Monday, 3 October 2016

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 96
BY MIEMIEBEE









     “Toh ni yanzu me kikeso in mata Ya Fannah?”
“Kema ai kinsani Amal kidena biyewa Ya Anas kibata chance da take nema to hold you and be your mother bawai nace kiyafe mata bane amman kibata wannan chance da takeso dakanki zaki yafe mata in kikaji dad’inta ke bakison kisan mamanki ne?”
    “Ai nasan Ummie.”
   “Ummie ba itace mahaifiyarki ba Ummimi ce mahaifiyarki...” haka Fannah tariga ma Amal nasiha seda ta kashe mata jiki.
    Dawowan Anas ya taho ma Fannah da tuwonta nan tasamu ta kora yunwa shikuma da Amal suka wuce kitchen dan dafa nasu kamar Anas yasani ya tambayi Amal ko Fannah tamata maganan Ummimi bayan fitansa, bata b’oye masa ba ta fad’a masa zahirin gaskia. “Ya Anas don’t you think is about time mu bawa Ummimi chance to be our mother? Wallahi wa’azin da Ya Fannah tamin ya mugun tsorata ni.”

    “Ai dama nasani, nasan hakan ze faru kinaji na ba bawani chance da zakibawa Ummimi am I clear?” Baki na rawa tace “yy.. Yes.”

   _Washegari..._
   Da sassafe Ummimi ta tashi tayi wanka sannan ta rok’i Ummie data rakata kitchen dan nuna mata inda postions na plates da sauran utensils suke hakan kuwa akayi breakfast me rai da lafiya favorite na Abuu ta had’a wato doya me k’wai a jiki bayan tagama ta had’a kan dining. 8:30AM Abuu yafito daga d’akinsa cike da ladabi da biyayya ta sauk’a har k’asa ta gaishesa ba yabo ba fallasa ya amsa. “Ya Ibraheem ga breakfast chan na had’a maka dan Allah kar kace bara kaci ba kayi hak’uri please” kai ya gyad’a mata sannan yabita dining d’in taja masa kujera ya zauna sannan tasoma serving nasa tana bud’e flask d’in k’amshin girkinta wanda he can’t tell how he missed it ya buga masa hanci bayan tayi serving nasa ta had’a masa tea sannan ta koma gefe tana kallonsa a hankali yasoma chin abincin har ya k’are. “In k’ara maka ne?” Ya gyad’a mata kai dad’i sosai taji a ranta “ashe har a yanzu baka dena son doya me k’wai ba.”
   “Mesa zan dena so bayan kin riga kin saba min dashi, kefa barakiyi breakfast d’inba?”
   “Zanyi amman nafison duk ku karya tukuna, Shettima fah? Har yanzu yana kai goman safe kafin ya tashi kokuwa ya rage bacci?”
   “Keda d’anki kuma kina iya zuwa kiduba d’akin sa ai shine first room by your right.”
 
    “Toh nagode sosai Ya Ibraheem.” Seda yagama chi ta masa Allah kare ya fice office sannan ta dawo ta d’iba wa Shettima nasa a plate da tea nasa ta nufa d’akinsa a hankali tayi knocking. “Waye ne” ya tambaya. Da k’yar bakinta ya iya cewa “Ummimi ce Shettima.” Daga nan be sake cewa komai ba.
   “Shettima yi hak’uri ka bud’en kaji? Yi hak’uri please.” Nanma shiru “Shettima barin bar nan ba har se in ka bud’en k’ofan nan.” Tafi minti goma tsaye a wajen sannan Shettima ya tashi ya bud’e mata ba tare da yace mata komai ba, bayansa tabi ta ajiye masa breakfast d’in akan centre table dake d’akin.
     “Ina kwana Shettima?” Nanma be amsata ba gefensa ta nufa ta zauna kan gado. “Shettima barin iya forcing naka kayimin magana ba saboda na kasance me laifi amman kayi hak’uri ka tashi ka karya kaji Babana?”
   “Ummimi why are you doing this?”
  “Saboda inason ka Shettima, ina sonka fiye da yadda nakeson kaina.”
   “Shine kika tafi kika barmu alokacin da muke buk’atanki?”
  “Barin ku danayi shine babban kuskuren dana tafka kuwa Baba na shiyasa nakeson inyi making up for the last 15years da mukayi ba a tare ba, yi hak’uri ka karya kaji?” Hannunsa taja ta zaunar dashi sannan da kansa ta soma basa abincin yana karb’a har yagama chi. “Thank you so much Shettima na wannan dama da kabani Allah ya saka maka da alheri yakuma maka albarka.”
   “Ameen” ya amsa. Daidai nan wayarsa yasoma ringing kasancewar wayar na kusa da Ummimi tasamu daman ganin wake kira ‘honey boo’ taga rubuce kan screen d’in. Da sauri ya d’aga wayar daga dubanta sede yakasa amsawa ganin Afrah ke kira, d’an murmushi ta saki “haka Baban nawa ya girma? D’aga wayar mana to ko se surikar tawa tayi zuciya ne?” Besan alokacinda ya murmusa ba.

