaushe beyi k’arya ba kaso d’anka duniya tak’i sa, kak’i naka duniya ta sosa.”
“Kai! Kai! Kai! Meh haka da wannan zance? Meyayi zafi? Meya kawo zancen wani kak’i d’anka duniya tak’i ta, me hakan?”
“Ai gaskiya d’aya ce Alhj kuma daga k’in jinta se b’ata you know right what I mean kuma ka cigaba, kar fa ka manta Zeezee ‘ya mace ce in Allah ya barta rai da lafiya dole wataran zatayi aure ka gayamin wani mijin ne ze iya taking halinta, ace ance wa yarinya babu sarai tasan abinda ya sameka weeks back amman dake batada wayo tazo tana ce maka ka sai mata waya ko ni zaka sai ka siya mata wayan bansani ba.”
“Toh ya isa haka! Zagin ya isa haka, ce miki akayi haka zata cigaba da zama ne? Ai tana girma tana dad’a wayo yanzu ada da take k’arama har zagi batayi neh? Yes tanayi yanzu kuma fah? Tun da ta shiga primary one ta sake d’aga hannu ta zageki ko nine a gidan nan? Hak’uri duk zamuyi amman dekam karki sake cewa K’anwata batada wayo.”
“Wannan kuma ku ya dama dan ni bazan cigaba da zama anan ‘yan unguwa suna zagi na ba, ina aurar da Yasmeen zan koma garinmu incigaba da zama na kai da K’anwarka se kusan inda dare ya muku gare ya waye muku” tana kaiwa nan tayi excusing kanta.
Sosai words na Mama suka ratsa jikin Baba amman sede shi bayason ganin fault in Zeezee, hannunta ya kama ya zaunar da ita gefensa “karki jita kinji K’anwata? Ki tayani da addu’a ina samun kud’i zan canza miki wayan kinji?”
“Toh” tace “zan koma d’aki.”
“Yauwa K’anwata kiyi hak’uri kinji?”
“Toh Baba Allah kawo kud’i.”
“Ameen K’anwata, ameen ameen.”
~* ~* ~*
D’akinsu Ibraheem ta wuce tayi sallama kaman ba ita ba “wa’alaikumus-salam” ya amsa.
“In shigo Ya?”
“Eh shigo” bayan ta shigo tanemi gu a k’asa ta zauna for the first time, “Ya ance mu sayi Evergreen solution na junior waec namu.”
“Nawa ne?”
“N2,000 ne.”
“Toh naji Allah ya kaimu gobe.”
“Ameen nagode” tana kaiwa nan ta mik’e ta koma d’akinta dubu biyun da ta karb’a gun Baba jiya ta ciro sannan ta murmusa wayarta taja ta kira Lubiee bayan sun gaisa tace, “ke yanzu na damparo Ya Ibraheem gobe yace ze bani.”
“Ohh! Zeezee yanzu bayan abinda yasamu Baba still sekinyi masa cuwa-cuwa.”
“Toh ai dubu biyu ne bawani kud’i dayawa ba kuma da nasan zan biya na Ya Ibraheem kashewa zan.”
“Uhn-uhn fa Zeezee, atleast kid’an ji tausayin Baba kiga yadda yake sonki fah.”
“Ke! Dake da wa’azin uwaku kinji ba! Semun had’u a school gobe, bye!” Tayi hanging.
*© MIEMIEBEE*
👄👄👄👄
www.beeenovels.blogspot.com
1 comment:
hmmmmm
Post a Comment