Saturday, 3 September 2016

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 21
BY MIEMIEBEE


Yusuf nada mutunci sosai cikin d’an k’ank’anin lokaci suka saba da juna, dake yanada surutu sekuma gashi shekarunsu d’aya, ma’aikaci ne shima a company’n. Har kitchen d’in ya kaita yajira bayan ta gama had’awa ta bashi ya amshi yakai wa Anas sannan ya dawo dan rakata har waje. wajen wata elevator suka nufa wanda is different from na d’azu dan haka ta tambayesa ko ina zasu. Murmushi yamata sannan yace, “sauk’a zamui zuwa first floor saboda in fita dake kar ki b’ata a wannan babban gini.”
     Murmushin ta maida masa “amman naga ba tanan muka hawo da Mr. Fauzi ba.”
    “Hakane, ta private elevator’nsa kuka hauro wannan kuma da zamu shiga shine na public, wancan nasa ne shi kad’ai ke shiga you are lucky ma kinsamu kin shiga wancan.” Ya mata bayani. ‘yar murnushi tayi tabi bayansa har waje ya rakota ya tsara mata napep sannan ya koma ciki. Daga can kasuwa ta wuce ta musu siyayyan abinci sosai tunda sun samu kyauta.

      Isarta gida keda wuya ta tarar da ‘yan sanda tsaye daga gani ita suke jira fuskar su Mami duk ya jik’e da hawaye. “Yawwa ga ta nan” cewar wata nurse.
    “Ku tsaya please.” Fannah tace da polisawan.
    “Dalili?” Cewar nurse d’in.
      “Ga kud’in kunan nasamu dan Allah” nan ta irga dubu goma ta bata sannan suka fice. Godiya Mami tayi wa Allah da gudu ta ruga tayi hugging Fannah.
     “Fannah dan Allah kiyi hak’uri ban tab’a san d’aya daga cikin abubuwan da suke faruwa dake su kasance haka ba dan Allah kiyi hak’uri.”
     “Haba! Mami wace erin magana kike inda kunji good news danake tattare dashi ma da duk kunbar kukan nan. Ga nan siyayya na mana nasamu aiki!!”

       Atare duk sukace “dan Allah???” “Alhamdulillah.” cewar Afrah.
    “Aina?” Mami ta tambaya.
    “A Flames Enterprises wallahi Mr Fauzi ya d’aukeni aiki wai zanna had’asa masa coffee...” nande ta musu bayanin komai. Sosai Mami sunji dad’i musamman ma dasukaji albashinta dakuma kyautan da ya mata. Nasiha sosai Mami tama Fannah dukda cewar tasan Fannah da hankali. Albarka tata sawa Anas data ta tsine masa da a baya.

   ***
     Tun k’arfe  4:40PM Fannah ke rik’e da wayarta gudun karta k’ara ko minti d’aya kan lokacin da Anas ya bata. 4:50PM na yi ta kirasa yana kwance kan gado alokacin call d’in yashiga yana gani yagane ita ne beyi picking ba instead seya katse nan yayi saving number’nta da *COFFEE MAKER* cike da mamaki ta sake kira mesa ze katse bayan shi yace ta kirasa  be d’aga ba sansa ya kusan tsinkewa. Cike da tsiwa yace “ke baki gane kan aiki ne? Kinga nayi declining call meaning na gane kece kenan haba!.”
  “I’m so-” bata k’are maganar ba ya katse wayar. Miyau Fannah ta had’e ita kam Allah bata ikon jure wulak’anci da masifan Anas.

     _Washegari..._
    Da safe da misalin k’arfe 7:40AM Fannah da Aiman da Afrah suna kwance kan katifarsu se bacci suke rafkawa an samu an k’oshi jiya wayar Fannah yasoma ringing firgit ta farka dake wayar na k’ark’ashin pillownta a gigice ta d’aga ganin sunan daya bayyana kan screen d’in ya wassakar mata da bacci. *MR. FAUZI* giara muryanta tayi sannan ta d’aga.
    “Assal-” be jira ta k’are sallaman ba ya katse ta “be here in my office at 8:00AM. Don’t be late” kafin tace “okay” ya katse wayarsa. Ita ba ma wannan ba duban agogonta tayi taga 7:42PM
“YA SALAM!!” ta d’anyi ihu “yaushe zanyi wanka in karya in tsari napep in isa har NEW GRA cikin minti 18 wayyo Allah help me.”

     Ko tafasa ruwan zafin wankanta batai ba da ruwan sanyi tayi wankan anayi ana ihu har ta k’are tafito ko shafa mai batai ba, da k’yar da fad’a da kokuwa tasamu ta kama gashinta hakan ma be kamu ba sakwa-sakwa kawai de aje ne. Tea da biredi ta karya da, ba Butter bale Jam haka gayansa taci ta saka wata maroon material lace da farin hijabi nan da nan ta d’au wayarta tajefa cikin jakarta da d'ari biyar ta fice. Duban agogonta tayi taga 7:53AM ji take kamar ta fire kafin ta sami keke napep har da 55 yayi. A takaice de se 8:20PM ta isa New GRA. Lattin minti ishirin tayi, imagining kalan masifan dazata sha gun Anas kawai take dan sanda ya fad’a mata baya tolerating late coming.