   “Ko kunyan Ummiminsa yake ne?”
  “Ummimi fa ba budurwa ta bace.”
  “Awww shine akayi saving lambarta da honey boo, d’aga mana kose ya tsinke ne.”
   “Zan kirata anjima.”
  “Toh wace ita? Wata lucky girl d’in ne ta sace min zuciyan one in town son d’ina?” Murmushi sosai Shettima ke “sunanta Afrah k’anwar Fannah.”
   “Wow aiko ina da tabbacin itama tana da hankali kamar Fannah, Allah tabbatar mana da alkhairi yabar ku tare.”
   “Ameen Ummimi”
  “I will love to know you better Shettima”
   “Don’t worry” yayi maganar yanasa shirt nasa.
   “Toh Babana ya naga kamar kana shirin fita?”
  “Eh makaranta zani inada lectures.”
  “Oh okay me kakeso kaci da rana?”
  “Babu ba sekin dafamin komai ba zan siya a school.”
   “A’a mahaifiyarka na raye bara ka chi abincin waje ba fad’a min meh kakeso.”
  “Ina irin macronin da kike dafa mana? Irinshi nakeso.”
   “Toh angama son Allah kiyaye kaji? I love you.” So yake yace mata he loves her too amman kuma yakasa dan haka ya gyad’a mata kai zallah. Bayan tafiyan Shettima ta share masa d’aki tayi mopping tsatsaf haka d’akin Abuu ma sannan tasake yin sabon breakfast masu Anas tare da Ummie suka fita dankai musu sede Ummie tak’i shiga tabar Ummimi ita kad’ai, securities suna ganin Ummie suka bar Ummimi tashiga door bell ta danna alokacin Anas na aka kitchen shida Amal suna had’a musu breakfast ita ya tura da taje ta bud’e ganin Ummimi ce ta bud’e tare da gaisheta kamar yadda Fannah ta buk’ace ta. Dad’i sosai Ummimi taji “Amal my princess ya kike?”
   “Lafiya.”
  “In shigo?” Daidai nan Anas yafito “waye ne Angel?”
   “Ummimi ce Ya Anas” apron d’in jikinsa yacire sannan ya k’ariso “ina kwana Anas” kamar wanda bare amsaba ya amsa “lafiya” tare da sake tare k’ofan dan kar ta samu daman shiga “wani abu ne?”
   “Breakfast na kawo muku.”
  “Ai da baki b’ata lokacinki ba we are making breakfast already zaki iya tafiya.”

    Hannu tasa ta taresa daga rufe k’ofan “Anas please karka min haka dan Allah” tayi maganan hawaye na ciko mata a ido daidai nan Fannah tafito daga d’akin sanye take da kayan bacci iya guiwarta, ganin alaman baquwa bakin k’ofan yasa takoma ta sanya hijabi sannan tafito “Habeebi meke faruwa anan?”
   “Ya Fannah Ummimi ce tazo.” Amal ta amsata.
  “Shine baku shigo da ita ba?” tayi maganan alokacin datake tsaye gefen Anas. “Ummimi please kishigo” wani kallo ta watsa wa Anas sannan tashigo da Ummimi ciki anan suka gaisa.
    “Waya miki kwatancen gidan namu?”
  “Tare da Ummie muka taho tana waje tana kuma gaisheku duka, dama breakfast na kawo muku.”
   “Allah sarki Ummimi da gajiya haka ai da baki wahalar da kanki haka ba, Anas d’an karb’i mana” yi yayi kaman be jita ba “Amal karb’i flask d’in kinji?” Ba gardama ta amsa takai kitchen hira kad’an suka tab’a wanda ciki ko uffan Anas be furta ba haka Amal ma kasancewar taga idon Anas daga k’arshe ma kitchen ya koma ya cigaba da abinda ke gabansa da Ummimi tazo tafiya takira Amal tare da miqa mata wasu hada’d’d’en porches na iphone 7s. “Gashi Habibti wannan naki ne naji Ya Anas ya siya miki iphone 7 koh?” Ta gyad’a kai “toh gashi bansani ba ko kinason maroon and red colour? best colorn Basmah da Barrah kenan I was thinking ko kema haka kinaso” amsa Amal tayi tana k’are musu kallo “sosai inason red and maroon colour Ummimi thank you.”
   “Always Habibti” ta bud’e mata hannu da nufin hug ba gardama Amal taje tayi hugging nata wani erin yanayin da bata tab’a tsintan kanta ciki ba tayi yau, tunda take bata tab’a jin dad’in hug ba kamar na yau gaskiyan Fannah our mothers are priceless sunjima a haka se kallonsu Fannah ke cike da jin dad’i ina ma Anas zebawa Ummimi chance d’innan ta zame masa uwa kamar yadda take buqata. “Toh zan tafi seko gobe in dawo kinji?” Amal ta gyad’a kai.
   “In na dawo gobe zaki bani labarin ki, kinga yanzu nasan favorite colors naki inason insan komai about you zaki min?” Shiru tayi chan ta gyad’a kai “thank you so much Amal Allah miki albarka yamuku albarka gabad’aya zan tafi” ahaka sukayi sallama. Dawowan Amal ta wuce kitchen “Ya Anas kalli porches da Ummimi ta kawo min na wayan daka sayamin amazing how tasan favorite colors d’ina koda shike tace favorite colors na step sisters namu Allah jik’an rai Barrah da Basmah ma kenan, Ya Anas Ummimi isn’t bad.”
 
   “Mesa kika karb’a?”
  “Ya Anas I’m sorry.”
  “Bance karki mata magana ba?”
  “Ya Anas she is our mother.”
  “Naji zan karb’i iphone d’ina se muga aina zaki sa porche d’in.”
  “Ya Anas I’m sorry.”***

   ★★★★
    Haka nan tun daga ranan Ummimi tacigaba da musu girki, da sauran ayyukan gida dukda abinda Anas ke mata hakan be hanata ja da baya ba saboda tasan dalilin dayake hakan alokacin data tafi shine me wayon chan dole abin yafi affecting nasa, addu’arta a kullum baifin Allah kawo ranan da Anas zeyi accepting nata as his mother ba, duk yadda yayi dan hana Amal alak’a da Ummimi yakasa as the saying goes ba a shiga tsakanin uwa da d’a, shak’uwa me k’arfi ne yashiga tsakanin Ummimi da Amal har fiye da nata da Shettima koda Amal takoma gida d’akin Ummimi ta tare, atare suke kwana da Ummimi, tamata tsifa tamata kitso har wanki haka ma Shettima tuni suka daidaita a tsakaninsu daman Abuu abinda yake jira kenan bayan ya tabbata everything is cool tsakanin Ummimi da yaranta ya dawo da ita d’akinta dad’i sosai Ummimi taji harda kukan murna her biggest dream is now a reality su Ummie da Fannah duk sunji dad’in wannan re union d’in har small party suka had’a inda Fannah tayi introducing Ummimi wa Maminta anan Ummimi taga Afrah in-law to be nata abinde se wanda yagani they turn out into a one big happy family banda Anas da duk wannan abubuwa da akeyi baima zuwa bale yaga kayan bak’in ciki har a yau bayajin ze iya yafewa Ummimi yariga ya dawo daga rakiyarta gabad’aya sede hakan be hana Ummimi fita daga harkansa ba ita ba.
   Musamman Abuu ya kira Fannah yamata godiya in person in da badan ita ba yasani da bare sake had’uwa da Ayshan sa ba, dabadan Fannah ba da Amal won’t get the chance to see her mother again, da badan Fannah ba da Ummimi won’t get the chance to see her family ever again har ta nemi gafararsu dan haka yayi mata godiya sosai tare sanya mata albarka ba iyaka. Shak’uwa na haqiqa ne ya cigaba da shigewa tsakanin Fannah da Ummimi, yadda Ummimi tad’au Amal haka tad’au Fannah tamkar ‘yar data haifa saboda irin ladabi da biyayyan da Fannah ke mata itama sekace wa Mami.

     Ummimi da Abuu dasu Shettima ne duk sukaje gidan iyayenta, alhamdulillah iyayen nata na nan da rai dakuma lafiya anan duk suka nemi gafarar Abuu akan abinda suka yi masa shekaru da dama da suka shud’e.
    Tun daga wannan rana rayuwa tayi turing perfect ma wannan family kan Ummimi da Ummie a had’e sekace ba in laws ba sosai Ummie kebawa Ummimi girma bata kuma dena yiwa Anas wa’azi ba itama fatanta Allah kawo ranan da Anas zeyi accepting Ummimi.
    Cikin Fannah se girma yake masha Allah a yanzu haka cikin nata ya tsufa yanada 8 months da sati d’aya, sosai cikin nata yayi girma yazamo ko k’wararren motsi zatayi setayi dagaske, ga wani erin tsoron haihuwan datake cikin yi a kullum ko asibiti bata son zuwa, Anas, Mami da Ummimi ke cikin kula da ita kullum, Amal tadawo zama dasu ma tak’i dan yadda batason rabuwa da Ummiminta bata tab’a sanin dad’in uwa ba se a yanzu.

  ****
     Yau ranar ta kasance Saturday zaune Fannah ke a garden tana d’an ciye ciyenta, gefenta Anas ne da laptop a gabansa yayi focusing sosai yana aiki akai. “Habeebi” takira sunansa. “Nagaji”
    “Yes Mom Hanan, Hanan na damunki ne?” Kai ta gyad’a a shagwab’ance. Laptop nasan ya rufe tare da ajiyewa kan table sannan ya matso kusa da ita yana shafa gashin kanta a hankali, “hak’uri kad’an zaki k’ara Sweetheart nan da 3 weeks in shaa Allah Hanan namu zata fito tadena damun min Flower” yayi pecking goshinta. “Yau zaki iya fita walk?”
   Kai ta girgiza mai da wuri “banajin zan iya fita yau Habeebi.”
   “Flower haka jiya mafa kika k’i fita kin tuna me Dr tace? Yi hak’uri kinji?” A hankali ya miqar da ita suka fita walk tafiya kad’an Fannah tayi tace ita su dawo gida hakan kuwa akayi.***

    _3 weeks later 2 days later, exactly 9:43AM..._
     Kamar yadda suka saba kwanciya manne da juna haka ma suke a yau sede Fannah ta kasa bacci tun bayan Sallan Asuba da sukayi, da k’yar ta miqe ta zauna dan girman cikin nata. Bayanta ke mata wani erin zafin azaba kamar tacire ta ajiye a gefe da na bayan ya lafa sekuma cikinta yahau juyi ta k’asa k’asa tun tana iya jure zafin takasa ta k’wala wa Anas kira a firgice ya tashi ganinta yayi miqe a k’asa tana hawaye tana juyi.
    “Omg! Flower what is happening?” kafin tayi magana ruwanta yayi breaking. “Anas I’m in labour please do something arrggh!” Ta saki k’ara hannunta na a k’asan mararta bayi yashige yayi brushing yafito da wuri da k’yar ya iya d’agata yakaita mota sannan ya d’ago maternity bag nata se asibiti, hankalinsa ya matuqar tashi ganin yadda Fannah ke kuka kamar ba gobe da k’yar ya iya tattara hankalinsa gu d’aya ya kira Mami ya sanar da ita, Mami ce ta sanar dasu Ummimi kusan a lokaci d’aya suka iso asibitin duka.

     Alokacin Anas na a d’akin da Fannah ke ya riqe hannunta gagam cikin nasa yana kissing kanta assuring her *_YANA TARE DA ITA_* sede sam its not helping sekaceba Flowersa ba gabad’aya tafita daga hayyacinta tana kuka tana ihu abin tausayi wane mutuwa zatayi, tana zufa yana share mata shima besan a lokacinda ya soma kukan ba sunfi minti talatin ana abu d’aya tun yana iya jure kukan nata har yakasa besan a lokacinda yafito ba he can’t take it anymore, bare iya jure pain da wahalan da Fannah ke fuskanta ba. Ummie, Ummimi da Mami ya tarar tsaye bakin k’ofan da gudu yayi kan Ummimi yayi hugging nata batayi tammanin hakan ba tsabagen yadda mamaki ya rufeta kasa hugging nasa back ma tayi. Kuka yake wane d’an yaro ya matseta gagam ajikinsa.

    “Ummimi I’m sorry, I’m so sorry please dan Allah kiyi hak’uri, please forgive me I never knew you went through this kafin kika haifeni nima dan Allah kiyi hak’uri for all that I’ve done to you, forgive me please mother.”



 *© MIEMIEBEE*

 beeenovels.blogspot.co.ke

7 comments:

Abusuhaylarh said...

tnx youuuuuuuu again

fatima said...

Uwa uwa ce

fatima said...

Uwa uwa ce

Unknown said...

Awwwwn 😩😻😻😻 tnx alt sisterrrrrrrr Allah ya qara basira

Unknown said...

Awwwwn.....thanks sweetheart u r such a darlin'...

Unknown said...

Gaskiya kam uwa uwa ce Allah yasa kawai iyayen mu da alkhairi thanks miemie

Unknown said...

Mr fauzi yaga haza. Allah ya kara basira