Saturday, 3 September 2016

TANA TARS DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 32
BY MIEMIEBEE



Bece da ita komai ba yabiya masu kud’in abincin, ahaka suka dawo cikin motar suka koma office, a lokacin azahar yayi. “Sir excuse me zanje inyi sallah.” Ba tare da ya kalle taba yace, “you have 5 minutes to do so, in kuma kika tsaya hira da Yusuf kikayi delaying d’ina you’ll answer to me.” Kai ta giad’a a hankali ta ajiye jakarta ta fice bayan ta idda sallah suka had’u da Yusuf hira yakeson janta dashi amman sauri take kar ta makara Mr. Fauzi ya samu abin magana kai. “Yusuf kayi hak’uri please, minti biyar Mr. Fauzi yabani ko second na k’ara ze ci mutunci na kabari in aka tashi zanzo musha labari har se sanda ka gaji.”
    “Toh Allah taimaka aiki as PA wa Mr. Fauzi kam seda hak’uri.” yace da ita yana tausaya mata, a haka ta koma office nasa,yana zaune kan kujera yayi focussing kan laptop dayake aiki akai kafin ta zauna yace taje ta had’a masa coffee bayan ta had’a tazo ta ajiye masa. “Kinga flasks biyu da suke can?” Ya nuna da yatsa. “Eh nagani” ta amsa a hankali.
   “Good ki cika min su da coffee.” Ido ta bud’e tana kallon ikon Allah yanzu dan tsiya har flask biyu? Ya kai ina?

   “Bakiji bane?”
   “Naji” ta amsa a takaice. “Good off you go.” Bayan ta isa wajen ta juyo tana kallonsa, shan coffeensa yake hankali kwance yana duban laptop tare da yin wasu ‘yan rubuce rubuce time to time “Sir ba d’an wani babban roba ko kwanon da zan had’a ciki se injuye cikin flasks d’in tunda dayawa zan had’a coffeen?” Ta tambayesa a nitse.
    “Babu kuma koda akoi ma ba barin ki zanyi kiyi amfani dashi ba ga cups nan kina had’awa ciki kina juye har ki cika.” Wannan wace erin mugunta ne kwata kwata cup d’in fa k’ananu ne erin teacups d’innan yaushe har zata cika wannan manyan flasks.
    “Sir hakan ze d’au lokaci ba gara naje kitchen na ari bowl ba.”
    “Bara kiyi ba, kinga banasan musu na fad’a miki stop breaking my rules in zaki had’a good in barakiyi ba kuma in kira Mami in sanar da ita kina min rashin kunya.”
   Chan k’asa k’asa tace, “ba se kanada lambarta ba.” Murmushi kad’an yayi, “haka kikace?” Wayarsa ya d’aga ya kai kan contact na Mami da yayi saving just d’azu data ajiye jakarta zuwa yin sallah. “Zo kiga” bayan ta k’ariso taga eh fah lambar Maminta ne to ya akayi ya samu? Ba tare da tace masa komi ba ta koma ta fara had’a coffeen cikin teacup d’in tana juyewa cikin babban flask d’in. Tayi hakan kusan sau goma amman data gwada jijjiga flask d’in taji har yanzu da saura cikansa ko rabi, gashi ko soma cika d’ayan ma batai ba haka kamar tayi kuka ta samu ta cike d’ayan da k’yar ta zauna dan ta huta.

      “Kin gama ne?” Ya tambayeta
   Kamar wacce bara tayi magana ba tace, “da saura d’ayan.”
   “Well? Me kike jira toh?”
   “Sir hannu na yagaji barin d’an huta please.”
    “Hutu?” Ya tambayeta yana murmushi. “Kin tab’a ganin inda aka huta a office? Get up ki cigaba we have thousand of things to attend to.” Haka kamar ta kashe kanta ta tashi ta soma cika d’ayan har tsayawa take tana mik’a hannunta Anas kuwa ganin haka dad’i yake masa nan gaba zata sake barin masa aiki ba tare da ta sanar dashi ba seya biya duka coffeen dayayi missing time da ta tafi. Tana gamawa ta koma zata zauna, kafin ta zaunan ya kirata fuskarta ta yamutsa kan kashi sannan ta nufa table nasa.