     Da Yusuf ta fara yin karo shiganta ciki ko gaisuwan arziki bata tsaya sunyi ba ta shige elevator se sauri take yayi ya ruhu, yana ruhuwa kuwa yafara tafiya sama ji take kamar ta fire sama bayan ya bud’u tafita da sauri gudu tayi ta k’arisa bakin k’ofar ta bud’e a hankali ta shiga tsaye ta gansa bayansa na fuakantarta sanye yake dawata pitch long sleeve shirt wanda yad’anyi rolling sleeves d’in zuwa k’ark’ashin elbow nasa. Waya ne rik’e a kunnesa se faman masifa yakeyi fitsari Fannah tasoma ji take tun kafin a fara mata nata bayan ya k’are wayar ya buga wayan kan table d’in tare da jan tsuka.

    B’ari take tayi “zaki k’ariso nan ne kokuma senayi firing naki!” Ya daka mata wata erin tsawacaccen tsawan da be tab’a mata ba. Tuni hawaye suka ciko idanunta tafiya take k’afafunta suna rawa har ta k’ariso gabansa kanta a k’asa ko fuskarsa bata kalli ba. “Mr. Fauzi dan Allah kayi hak’uri wallahi unguwar danike da nisa daga nan kafin insamu abin hawa har in zo nan-”
   Katse yayi dawata tsawam sede bekai na d’azu ba “shut up! I don’t care. Koda a wani planet kike bandamu ba in na kiraki you have to be here at the exact time kina jina!?”
      Hawaye na gangarowa kan kumatunta ta giad’a kai “I’m sorry.”
    “Wuce ki had’a min coffee make it quick” ya fad’i yana k’ok’arin zama. Kallonta yake sanda takai bakin k’ofa sannan ya tsaida ta. “Ina kuma zakije?”
   
     Hannu tasa ta share hawayenta “kitchen.”
      “Okay, wannan kuma fa? Na kwalya ne shi?” Juyowa tayi ta dawo cikin office d’in tana kallon direction dayake nunawa da yatsansa, coffee machine tagani.
     “Ban gani bane” tace a hankali.
      “Banasan surutu get on with it duk abinda kike nema akoi cikin fridge d’incan.” Kai ta giad’a seta tuna da halin sa tace, “toh.” A sanyaye ta k’arisa wajen fridge d’in ta bud’e, kwalb’an giyan data gani ba adadi ne ya mugun razanar da ita. Hannu tasa bibbiyu ta rufe bakinta dan hana ihun dake k’ok’arin fito mata. A razane ta juya tana kallonsa shima kallon nata yake.
   
     “Lafiya? Gawa ko jini kika gani ciki?”
    Kasa fad’in komi tayi har yanzu takasa believing abinda tagani. “Ke! Tambaya nake miki.” Kasa amsa sa tayi nanma sanda ya tashi ya nufo wajen, fisgan murfin fridge d’in yayi ya duba cikin. Nanne yagano giyan data gani ciki ne ya razana ta. Kallo ya watsa mata “acikin rules dana fad’a miki sanda na ce miki banasan shisshigi abinda ya kawo ki kawai zakiyi so get on with it.” Yana kaiwa nan ya koma ya zauna. Da k’yar Fannah ta dawo da hankalinta gu d’aya taciro abubuwan da zata had’a masa coffeen da, tare da rufo fridge d’in duk hankalinta bai jikinta bata ma san me take had’awa ba haka ta kwarara sugar ciki tagama takai masa se mamaki take. Yanzu na miji kyakkyawa kamar Anas amman ya b’ata rayuwarsa da shaye shaye? Meyake nema a duniya? Ga kyau ga kud’i mena shaye shaye? Meyake nema? Me yasa yake shaye shaye?

      Anas na kai coffeen bakinsa ya sake maidashi cikin cup d’in dan uban sugar ga coffeen datasa ciki yayi yawa. K’aran da glass cup d’in yayi sakamakon fashewan da yayi k’asa ya dawo da Fannah daga duniyar tunanin data fad’a a firgice ta mik’e daga kan kujerar data ke zaune tana b’ari, hannunta biyu dafe kan bakinta se raba ido take.
     “Meh wannan kika had’a min? So kike diabetes yakamani da zaki d’ura min wannan sugar a coffee?”
     “Sir dan Allah kayi hak’uri my mind was carried away, zan sake had’a maka kayi hak’uri.” ta fad’a tana b’ari.

