Wednesday, 14 December 2016

‘YAR GATA CE!

BY MIEMIEBEE
PAGE 13




   _I’ve recieved your message *Khadija Shehu Musa* and I want to thank  you in person for the love and support, ILY too💕 this page is dedicated to YOU #OneLove_

   _*A/N*_
  _Assalamu Alaikum everyone, I usually don’t say a thing on matters like this but I think its high time I do now, ku sani your negative comments will never stop me from continuing with what I’ve started. Na farko dana fara rubutun nan ba wacce na cukume mata kwalar riga ko bakin zani nace dole seta karanta min littafi in kinga bazaki iya karantawa ba fine quit it there are thousand of books out there sekije ki karantasu amman kam BAZAN TAB’A TSARIN RUBUTA NA BA saboda tun farko dana fara bada idea'n wata na fara ba dan haka dan ke ko ita bazan canza tsarin labarina ba wacce taga bata k'aruwa dashi walillahil hamd seta bar karantawa. Duk me hankalin da ya zauna yasan akwai babban darasi cikin wannan littafin saboda dole ILLAN GATA ze biyo baya, ku baku tsaya kunga k'arshen littafi naba kuna judging d’ina, phew!😅. Masu cewa wai zagin Mama da Zeezee takeyi is too much inku baku tab'a ji ko gani ba toni nagani da idanu na inda 'ya ke zagin uwa infact abinda ke faruwa mostly kenan a rayumar ta yau and dole agyara kokuwa muna tare da babban hatsari. Ni ba anyhow nake rubutu ba duk books d'ina akwai life lessons ciki kamar yadda wannan ma darusan suna nan fitowa one-by-one wanda already wasu masu tunanin har sun fara gano hakan. I just want to tell y'all masu cewa littafi na baida direction su sani cewa reading is not by force kamar yanda ban saki karantawa ba seki bari dan kanki tunda yana b'ata miki rai ba dole a duniya. Fans dina masu sona kuma thanks y'all for the support, I LOVE YOU ALL, INA TARE DA KU!_


          ***********
    Tsaye take a tsakiyan d’akinta tana sanye da blue vest meh crossed arms seda ¾ black leggings, kanta kitson shade biyu ne wanda ta kama k’arshen da ribbon jaa da alama neman abu take bata gani ba danko gabad’aya d’akin nata upside down yake, d’aki ne me kyan gaske komi cikinsa combination na dark and light pink ne ba’a cewa komai sede masha Allah, dogon tsuka taja sannan ta d’au laptop nata ta fice daga d’akin a fusace tana k’walla wa Baaba meh aikinsu kira “Baaba! Baaba! Baaba!”
  “Na’am” dattijuwar ta amsa tare da katse sharan da take.
   “Ina kika kaimin USB na?”
  “Meh kuma USB Zeezee ban tab’a kominki ba, d’akin naki kawai na share.”
  “Bawanin nan kullum sede baki shiga min d’aki ba se na rasa abuna ni wallahi bana so kije ki d’au min USB na kawai” ana cikin haka Mama ta shigo parlour’n “ya haka Zeezee mawa kike d’agawa murya haka?”
  “Ma Baaba haka kawai kullum tayita canza min position na abubuwa na ni banaso abanza ta b’atar min da USB yanzu.”
     “Bakida hankali ne? Baaban kike cewa haka? Batayi jika dake bane?”
  “Wannan kuma ku ya dama nide kar a sake tab’a min abu na, ina wayana in kira Baba ya sai min sabo” ta k’are maganan dai-dai ta shiga d’akinta ta musu banging k’ofar. Binta Mama tayi da kallo sannan ta kad’a kai “yi hak’uri Baaba kinsan halin Zeezee addu’a kawai zamuyi mata.”
  “Ba komai Maman Zeezee ai yarinya ce.”
  “Kuma daga yau karki sake share mata d’akin, tunda da kin share se tace abinta ya b’ata.”
  “Maman Zeezee beyi zafi haka ba.”
  “A’a Baaba karki sake ni na fad’a miki.”

_Back in Zeezee’s room..._
   “Hello Baba?” Tayi maganan a shagwabance.
  “K’anwata ya haka? Meya sameki?”
  “Baaba ce” tayi stating almost like crying.
  “Me tayi miki kuma?”
  “Ta b’atar min da USB na.”
  “Shine abin damuwan? Bari yanzu zan aika Omar ya siyo miki kinji?”
  “Toh yaje yanzu.”
  “Angama K’anwata shikenan?”
  “Eh shikenan nagode” tayi hanging. Data connection ta bud’e ta hau whatsapp, group nasu na LYS STARS ta shiga tana glimpsing chats d’in data gama taje kan contact na Lubiee tayi mata sending;
   _‘Yan mata kinsan yau kika ce zakizo koh? I will be waiting for you_.
   Kafin ta sauk’a Lubiee ta hau tayi replying nata back;
   _Ina tuni Babe, Ya Salman nake jira by 3 in shaa Allah zan iso akwai gist fah, Ahmed yace yana son Lailan Jss 1B se nazo deh!_ Zeezee na gama karantawa tayi replying nata;
   _Sekin iso I can’t wait_ nan ta kashe datan ta had’a wayarta chargy ta baro d’akin.

  *

    ~* ~* ~*
  “Ya haka kana tsaki kai kad’ai?” Ibraheem dake sake da headphone akansa amman ba komi yakeji ba ya jefa wa d’an uwansa Omar tambaya.
   “Mschw! Wannan Baba da Zeezee mana wai inbar duk abinda nake inje in siyo mata USB tayi misplacing nata.”
  “Shine abin tsakin? Sekace sabon abu, yaci ace ka saba ai yanzu”
  “Ai dole kace haka saboda kaga kai babba ne yanzu ana isolating naka a matters haka wallahi yarinyan nan b’ab’b’ala ta zan mschww!”
 
   “Wai ina Ya Omar ne beje ya siyo min USB’n bane? Inafa so inyi amfani dashi” Zeezee tayi maganan tana shiga d’akinsu Omar.
   “Ke ban hanaki yawo cikin gidan nan da vest da ¾ leggings ba? Ce miki akayi gidan arna ne? Maza wuce kije kisa kaya” Ibraheem yayi scolding nata.
  “Haaa’a! Jimin mutum, nikam ka barni sekace wani Babana ka tsaya kana wani gaya min abinda zanyi bale ma ni ban maka magana ba kowa yayi harkan gabansa, Ya Omar USB na” ta miqa hannu nufin ya sa mata.
  “Ni kike gayawa magana?” Ibraheem yayi maganar a fusace tare da mik’ewa, ganin haka tasa gudu amman ina taku d’aya yayi ya cafko hannunta “wayyo Allah Baba na kayi hak’uri, wallahi bada kai nake ba dan Allah karka tab’ani na tuba.” rank’washi me d’ankaren zafi ya danna mata akai “waye sa’anki anan?” Tana kuka tace, “wallahi babu duk kun girmen kayi hak’uri dan Allah.”
  “Shegiya me kan kwa-kwa kawai ki sake min rashin kunya kiga abinda zan miki” ya turata seda ta fad’i, harara ta watsa masa ganin bai ganinta “mugu kawai” ta fad’i chan k’asa k’asa yadda ita kad’ai taji me ta fad’an, miqewa tayi a wahalance ta takai bakin k’ofa tace, “mugu kawai da wani farin fuska kaman k’osai Allah ze sak’a min kai kuma Omar kaje ka siyomin USB na” tana kaiwa nan tasa gudu binta Ibraheem yayi a guje se bayan Mama taje ta lab’e, “meh haka? Sakeni nikam! Kije kiyi rashin kunya kizo kina b’uya min a baya, sakeni!”
   “Wallahi Mama yarinyan nan ta kiyaye ni.” Ibraheem yayi maganan yana nunata da yatsa.
  “Ai kazo ka d’auke ta ka mata duk abinda kaga ya dace shegen rashin kunya ne da ita.” Jin haka Zeezee ta sake dandame jikinta a na Mama tana ihu dan kanta Mama tabawa Ibraheem hak’uri ya fice, “wallahi Zeezee ki sake kibar halin nan naki kin mai da manyan yayyun ki tamkar kece babba bakijin tsoron idonsu?”
  “Nikam da Allah! kullum sede kita scolding d’ina su baki ganin laifinsu ai nasani Baba kad’ai ke sona a gidan nan kuma zaki gani” tana kaiwa nan ta shige d’akinta.

   Bayan sallan Azahar Baba ya dawo gida har alokacin Omar beje ya siyo wa Zeezee USB’n ba, d’akinsa ya wuce direct alokacin Zeezee ke fitowa daga d’akinta sukayi clashing sekace ‘yar yarinya taje ta rungemeshi ya d’agata sama “Omar ya siyo miki kuwa?” Kai ta kad’a “yak’i shikuma Ya Ibraheem ya nank’washeni a kaina.”
  “Haka ya faru? Bari ina zuwa, kinci abinci?”
  “A’a”
  “Jeki d’iba kici ina zuwa” yana sauk’eta ta wuce kitchen su Mariam da Yasmeen ta tarar se aiki suke da Mama tana tayasu.
  “Ina abinci na?” tayi tambayan ma dukansu, ba sannu da aiki ba komai.
  “Kinba ma waye ajiya kike wannan tambayar?” Yasmeen ta watsa mata harara. Hararan ta miyar mata itama, “ma ke na baiwa, ni ina abinci na? Tun d’azu ku d’aura lunch kunk’i sekun bari yunwa ya gara mutum.”
  “Wai waye sa’anki anan? Zan gaggaura miki mari fah!” Mariam ta  bud’e mata ido.
  “Mschww!” Zeezee taja tsaki, ganin Mariam ta miqe Mama tayi saurin dakatar da ita “yi hak’uri Mariam barta tana yima kanta ne” nan da nan suka sauk’e girkin Zeezee ta matso da plate nata “asamin.”
  “Baza’a san ba kinyi sallah neh?” Mama ta tambayeta, shiruu Zeezee batace komi ba dan kuwa batayi sallan ba, “tambaya nake kinyi sallan Azahar?”
  “Ni meh had’in abinci da Sallah kisa min kona fad’awa Baba.”
  “Jeki gayan maras kunya kawai” dai-dai nan Baba yashigo kitchen d’in “yauwa Baba kaga Mama tasamin abinci wai o’o.”
  “O’o kamar ya? Sa mata abinci mana Hafsah.”
  “Kasan kuwa yarinyan nan batayi sallah ba infact bata ma sallah kullum ko an sata se baza tayi ba.”
  “Bata sallah?” Baba yayi maganan unbelievably.
  “Wallahi k’arya ne” cewar Zeezee.
  “Toh kinayi neh?”
  “Wallahi batayi Mama” cewar Yasmeen.
  “Rufa min baki abinda kika iya kenan” Baba ya tsawata wa Yasmeen. “Zeezee wai baki sallah?”
  “Baba inayi wallahi kawai yanzu ne ban yiba saboda ina jin yunwa amman ina gama ci zanyi.”
  “Yauwa K’anwata I trust you ai” k’wace serving spoon na hannun Mama yayi ya zuba wa Zeezee potatoe porridge d’in da nama biyar akai.
  “Haba Alhj ya da haka? Mukuma sauran me zamu samu?”
  “Ke ko kunya bakiji ba me zakiyi da nama tsohuwa dake?”
  “Nide ba tsohuwa bace kuma naga wanda suka fini shekaru ma sunaci, kuma Mariam ku d’ibi biyar-biyar d’in, yarinya ko aikin d’aga tsinke batayi sede taci tayi kashi tayi rashin kunya kuma aka tashi ita za’a na bata duka naman miya.”
  “Kanki akeji” plate ya ja ya d’iba nasa suka fice da K’anwarsa.

