Sunday, 20 November 2016

HEEDAYAH!


                9⃣7⃣
   written by miemiebee👄

           Exactly 3:00PM aneesa da rayyan suka wuce wata eatery inda suka yi getting to know more about each other, anan rayyan yasan aneesa bata taba yin soyayya ba meaning he'll be her first love sede be boye mata ba yace "aneesa koda i'll love u in the future, heedayah will always have a place in my hrt" itako dan yadda takesonsa ba ta damu ba. A wasa a wasa soyayya me karfi yafara shiga xuqatan su, dukda rayyan baya wani santa kamar yadda takeson sa shide kawai dan maminsa yake kula aneesa dakuma dan small feeling dayake da mata.
        Garin kano gdan hjy heedayah! 3 weeks later kimanin 1 month 3 weeks da auren su knan.
          Sanda naci tuntube dan wani uban dotti da kuran da gdan heedayah yayi kasancewar ummu jalila tayi tafiya bame ce mata yi ko bari dan haka tasamu kanta gashy tunda tayi aure mummy batai visiting nata ba. Wanke wanken ma don moha ne yakoma mata yanzu kullum kuwa setayi kukan rayyan nata gashy ba inda take zuwa a daki take wuni ta tashy. Tana zaune a dakinta tajiyo karar doorbell nan gabanta ya fadi ita tsoronta kar ummu jalila ce asirinta ya tonu. "waye ne?" Muryan mummy taji tana "nice bude." Hankalin heedayah in yayi dubu be tashy ba "toh ina zuwa barin dauko key," dakin don moha ta nufa ta samesa yana bacci kansa ta hau tafara tapping nasa tana jijiqa sa itan datace barata taba bari ya tab'a ta ba, sega yau ita ke tab'a sa "muhammad muhammad don moha wake up pls" da idanunsa a rufe yace "what is the matter?" Tace "dan Allah katashy"**muryan mummy tajiyo tana "heedayah neman key'n ne har ynxu?"** heedayah tace "don moha pls mummy ce tazo nd kasan yadda gdan nan yake duka zata min in taga bana shara pls kaje ka bude kace mata banda lfya ne pls pls pls." Don moha yace "is that it? Shine kka ta dani ina bacci?" Pillow yaja ya rufe face nasa dashy, pillown ta ja "pls mana don moha" tafara kukan munafirci "wlh duka na mummy zatayi, dan Allah kace mata banda lfya ne sesa bana shara kwana biyu."
        Ras maganan ya fada kunnen mummy da nanny da suke zagaya ta back door suka shigo kofar dakin ta wangale ran mummy in yayi dubu be bacy ba kallo daya heedayah ta mata tasan shes in trouble yau jikin don moha tashiga tana "pls karka bari ta tabani pls don moha," daidai bayanta mummy tazo sa mata mari don moha yasa hannunsa se marin yasauka kan hannunsa a rikice heedayah ta jiyo kafin ace meh sekukaji tas! A fuskar heedayah tuni ta fara kuka. Mummy tana huci "erin tarbiyyan dana baki knan? Ko a waje aka cemin ga abinda kkeyi baran yarda ba," hannunta taja ixuwa parlour don moha ya bar gadon shima yabisu a tsakiyar parlourn mummy tayi wurgi da ita, "kalli parlournki heedayah me haka? Sekace gdan mahaukaciya, bakida hankali ne?" Don moha ne yayi karfin hali yace "mummy is not like that, there must be a misunderstanding here." Mummy tace "yimin shiru muhammad kaima ina zuwa kanka" kan heedayah ta nufa ta fara ball da ita nanny da bata taba ganin abu haka ba ita da don moha suka shiga da kyar suka iya suka kwato heedayah dake ta kuka kamar jaka. Shima don moha ji yake kamar yayi kukan. "Maza wuce kije ki dau tsintsiya ki fara shara, bada ke nake mgn ba!" A rikice ta tashy taje ta dau tsinstiyan "baraki fara sharan bane, ko sena kara miki?" nanny tace "mummy bari muyi tare kinga gdan yyi dotti dayawa", mummy tace "ba abinda xakiyi ita kadai zata share ko ina a gdan nan." Mummy ta duba sauran dakunan taga harda cobwebs a bakin kofofin alamar ko shiga dakin ba ba'ayi bale a share. "Muhammad ynxu da girmanka da hankalinka kabar heedayah tana tsula shashanci a gdan nan muna