      “Fannah Aleeyu in kinsan you are not ready for this job ki tattara kanki kibar min office, NOW!” Ya daka mata tsawa. Hawaye ta soma yi take.
    “Mr Anas I’m so sorry dan Allah kayi hak’uri zan sake had’a maka wani” da sauri taje ta tsuguna ta soma tattara broken glasses d’in acikin yin haka d’ayan ya yanke ta sosai a yatsar ta.
     “Arghhhhhh!!!” Ta saki k’ara a firgice Anas ya taso tare da kama ta da hannunta daga sama da k’arfi sosai ya mik’ar da ita. K’ara ta sake saki se hawaye take ganin yadda jinin jikinta ke d’iga sosai a k’asa. “Bakida hankali ne?” Ya daka mata tsawa.
    “Kin tab’a ganin ana tattara broken glasses da hannu? Mschww.” Hannunta ya ja da k’arfi ya kaita bathroom ba abinda Fannah keyi se kuka ita ko noticing na mijin daba muharraminta ya kama mata hannu ma batai ba dan azaba.

       Famfo ya bud’e yasa yatsan nata a k’ark’ashi ruwa na tab’awa ta sakar da ihu “arghhhhhh!!!” Kallonta yatsaya yi se hawaye take wanke mata yankan yayi sannan ya zaunar da ita kan toilet sit. Har yanzu se hawaye Fannah take bayan ya fice da ‘yan mintuna ya dawo da first aid box hannunsa bayan ya d’iga spirit jikin auduga ya gwada d’aga hannunta seta kankame se yanzu hankalinta ya dawo jikinta ta hanasa rik’e hannun nata dan haramun ne. Kallo ya bita dashi sannan yaja tsaki ya finciko hannun nata da k’arfi ya danna spirit d’in kai ihu ta sake saki “arghhhhh!!! Wayyo Allah zaafiii!!!” Be cire ba sanda ya tabbata spirit d’in yashiga sosai. Sannan ya ciro plaster ya b’are ya nannad’a mata a hannun.

      “Get up!” Yace da ita tana kuka tabi bayansa suka koma cikin office d’in coffeen ta wuce zata had’a masa sabo. “Meh kuma zaki yi can?”
    Murya na rawa tace, “zan sake had’a maka wani ne.”
     “Saboda ki sake yanke hannunki koh? A jinki nid’in ina san rik’e hannun ki ne? Mschww” Matsowa kusa da ita yayi ta matsa baya take “be telling me the procedure in had’a.” Haka tana fad’a masa abinda zeyi step by step har ya had’a sede ko daya tab’a nasan be masa dad’i kaman nata ba.
    Tsuka yaja. “Ba dad’i” ya fad’i a hankali.
    “Sorry sir me kace?”
   Tsawa ya daka mata “nace ba dad’i! Damn it!”
    “Sir! But yadda nake had’awa fa haka kayi.”
    Juyowa yayi ya galla mata kallo “so kike kiji mesa nawa be kai naki dad’i ba? Ehh? Saboda kin fini iya had’awa saboda your hands are special when it comes to making coffee. Dang it!” Ya buga hannunsa jikin bango wanda ya mugun firgita ta. Komawa yayi kan sofa ya zauna tare da sake necktie nasa. Numfashi ya saki “mik’o min bottle na giya d’aya cikin fridge d’in.”

     Ido Fannah ta zaro waro waro. Se salati take a zuci. “Bakiji me nace bane?” Ya fad'i a tsawace.
    K’arya tayi, “na’am banji ba.”
     “Nace ki mik’o min bottle d’aya na beer (giya).”
     “Wayyo Allah!” Fannah tace a zuci “yau za’a sha giya a gabana Ya Allah kace da wanda ya sayar da wanda ya raba da wanda yasha duk sunada zunubi. Wayyo ya zanyi?”
    “Don’t let me repeat myself!” ya fad’i a tsawace. Bata san sanda ta d’auko ta kai masa ba. Fisga yayi ya  bud’e tare da yin wulli da murfin daya kafa a bakinsa be cire ba sanda yashanye rabi. Take idanunsa suka soma juyawa wanda ya mugun firgita Fannah wai a ina tasan wannan idanu? Se yanzu ma take k’ara ji a jikinta sun tab’a had’uwa. B’ari take sosai.

     Bayan ‘yan mintuna ta kira sunan sa “Sir?” Shiru kukeji. “Sir?” Tasake kira “uhmmm” ya amsa a gigin bacci. Gabansa ta k’arisa tasa hannu tana waving a iska ko kad’an be motsa ido ba da alama bacci ya sacesa. Giyan hannunsan ta gwada karb’a ya damke a jikinsa da k’yar tasamu ta karb’e a hankali ta je ta juye a bayi tayi flushing data dawo kuwa ta samesa yana bacci a karkace, kansa yayi gefe guda har ta kai bakin k’ofa zata fita sekuma ta tuna yadda yamata treating ciwonta dukda yata mata tsawa, be kamata tabar sa haka ba shima tabbas inya cigaba da kwanciya haka ze tashi da ciwon wuya komawa tayi ciki dan giara masa kwanciyar, sede bata san ya zatayi ba saboda batasan tab’a sa. Tsayawa tayi kansa tana nazari...

 
*© miemiebee*

No comments:

Post a Comment