*** _2:45PM_
  Baba ya tara iyalan sa a parlour dan raba musu kayan babban sallan su wanda will take place in 3 weeks time. “Ina Omar?”
    “Yaje siyo wa Zeezee USB.” Ibraheem ya amsa.
  “Okay” yayi maganan yana zaro had’ad’d’un zannuwan dake cikin wani babban leda, guda goman duka ya baza a kan carpet “ina K’anwata?”
  “Na’am Baba” ta matso kusa dashi ta zauna.
  “Zab’i guda hud’un da suka miki anan-”
  “Haba! Haba! Alhj kayi adalci mana, Mariam Babban su ai ita ya kamata ta fara zab’a” Mama ta fad’a.
  “Zani ba zani bane kam? D’auka Zeezee da Allah kar kiji ta.” Gwalo Zeezee tayi ma Mama sannan ta kwasa hud’u mafi had’uwa cikin goman. “Oya kema Hafsah d’au naki guda biyu.”
  “Biyu? Ita hud’u ni biyu kuma seda ta d’auka zan d’au wallahi banaso kabata nawan, na hak’ura.”
  “Kanki akeji” ya d’au guda biyu ya wulla mata sauran hud’un kuma ya bawa Mariam ta zab’a biyu ta bawa Yasmeen biyu ana cikin haka Omar ya dawo nan Baba ya basu shaddojinsu shida Ibraheem guda uku-uku had’d’d’u masu kyau, bayan nan ya sake jawo wani leda ya zazzage laces biyar ciki nanma yace Zeezee ta zab’a biyu bayan ta zab’a ya raba wa Mama da su Yasmeen ragowar haka kaman suyi kuka sukayi godiya suka watse. D’aki Zeezee ta nufa da kayakin sallanta se tsalle take nata guda six (6) na sauran 3-3 ganin ta wargaza wardrobe natan d’azu agarin neman USB kuma gashi tana son sa sabin kayanta ciki yanzu gashi she is not in the mood of preparing her wardrobe taje tasamu Baba tayi ta mai shagwab’a ita akira Yasmeen ta gyara mata wardrobe nata, bayan taje ta kira Yasmeen Baba ya isar mata da abinda yakeson tayi ai atapir tace ita baza tayi ba ai da gan-gan Zeezeen ta wargaza kayakin, ido sosai Baba ya bud’e mata sannan ta amince se kumbure-kumbere take.
  Nan da nan ta shiga gyara wa Zeezee wardrobe nata ana cikin haka Lubiee tazo, parlour’n Baba Zeezee ta kaita suka yita hira kaman ba gobe suna game, bayan Yasmeen tagama gyara mata wardrobe d’in suka koma d’akinta taciro wa Lubiee kayakin sallanta seh 5:30PM Lubiee tace zata tafi bayan sallamarta da Baba yayi yasa Ibraheem yayi dropping nata nan Zeezee tace se ta bisu itama. A bayan mota suka zauna su biyu se k’us-k’us suke har suka yi dropping nata.

   “Toh bazaki dawo gaba bane sena mauje ki?”
  “Ayyi Ya-”
  “K’aniyanki nan waye driver’nki? dawo gaba nace!” Harara me rai da lafiya ta watsa mai batasan ko ya ganta ta mirror ba, bayan ta dawo gidan gaba ya seta kanta ya sake mata rank’washi me zafi, “Allah ya is-”
  “Meh kikace?”
  “Babu” hannunta yakama da niyar murd’awa aiko tasaki ihu “dan Allah Ya kayi hak’uri wallahi bazan k’ara ba.”
   “‘Yar banza kawai ai ko kiyi behaving kanki ko na b’ab’b’ala ki kamin mu isa gida wallahi” daga nan Zeezee bata sake ce mai komi ba dan lafiyarta tayi shiru on their way back home budurwan Ibraheem Fateema ta mai waya kan tana buk’atan ganinsa nan ya sha U-turn Zeezee na ganin haka tace, “ni wallahi ka kaini gida kafin nan kaje gun Fateeman.”
  “Magana kike?” Ya mata sending wani dirty look dan kanta tayi tsit ahaka suka isa Ibraheem yasata tabar motan Fateema ta shiga. Se hira sukeyi tun Zeezee na hak’ura taga bazata iya ba ta mik’e taje ta samesu “ni wallahi kashi nakeji hiran ya isa haka.” Kallonta Ibraheem ya tsaya yi totally out of words.
   “Zeezee toh muje in kaiki ciki kiyi?” cwar Fateema.
  “Ni bana sharing toilet, na gidanmu nakeso” baki wangalau Fateema ta bud’e tana kallon Zeezee dake murgud’a mata baki sama-sama “toh Baby se next time baby sis is in need kuyi ku tafi.” Har a yanzu Ibraheem ya kasa cewa komai haka yana gani har Fateema ta shige gidansu Zeezee ta bud’e motan ta shiga “toh kayi sauri mana Ya, yafa matseni” bece da ita komi ba ya kunna motar suna cikin tafiya sunzo ta old GRA ya yi parking gefen hanya “meh kuma zamuyi anan Ya?” Nanma bece komi ba ficewa yayi kawai ganinsa tayi ya karyo itche d’anye yana nufan motan kafin tace zata bud’e k’ofar ta har ya isketa, fincikota yayi ya hau zabga mata itchen a k’afafunta daman ‘yar guntuwar ‘yar kanti ne a jikin ta tana ihu tana basa hak’uri amman ina se k’ara mata yake kasancewar hanyan shiru ba hayaniya, seda ya nad’a mata na jaki sannan ya barta lokacin har wani sama-sama nishinta ke. “Kad’an kika gani bake fitsara da rashin kunya ba? Muna tare dake ai gyara miki zama zanyi maza miqe ki bud’e motan ki shiga.”

   Har a yanzu kuka take wane dan shi aka turota k’afafunta har sun soma kumbura sunyi jaa dan azaba, yi tayi kamar bata jisa ba, bulalan ya d’aga as if ze sake zaneta “dan Allah kayi hak’uri zan shiga.”
  “Oya!” Yayi commanding nata, motar ta bud’e ta shiga shima haka sede har a yanzu bata bar kukan ba. “Kuma kimin shiru wallahi in bakiyi ba sena k’ara miki wanda yafi wannan” kukan tacigaba dayi “aww! Baza kiyi shirun ba kenan?”
  “Zanyi dan Allah kayi hak’uri.”
  “Oya yi shirun kuma wallahi kikaje kika fad’awa Baba na dakeki ya kirani yamin suratan banza zakiga abinda zan miki, kinfi kowa sani na” a da tanada niyyar sanar da Baba abinda yayi mata amman jin ya kashe mata warning ta fasa saboda tasan halin Ibraheem sarai mugu ne first class ma kuwa. Haka tana ta sobbing har suka samu suka isa gida aranta tana meh tunanin wani abin zata yimasa ta rama.

 
   Tana fitowa daga motan ta buga murfin wane zata b’alla ko uffan bece mata shide da murfin motansa ya b’alle da seta raina ma kanta wayo. Karo taci da Baaba A’ee gbam! “meh haka mutum na tafiya bai ganin gabansa” tayi maganan ba tare da tasan da wa ma sukaci karon ba.
  “Toh Zeezee lafiya dai koh?”
  “Aww Baaba kece sannu nasha ma ‘yan iskan almajiran nan ne.”
  “Sannu Zeezee ba gaisuwa?”
  “Nikam da Allah kullum gaisuwa baki gajiya da amsawa ne?” Bata jira jin meh A’ee zata ce ba ta wuce ciki, baki A’ee ta tab’e tace, “Allah shiryeki Zeezee.”

   **** _8:17PM_
   Tailor’n su ya iso nan kowa ya fito da zannuwansa bayan ya gama a’aunasu suka zab’i styles nasu Baba ya bada advance har tailor yazo tafiya Baba ya tsayar dashi, “yauwa Shaheed d’inkin nace ka tabbata seka gama dana Zeezee kafin ka fara na sauran saboda kaga ita yarinya ce, su ko ba kayan sallah zasu iya yin sallan ka gane ai?”
  “Eh Alhj zan fara da nata in nasamu nayi koda biyu ne a natan sena tab’a na ‘yan uwan nata.”
  “O’o ni seka gama min duka six d’in” Zeezee tayi chipping in.
  “Bakida hankali? Mu kuma fa? Shaheed please kar ka saurareta” cewar Mariam.
   “Lallai sannu toh se an gama da natan za’a tab’a naku maras kunya kawai” Baba ya sanar da ita.
  “Allah sarki Baba-” inji Yasmeen.
  “Allah sarkin K’aniya,  sam ku baku san meh kara wa k’anwarku ba? Se an gama nata a fara da naku ka jini ai Shaheed? Se mun jika nan da 2 weeks d’in.”

 
 
*© MIEMIEBEE*
👄👄👄👄
  www.beeenovels.blogspot.com

1 comment:

  1. fatan farin ciki gareki
    Allah yakara basira

    ReplyDelete