gari daya baraka kirani ka irga min ba?" shiru yayi tace "am very disappointed in you ai heedayah kadan kka gani muna tare dake a gdan nan kuma sena gaya wa daddy'nki yasan rashin hankalinki." Ana cikin haka aka danna doorbell don moha ya tashy ya bude ummu jalila ce yanxu dawowanta daga tafiya amman ko gdan ta bata shiga ba tafison tazo taga halin da heedayah da don moha ke ciki. Sallama tayi da mummy bayan sun gaisa ummu jalila tace "heedayah ya haka? Kar ki gayamun tun tafiya na for the past 2 weeks baki sakeyin shara ba?" Mummy tace "aww kema kin sani knan," ummu jalila tace "mahaifiyarta ce ke ko?" Mummy tace "unfortunately har kunyan fadin ni na haife ta nake dan wannan abin kunya ne," heedayah nata shara langwai langwai har ynxu tana kuka. Mummy ta cigaba "muhammad amman ban taba tsammanin kaima hankalinka kamar na heedayah bane," ummu jalila tace "ko kadan ba haka bane, muhammad nason heedayah ne sosai har ya kaiga baya ganin laifinta..." nan ta kwashe labarin komi tabawa mummy.
      Hannu mummy tasa a kai tana salati "heedayah! Wanke wanke kkesa muhammad? Nashiga uku ynxu kinmin adalci knan? Upon duk yadda nayi training naki da abinda zaki saka min knan?" Tuni mummy tafara kuka nanny da ummu jalila suna bata hkr. Haka as a punishment mummy tasa heedayah share gdan kap, ta kuma yi mopping tayi dusting tare da clearing duka cobwebs da suke gdan, bayan heedayah kamar ze balle sannan kuma ta aza girki. Kafin su mummy su tafi tamata wa'azi da nasiha sosai heedayah se kuka takeyi tana neman gafarar mummy dan bata taba ganin bacin ran mummy kamar na yau ba! Ummu jalila ma ta kara nata akan na mummy sannan suka jama don moha kunne shima kan yadena barin ta tana abinda taga dama, ahaka suka tafi.
          Bayan don moha yamusu rakiya ya shigo yaga heedayah bata parlour dan haka ya shiga dakinta yasmeta kwance kan gado se sharba kuka takeyi ya nufa kanta yasa hannu kan bayanta yana shafawa a hankali, "heedayah is okay pls kibar kuka kinji? Yi hkr am so sorry this is all my fault..." haka yata bata hkr amman ko uffan bata cemasa ba se qara karfin volume na kukanta take tana kiran sunan rayyan irin ga rayyan hero ko life saver dinnan.
            Washegary! heedayah ta tashy da severe ciwon mara can anjima period nata ya iso ba abinda takeyi a gdan se kuka duk tasa hankalin don moha ya tashy gashy tasha mgn amman sam ciwon cikin yaki bari, gana baya ma kasancewar aikin data sha jiya kwata kwata taki cin abinci black tea dinma dakyar tasha yadda kukasan don moha shima ciwon yake duk hankalinsa ya tashy ya kira mummy kuma gaskia he can't nanny kuwa tace karya sake kiranta inde mgn ze mata kan heedayah. He cant think  of any1 se ummu jalila gashy baida numbernta. Slipper nasa yasa ya fita a gurguje ya je gdan ummu jalila knocking yakeyi kamar zararre me aiki ta bude masa ya tambayeta ko unmu jalila na gda, ta amsa da "eh baran kirata".
           Bayan 'yan mintuna ummu jalil tafito "muhammad lfya? Yana ganka haka?" Don moha yace "ummu jalila I need ur help pls heedayah kamar zata mutu bata da lfya," murmushi ummu jalila tayi a zatonta ko shigan ciki ne da heedayah. Tace "toh ai ba abin damuwa bane Asibiti kawai zaka kaita abaku mgn dama haka ciki yake." Don moha yace "yau akeyinta ummu jalila ba ciki bane," ya gaya mata mp ne kuma yana jin kunya, ummu jalila dake murmushi har ynxu tace "dama taya zaka sani? Dr ne kai?"  Kunya yacire yace "bafa abinda yataba shiga tsakani na da heedayah, mp ne ke damunta pls ki taimakeni wlh kamar xata mutu tunda garin Allah ya waye take kuka." Ummu jalila ta zaro ido "muhammad! Me kace??" Dan ji tayi kamar kunnenta sun mata karya

No comments: