TANA TARE DA NI... PAGE 92
BY MIEMIEBEE
Tunaninsa yaji ya katse kwatsam! sam yakasa yarda da abinda Flowersa ke ce masa, cikin sauti me rawa yayi maganar “Flower what did you just say?” Sake nanata abinda ta fad’i tayi.
“Subhanallah! Flower are you sure?” Yayi maganar tare da karb’e picture’n yana sake kalla. “Kina nufin dukansu nan basuwa nan yanzu?”
“Yes Habeebi” ta yi maganar tana gyad’a kai.
“Allah sarki... They are in a better place in shaa Allah.”
“Toh Habeebi Ummmi fah?”
“Meh had’i na da ita? Infact ni banma yarda ba who knows ko duk k’arya take tanason in tausaya mata ne tayi coming up da plan d’innan.”
”Haba! My Lion don’t be like that, taya zakace haka wa mahaifiyarka? Inhar k’arya kake tsammanin tamana uniform na cleaners dake jikinta kad’ai sheda ce, Habeebi mahaifiyarka cefah feel sympathy towards her atleast yara uku fa ta rasa one, two, three” ta irga da hannunta.
“Toh Flower laifi na ne? Nine na siyar mata da yara? Kwad’ayinta ya kaita kinga erin disadvantage da nake fad’a miki ai yanzu itace silan mutuwan yaran nan, mschw! What a pity.”
“I know Habeebi bara mu iya canja komai ba abinda ya faru ya riga ya faru please ka taimaka wa Ummimi.”
“In taimaka in mata meh?”
“Mutafi da ita hotel da muke.” D’an dariyan rainin wayo ya saki “intafi da ita? LOL lallai kam Flower you are such a wonder ni magananta ma ya isheni kimiyar mata da photo d’in ki taho mutafi.” Haka Fannah ta riga lalashinsa tana basa hak’uri da k’yar d’in k’yar ya yarda Ummimi ta bisu amman ba’a cikin motarsa ba hakan kuwa akayi.
Bayan taje ta taho da Ummimi ta tsare mata cap (taxi) kafin Ummimi tashiga taje gun Anas dan masa godiya, yana zaune cikin mota yana jiran Fannah.
“Assalamu Alaikum Anas nagode da taimakon dakamin, Allah saka da alheri ya kuma maka albarka.” Tayi maganan tana tsaye ta bakin windon side na Anas. Ko kallonta beyi ba se latsa wayansa yake chan yace, “thank her not me bani na taimaka miki ba excuse me please” Shiru tayi bata kuma cewa komai ba takoma taje ta shiga cap d’in hawaye na bin k’uncinta har suka isa hotel d’in kuka bata bar kukan ba.
Bayan isansu Fannah ta kalli Anas sannan cikin salon da inta mai magana yakeji tace, “My Lion nace zakayi wa Ummimi booking room koh?” Tayi maganan tana murza hannunsa a hankali.
“Flower kinga ba haka mukayi dake ba cewa kikayi zata biyomu nan bakice zan mata booking room ba saboda haka figure out me zakiyi da ita” yana kaiwa nan yafito daga motar ya wuce ciki. Binsa da kallo tayi “Habeebi yau ko kafi babarka k’ok’ari seka mata booking room d’innan” ta fice daga motar ta sallami taxi driver’n. “Ummimi muje reception ki zauna achan kafin amiki booking room.”
“Nagode ‘yata Allah miki albarka.”
“Ameen Ummimi” anan tajata zuwa reception daidai zata juya Ummimi ta riqo hannunta “Fannah karki b’oye min Anas yace bare kama min d’aki bakoh?”
“A’a Ummimi ya kike magana haka-” katseta Ummimi tayi “please karki min k’arya” zama Fannah tayi a gefenta hannunta riqe cikin na Ummimi. “Inason kisa a ranki Anas ze yafe miki saboda mahaifiyar sa ce ke kinji?” Kai Ummimi ta gyad’a mata “good kuma please kukan ya isa haka zan masa magana ina zuwa” ahaka suka rabu.
****
Miqe Anas ke akan gado da newspaper a hannunsa yana karantawa yana jin k’aran bud’e k’ofa ya ajiye yasoma baccin k’arya agefensa ta zauna “My Lion nasan ba bacci kake ba.” Shiru yayi be tanka taba.
“Habeebi katashi please kaji?” Ta hau jijjiqa sa badan yanaso ba ya bud’e ido. “Meh?”
“Habeebi Ummimi mana kamata booking room.”
“Banida kud’i.”
“Youngest billonaire d’in? Habeebi please ka tashi” nan ta miqe ta hau jansa daga gadon sam takasa murmushi ya saki sannan yajata ta fad’a jikinsa. K’ara ta saki sosai sanadin cikinta data buga. “Arghhh! Habeebi ciki na.”
“Sorry Mom Hanan” ya zaunar da ita kan cinyansa. Kukan k’arya ta soma tana riqe cikinta.
“Flower nayi hitting naki sosai ne?” Kai ta gyad’a tana murzq idanunta. “Am sorry kinji? Muje asibiti?”
“A’a nikayi booking wa Ummimi d’aki.”
“Flower barinyi ba.” Rushewa takumayi da kuka, “Flower wai bara kibar kukan nan ba?” Ta gyad’a kai ba yadda beyi tayi shiru ba amman taqi daga k’arshe seda ya yarda da k’udirinta. “Okay, okay naji zan mata for Hanan’s sake.”
Koma meh tace a zuciyarta tare da share hawayen k’aryan nata. Tana ganinsa ya fice ta saki murmushi.
Nan da nan ya sauqa yaje yama Ummimi booking d’aki a chan last floor ta yadda bare ma na kallonta ba bale yana jin baqin ciki. Tana zaune a reception d’in Anas yazo ya wuceta batareda yace mata ko k’ala ba bayan daya gama komai ya nufo inda take tare da ajiye mata key d’in a kujerar dake gefenta “room 116” kad’ai yace da ita. Hannunsa ta riqo kafin ya kub’uce mata. “Anas nagode Allah saka maka da alkhairi.” Hannunsa ya fisge ba tare da yace da ita komai ba.
“Anas dan Allah kayi hak’uri kamin magana barin iya jure fushinka ba please talk to me your mother” ba tare da yace da ita komai ba ya haye sama d’akinsu da Fannah.
*****
Haka nan tun daga ranan Ummimi tasoma zama dasu Fannah ko kad’an Anas baya shiga harkarta magana ma ba mata yake ba, koda ta mai magana baya amsata ba yadda Fannah batayi dashi ba amman yak’i yafewa Ummimi, a dalilin haka tasoma tashi Sallan dare tana roqan Allah. Cikin d’an k’ank’anin lokaci Fannah suka shaqu da Ummimi dan yadda Fannah kebata kulawa tamkar uwarta abinci kullum ita ke kai mata dan kuwa tsoron placing order ma take, haka Fannah tasa Anas agaba seda ya siya wa Ummimi kayan sawa da sauran abubuwan da zata buk’ata. Dukda shariyan da Anas ke mata hakan be hanata yimasa magana anytime she gets the chance to ba fatanta Allah sa Anas ya bata daman da take nema. Sunyi zaman two weeks tare Anas ya fara zancen komawa gida, Nigeria badan komai ba dan ya rabu da Ummimi.
_4:30PM_
Yana cikin harhad’a musu kayaki kasancewar gobe zasu tafi Fannah ta shigo d’akin bayan fitowarta daga d’akin Ummimi, akan gado ta zauna “sannu da aiki Habeebi.”
“Yauwa Flower.”
“Uhm nace in zamu koma Ummimi zata bimu ba?” Barin abinda yake yayi “waze bi wa?!” Yayi maganar cike da rashin yarda.
“Ummimi zata bi FAHNAS nace.”
“Humm!” yaja numfashi “sede in wani FAHNAS d’in kam ba wanda nasani ba.”
“Toh My Lion ita kad’ai zamu bari anan ne?”
“Dama dawa muka sameta? Ita kad’an ta muka sameta haka kuma zamu barta”
“Haba! My Lion katuna fa batada family yanzu we are her only family.”
“Flower I’m not her family kuma ba inda zanje da ita ta sake messing min family like she did before.”
“But Hab-”
“Period!” Ya katse ta. Bata sake ce masa komai ba gudun kar suyi fad’a. Chan bayan sallan isha bayan sun k’are chin abinci ta matso ta zauna kusa dashi akan gado tare da riqo hannunsa cikin nata.
“Habeebi please badan niba dan Allah kar kabar Ummimi anan baka tunanin in rananda step father’nka ya ganta ze siyar da ita kamar yadda ya siyar da su Barrah? Baka tunanin barinta anan had’ari ne Habeebi? I’m not asking you to forgive her all am asking is mutafi da ita kar mu barta anan please Habeebi don’t say no please.” Shiru yayi harga Allah bai tunanin ze iya ce ma Flowersa no this time akan abinda yasan ba gagaransa zeyi ba sede yanzu in yabar Ummimi tabisu dole gida ze kaita abinda bayyaso kenan yafison kamar yadda suka saba ba ita su cigaba da kasancewa ahakan shi bama wannan ba mezece wa Amal da batasan tanada wata mahaifiya ba bayan Ummie? Abinda ke damunsa kenan.
“Habeebi please kayi hak’uri mutafi da ita kaji?” Kai zallah ya gyad’a mata yana me nazarin aina ze kai Ummimi bayan isansu Nigeria. “Thank you so much My Lion” tayi pecking nasa tare da miqewa. “Ina kuma zakije Flower?”
“Zanje ince ma Ummimi ta shirya kayanta zamu tafi gobe.”
“Flower shine baraki iya kiranta a waya ba? Ni banason kina unnecessary zirga-zirga kinde sani bakida lafiya kuma munada tafiya gobe.”
“Don’t worry Habeebi I won’t take long” tayi mai blowing kiss, murmushi ya mata sannan ta fice.
Zaune ta tarar da Ummimi kan gado as always ta had’a tagumi bayan tayi sallama ta shigo tazauna a gefenta. “Ummimi ki shirya kayanki zamu tafi gobe.” Cike da rashin fahimta ta d’ago kai tana kallonta “ina zamuje Fannah?”
“Nigeria! Zakije kiga su Amal!” ta sanar da ita cike da jin dad’i.
“Nigeria?! Kina nufin Anas ya yarda zan biku?
“Ai na fad’a miki Anas na sonki he is just taking time to adjust nan bada jimawa zakuyi sorting out komai.”
“Allah sa Fannah nagode kuma sosai Allah biyaki.”
“Ameen Ummimi ba komai tashi mu shirya miki kayan naki.”
“A’a please karki damu kayan nawa dududu nawa ne? Keda bakida lafiya ma kije ki huta dan Allah kar gajiyan ya miki yawa.”
“Tunda haka kikace fine kiyi ki shirya ki huta kema Allah kaimu gobe.”
“Ameen nagode kima Anas godiya please nasan koda mutuwa zanyi ina mai magana ba amsani zeyi ba.”
“Bakomai Ummimi zan masa in shaa Allah seda safe” ta rufo mata k’ofar.
****
Bayan Anas ya kashe musu wuta suna kwance kamar yadda suka saba Fannah ta kira sunansa, “Habeebi.”
“Yes Flower.”
“Thank you so much for everything.” Ta fad’a tare da sake shigewa jikinsa.
“You don’t have to thank me Flower, ma godiyan me kike?”
“Aika fini sani d’azu Mami takirani tace in maka godiya mekayi musu, nayi nayi da ita ta fad’amin tak’i.”
“Haha!” yayi dariya kad’an “hakane?”
“Eh mekayi musu?”
“Babu.”
“Kamar ya babu Habeebi duk alkhairun da kake musu da a baya Mami bata tab’a cemin na maka godiya kamar na yau ba meh ka musu please?”
“Nace miki babu lets sleep tomorrow is a big day.”
“O’o ni seka fad’amin wani alkhairi kamusu.”
“Nace miki babu please kiyi bacci ko Hanan ma zata samu tayi, goodnight” yayi pecking kanta. Shiru tayi chan ta kira sunansa “Habeebi.”
“Yes Flower lets sleep.”
“Thank you kaji? Allah k’ara bud’i.” Magana yake cike da gyangyad’i “Flower nace miki banason godiyan nan.”
“Bakasan akan mefa nake maka godiyan ba.” Ya nisanta “akan meh?”
“Ummimi ce tace na maka godiya.” Shiru yayi bece komai ba. “Kaji My Lion?” Nan ma shiru data d’ago kai ta kallesa setaga idanunsa a rufe she is sure ba bacci yake ba, bayason maganan Ummimi ne. “Liar nasan ba bacci kake ba kadeji Ummimi tace ta gode” nanma bece komai ba murmushi ta saki tare da jan hancinsa. “Awwch!” Ya sakar da k’ara “kinsan da zafi koh?”
“Aww! kana jina kamin shiru kenan.”
“Sa’an ki d’aya Baby Hanan if not da na rama.” Gwalo ta saki masa sannan yajata jikinsa suka kwanta***
_washegari..._
As early as possible suka shirya luggages nasu duk na acikin mota Anas yabari asa akwatin Ummimi a motansu yak’i taxi aka tsare mata ta shiga ciki, kusan a tare suka isa airport akayi musu ciki da akwatinansu. A sama su Fannah suke a yayinda Ummimi ke k’asa ita kad’ai ba yadda Fannah batai da Anas yabar Ummimi ta samesu ba yak’i.
_2 hours later..._
Miqe Anas yake kan wani medium sized bed se baccinsa yake sha ayayinda Fannah ke zaune a d’ayan side d’in da Qur’ani a hannunta se karatu take tayi daidai takai inda k’arfinta ya k’are ta tsaya tare da miqewa ta sauk’a k’asa gun Ummimi as always ta sameta ta ta had’a tagumi bayan ta zauna a gefenta ta dafe kafad’arta se anan Ummimi tasan da shigowarta. “Fannah” takira sunanta a bit suprised.
“Na’am Ummimi kin zauna shiru ko TV ne ki kunna mana.”
“A’a barshi karki damu, ya Anas yake?”
“Yana bacci kema ya kamata ki kwanta.”
“A’a nikam, se hankali a kwance ake iya bacci ai.” D’an murmushi Fannah ta sakar mata “toh ga Qur’ani ki karanta” ta miqa mata. “Nagode kema kije ki huta wannan hawa da sauqan ze dameki kinga already k’afafuki sun kumbura.”
“Toh Ummimi.”
“Nace yaushe ne jikan nawan ze fito?” D’an dariya ta saki dan kunya ma takasa fad’a mata. “Surikar tawa tana jin kunya na ne?” Ummimi tayi teasing nata.
“Nanda wata uku in shaa Allah.”
“Ahh ashe ma kin kusa toh Allah raba lafiya ‘yata Allah ya sauk’eki lafiya.”
“Ameen Ummimi nagode barinje in huta nima.”
“Yawwa ‘yata” ahaka suka rabu beside Anas taje ta kwanta alokacin har ya tashi. “Flower ina kikaje?”
“Gun Ummimi.”
“Baraki koyi zama gu d’aya ba ko kinga k’afafunki kuwa? Wai bakiya jin tausayin kanki ne?”
“Habeebi please ya isa ai dama kumburin dole ne kaide kace kanason min surutu ne saboda gun Ummimi naje inda toilet nace na shiga ai barakayi magana ba.”
“Ohkayyyy haka kika ce? Toh har mu isa banason kisake sauk’a wajenta am not asking you am ordering you as your husband.”
“Sekayi ai” tayi maganar k’asa k’asa.
“Kuma najiki nide na fad’a miki.” Baya ta juya masa ba tare da tace komai ba haka tundaga nan bata sake masa magana ba kodaya tasheta Sallan Azahar haka La’asr ma shima be mata magana ba.
10 hours ya d’aukesu sannan suka iso Nigeria inda suka sauk’a a Sandralia Hotel Abuja har anan Fannah bata sake ma Anas magana ba, ruwa ta watsa taso shiga duban Ummimi amman Anas ya hanata. Bayan ta shirya cikin kayan baccinta ta zauna kan gado tana ma kanta tausa a k’afafunta, fitowan Anas daga wanka kenan singlet da nickers yasa ya hauro gadon yana k’are mata kallo.
“Flower.” Shiru tayi bata tanka sa ba. Kusa da ita ya matso “Flower bara kimin magana ba?” Nanma shiru se massaging kumburarrun k’afafunta take hannunta ya d’aga daga kan k’afan nata nanma bata ce masa ko k’ala ba. “Flower wai barakimin magana?” Nanma shiru. “Okay I’m sorry kinji? I’m sorry.”
“Kasakemin hannu as you can see am massaging my legs.”
“Flower I said I’m sorry.”
“Naji sakeni toh.”
“Bari zan miki.”
“Banaso zanyi abuna da kaina.”
“I’m sorry” ya sake hannun nata tare da kama kunnuwansa ko kallonsa batayi ba ta cigaba da massaging k’afanta. “Flower please.”
“Wai hak’urin me kake bani? Nace kamin laifi ne?”
“Baki fad’a ba amman nasan na miki laifi and I’m sorry kije kisameta in kinaso.”
“Banaso” ta fad’a stubbornly.
“Yi hak’uri mana Mom Hanan” ya sake matsowa kusa da ita closing the gab between them, gashin kanta data barbaza a kafad’anta yahau shafawa. “Yi hak’uri kinji barin sake ba.” Kallonta ta miyar garesa “I’m sorry sweetheart” d’an murmushi ta sakar masa ma’anan ta huce. “Thats my woman!” Lips nata yasoma laluba bata hanasa ba se dab da bakinsu ya kusa had’iye tasa hannu ta kama mai baki “no kisses today thats your punishment” tayi maganar tare da miqewa daga kan gadon ta sanya hijabinta.
“Oh common please Flower ko peck ne.”
“Nace NO! Gobe zaka sake repeating abinda kayi yau.” Tana kaiwa nan ta fice zuwa d’akin Ummimi.
Some minutes later ta dawo har anan Anas beyi bacci ba yana jiranta, a nitse ta cire hijabin ta haye gado ta kwanta ganin bata matso kusa dashi ba yasa ya matso dakansa tare da zama. K’afanta ya miqar kan cinyansa sannan ya fara mata massaging.
“Ta nan ka b’ullo kenan? Saboda in ka gama in baka kiss as token of appreciation, uh-uh yau ba kiss na fad’a maka smart guy, wannan logic nakan bareyi aiki ba yau.” Dariya yaso yi dankuwa ta kamasa amman seya matse.
“Ni ba haka nace miki ba am massaging your legs because I love to”
“Humm! Allah sa de, nagode” bayan daya gama yaja d’ayan ma yamata godiya ta masa sannan ya kashe musu wutan ya koma ya kwanta agefenta yana wasa da gashin kanta duk wani salo nashi yayi applying amman Fannah tak’i bari yayi kissing nata haka yatayi har ya gaji seda tajishi yayi shiru sannan ta juyo tana kallon shi unexpectedly tayi pecking nasa a lips. Kafin ta d’ago kanta ya riqeta gagam yasoma sarrafata haka sukata romancing junansu har seda bacci b’arawo yayi gaba dasu.
*© MIEMIEBEE*
beeenovels.blogspot.co.ke
4 comments:
Tanks sis
tnx youuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuu
Weldon dear
shukran
Post a Comment