         “Ina details dana rubuta a hannun ki d’azu?” Jakarta ta koma ta ciro wayarta takai kan inda tayi saving sannan ta tura masa gabansa “gashi.” Kallon wayar nata ya tsaya yi sekace bashi ya d’auka ya copy number ciki d’azu ba. “Wannan shi kike kira da waya?” ya tambayeta. Sosai tambayarsa ya bata mamaki haka kuma ya bata haushi taga de wayarta bara a zagesa ba, tecno ce D7 ba abinda bayayi, duk abinda iphone 6s nasa da samsung galaxy 6 edge nasa dayake tak’ama dashi taga nata ma yanayi kawai de d’an cracks ne wanda basu fi uku akai ba. Amsa daidansa ta basa “shine, kuma naga ga details da kake buk’ata a kai.”

    Biro da paper ya mik’a mata “ungo copy it down for me banasan wannan fashasshen screen nakin ya tsaga min hannu.” Kallonsa tayi tare da kad’a kai kamin ta amsa ta yi copying masa neatly bayan data gama ta mik’a masa d’aga wa yayi yana kallo ya d’au batada clear and neat handwriting ne da seya samu abin magana kai se yaga kamar tafi sa iya rubutu ma dan haka ya gwada yin shiru amman shegen neman maganansa bare barsa ba. “I don’t think wannan wayan kin zena recieving calls da emails me kyau yakamata asan nayi.”
  “Sir nifa waya na ba abinda ba yayi, kuma naga ta nan nake answering calls naka da.”
   “Da kikace, ada dakike as my coffee maker yanzu kuma you are my PA abin kunya ne ma in shiga dake cikin jama’a da wannan abin da kike kira da waya.”
      Kasa rik’e bak’ak’en maganganunsa tayi yanzu kam, abin nasa yayi yawa. “Excuse me Mr. Fauzi just because ina aiki k’ark’ashin ka be baka izinin looking down on me ba, I’m not ashamed ko ina zan shiga da waya na tunda ba wani ne yasaya min ba ni na saya da kud’i na.”

      “Wannan kuma ke ya dama na fad’a miki cikin rules naki banasan ina fad’an abu kina fad’a kema ba, I’m your Boss duk abinda na fada koda ba haka bane dolen ki  kiyarda in baki san me kalman respect ba kisani yau.” Telephone nakan table nasa ya ja tare da danna ‘yan lambobi akai “hello? Akoi iphone 6 gold ne a shop naku?”
    On the other side matar tace, “yes Sir akoi.”
  “Good akawo min guda d’aya yanzu the money will be delivered very soon.”
  “Okay Sir thank you.” Kallon sa Fannah ta tsaya yi iphone 6 ma waye? Inma wa ita ne toh ya kwantar da bokatin hankalinsa ba amsa zatayi ba, tecnon ta ya isheta.
    “Stop starring at me” yace da ita yana me cigaba da abinda yakeyi cikin laptop d’in. Bata ce masa komi ba takoma ta zauna shiru tana mamakin hali irin na Anas. Bayan kamar minti goma knock ya shigo daga k’ofar office nasan. “Get the door” yace da ita hankalinsa kan abinda yakeyi. A sanyaye ta mik’e ta bud’e mace tagani sanye da uniform da k'aramar shopping bag na tambarin AA communications a hannunta. Bayan ta gaishe da Fannah ta mik’a mata leather’n, amsa Fannah tayi ta kai wa Anas tare da ajiye masa kan table wani card ya ciro ya mik’a mata da nufin takai wa matar tana kai mata, ta amsa tayi godiya sannan ta fice, ciki Fannah ta dawo kafin ta zauna Anas ya kirata. A gaban table nasa ta tsaya a yayinda ya mik’o hannunsa da nufin ta ajiye masa abu kai. Itako bata gane me yakeso ba dan haka ta tambayesa “excuse me?”

      “Bani wayarki” ya fad’a a nitse. Zatayi magana ya tsawa ta mata “nace bani wayarki! Don’t let me repeat myself.” Tsabagen tsoro bata san sanda ta ajiye masa wayar a tafin hannu ba. Bayan wayar ya bud’e tare da ciro sim nata “Sir meh zaka min da sim card?” Ta tambayesa ko d’aga kansa beyi ya kalleta ba bale ya amsa ta, daman micro sim cikin wayar tatan, nan ya bud’e leather'n ya ciro sabuwar iphone 6 pil daga ciki ya sa sim d’in ciki wayarta kuwa ya jefa a dustbin kusa da shi.

      “Excuse me! Mr. Fauzi taya zaka jefar min da waya a dustbin da kud’i fa na saya in kai bakasan almubazaranci ba kyau ba toh ni nasani” wajen dustbin d’in ta nufa da nufin zaro wayarta karap ya d’aga ya kai d’ayn gefen. “Sir ka bani wayata.” Drawer’n dayake ajiye kad’an daga kud’ad’ensa ya bud’o tare da ciro bandir na naira d’ari ya ajiye kan table d’in “I’m sure wannan yayi kud’in wayarki. Take ita tare da sabon wayanki.” Bandir na d’arin ta d’aga “zanje in sake siyan sabon waya kalan nawa in chenji ya rage zan dawo maka dashi amman ni barin karb’i iphone naka ba bana buk’ata.”

     “Miss Aleeyu!” Ya kira sunanta a tsawace. “Kap building d’innan bame gaya min magana, bame crossing d’ina se ke. Ko a gida in nayi magana ba’a objecting d’ina saboda haka ki mayar da hankalin ki, I’m your Boss not your friend.” Yayi lecturing nata cikin tattausar murya. “Wannan yazama karo na farko nakuma k’arshe da zan miki magana ko in saki yin abu kimin musu. Ki d’au iphone d’in, I don’t care ko kin koma kin sake siyan kalan wancan abinda kike kira  waya dashi all I know is da wannan wayar zamuna business dake, now take it.”
    Shiru tayi chan ta mik’a hannu ta d’aga da kwalin duka. “Good” yace tare da mik’ewa “follow me.” Ba musu ta mara bayansa still a floor na saman yakaita zuwa wata office a saman aka rubuta *MISS ALEEYU* ajikin kuwa aka rubuta *PERSONAL ASSISTANT* bayan ya bud’e k’ofar ya shiga still tana biye dashi office ne babba me kyan gaske da table na katakon zamani da kuma kujerun office guda biyu, kan table d’in laptop ne seda telephone, dasu fax and printing machine da cup cike da pencils da biro da sauran office equipments irinsu stepler, pin, glue, dade sauransu. Gefe guda kujerar cushion ne 3 seater dogo me kuma fad’in da za’a iya kwanciya akai se ‘yar k’aramar fridge dakuma dispenser se kuma split AC dakuma toilet a ciki. Sosai office d’in ya had’u ya kuma yima Fannah kyau dan se kallace-kallace take kamar zata karya wuyar ta.

     “Kallon ya isa haka ba sekin karya wuyarki ba” yace da ita cike da kunya ta daidaita kallonta gu d’aya. “Kin iya karatu ba sena fad’a miki ba, nan office naki ne as my personal assistant kamar yadda kika karanta rubuce a bakin k’ofar. Duk wani abinda zaki buk’ata akoi anan, ba kuma na baki office bane dan kisamu wajen yin bacci da hira da saurayin ki aiki ne yakwo ki nan, wancan telephone should stay on always, karki kuskura koda wasa kiyi disconnecting daga jikin plug na bangon saboda dashi zan na miki magana as well as other staffs, clear?”

    Kai ta giad’a “yes.”
    “Good saboda haka yanzu ba ruwanki da office d’ina fashe ni na kiraki, nima zan huta da kallo, for now ki biyo ni akwai aikin da zan baki ki fara dan nasan na barki anan ba abinda zaki amfana se bacci.” Ita tama soma sabuwa da bak’ak’en kalamunsa. Jakarta ta ajiye ta juya tabi bayansa bayan sun isa office nasa ya zauna ya d’ago blue eyes nasa yana kallonta “ina jotter’n ki?”
   “Yana d’ayan office d’in” ta amsa sa a takaice.
    “Okay office d’inne zena d’auka miki record d’in kokuma so kike kicemin ilimi yamiki yawa da duk abinda na fad’a miki zaki iya d’auka akai ba mistake.”
  Share abinda ya fad’a mata tayi tace, “barin je in d’auko”
    “Make it quick” ya amsata yana duban rolex agogon hannunsa bayan minti d’ai Fannah tadawo rik’e da biro da jotter.
 
        Tun kafin ta bud’o biron ya soma bata aiki  “Kije file room acikin first cabinet akoi stack papers type A-D  kiyi printing sekimin e-mailing, bayan haka ina buk’atar neat handwritten version nasu, avoid any mistake. Sekije 5th floor ki karb’a wasu papers a wajen Miss Suleiman kiyi typing nasu a computer kimin e-mailing, take note kowani paper seprate document ne, bayan kin gama typing nasu print them out ki mayar filing cabinet kiyi arranging. You can go now.” Hannun Fannah har b’ari yake dan yadda take rubutun da sauri duk wannan uban bayani da numfashi d’aya Anas yayi dan mugunta, magana yake sauri sauri saboda tayi missing wani abu dan ta buk’ace sa ya koma baya seya samu ya zageta yanzu.

    A sanyaye ta juya ta fice file room 3rd floor ta nufa kamar yadda ya mata kwatance taga a rubuce a sama 1st cabinet papers d’in ta tsakuro sunyi kusan d’ari har yaushe zatayi typing nasu har tayi e-mailing sannan ta zauna ta k’ara rubuta su da hannu? ai aiki ne babba why not kawai in tayi typing tayi printing ai duk d’aya ne. Bayan ta tattara  papers d’in ta haura 5th floor ta amshi papers wajen Miss Suleiman ta haura sama inda office nata dana Mr. Fauzi suke. Office nasa ta soma wucewa dan masa bayani bayan tayi knocking yace, “come in” tana bud’e k’ofar yaga itane sarai yasan meya dawo da ita, so take ta nemi alfarman printing stack papers d’in ba seta rubuta su ba, da gangan dan mugunta daman ya buk’aci ta rubutan dan kawai yayi punishing nata.

    Bayan ta k’arisa gabansa ta daidaita muryarta ko ze d’an tausaya mata ya yarda da k’udurinta. “Sir naje na d’ibo stack papers d’in nace ko ze yuwu kawai nayi printing nasu bayan nayi typing d’in? Ma’ana ba sena rubuta ba.”
        “Miss Aleeyu nan office ne ba gidan hutu ba, yadda nace sekin rubuta sekin rubuta off you go.”
       “Sir but plea-” bata k’are maganar ba ya dakatar da ita “banasan musu just go nima in huta.” Daman tasan ba yarda zeyi ba juyawa tayi ta nufa office nata. Chan ta soma da typing stack papers d’in bayan tagama ta masa e-mailing duka sannan tayi printing papers data amso wajen Miss Suleiman ta sauk’a taje ta jerasu a filing cabinet sannan ta sake haurowa ta koma office nata batasan a wani shekara zata gama rubuta wannan uban papers da suka kai kusan d’ari ba.

      Guda 20 ta rubuta amman wani erin zogi hannun ta yake mata, kuka ne kawai batayi ba haka da k’yar tayi ta huta ta rubuta hamsin saura hamsin. Telephone dake kan table nata ne yasoma ruri tana kai dubanta taga CEO rubuce akai kamar barata d’aga ba kawai ta sa hannu tayi picking. “Yes Sir” tace masa.
    “Kin gama?” ya tambayeta
    “A’a Sir da saura papers d’in fa har d’ari ne.”
   “Good kicigaba da yi in kin gama seki kawo min akoi aiken da zakije min.”
   Kamar wacce zatayi kuka tace, “Sir please kabar aiken gobe wallahi nagaji please.”
    Murmushi yayi cike da mugunta “kin gaji? Ai bakiyi komi ba tukun hurry up nan da one hour ki tabbata kin gama.” Ding! Ya katse. Tsuka taja “mugu kawai.”

    © miemiebee

No comments:

Post a Comment