Saturday, 3 September 2016

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 18
BY MIEMIEBEE


     “I miss you too my Angel, bar kuka barin sake tafiya ba, I’m back forever.”  “Yeyy!” tasake hugging nasa. Bayan sun shigo su Abuu da Ummie duk sukayi hugging nasa sun mugun jin dad’in dawowansa. “Sannu da zuwa Baba” na cewar Ummie, “kar ka sake tafiya dan Allah.”
       “In shaa Allah Ummie.” Anas yayi assuring nata.
      “Erm Anas I’m sure Shettima ya sanar dakai halin da ake ciki koh? Ma’aikatan company’nka har gidan nan sukazo suna rok’o na in maka magana sukoma office.”
     “In shaa Allah monday zan bud’e Shettima ya fad’a min komai. I’m sorry baran sake barin gidah ba. Problems ne suka min yawa Abuu bansan ta ina zan fara solving ba.”

         “Anas just know we are here for you running is never a solution.”
        “In shaa Allah Abuu barin shiga daga ciki.” Amal dake mak’ale kan cinyarsa ta tashi tare da k’ara mak’ale hannunta a nasa. “Kekuma Amal ina zaki?” cewar Ummie. “Zanbi Ya Anas d’akinsa.”
   “A’a kinga Ya Anas ya gaji yana neman hutu da bakin kinnan zaki damesa.”
     “Ummie mana, barinyi surutu ba” tafad’a tana bubbuga k’afa.
     “Don’t worry Ummie, taho muje my Angel.” Gwalo Amal tama Ummie sannan tabi Anas d’akinsa.
 
    Bayan ya rage kayan jikinsa ya haura gado tana zaune kan couch “Ya Anas ina kaje daka tafi?” Ta tambayesa.
    “Hotel Angel.”
    “Ohhh! kasan kowa yayi kuka daka tafi, tunba ni ba we all miss you blue eyes.”
Ido ya zaro “Amal ina kika san sunan nan?”
    K’arya tayi “babu kawai ni na had’a.”
      “Yau ni kike ma k’arya? Saboda kinsan password d’ina kika fara min shisshigi a waya ko?” ya tambayeta.
      “A’a fah Ya Anas ranan ne wata ta turo message lokacin ina game a wayan shine... Shine..” Sekuma tayi shiru.
     “Shine kika bud’e kika karanta koh?”
     “I’m sorry Ya Anas please karka canza password d’in.”
    “Toh naji barin d’an kwanta koh?”
     “Okah ba-bye” nan ta mik’e ta fice.

        _Washegari..._

Yau ta kasance Monday da safe Anas ya tashi ya shirya cikin black suit, black shirt da white necktie wanda yamun masa kyau bayan yayi  breakfast yaja benz na sa ya fice zuwa office. Daidai k’arfe takwas ya isa mutane turum ya tarar bakin k’ofar duk shi suke jira yana fitowa sukayi kansa suna gaishesa da “Boss” bayan ya bud’e office d’in ya shiga  elevator zuwa last floor inda new office nasa yake. Kallon office d’in kawai yake se gani yake kamar Baba ze shigo ya zauna kan office. Ba abin arzikin dayayi ranan inbanda  tunanin daya tayi seda signing papers da ake ta kawo masa. Sosai su Kacallah da Yunus suka yi condoling nasa kamar yadda duk sauran ma’aikatan suka masa. Sam be saba ba in suna kiransa da Boss. Aranan akayi renovating office d’in yakoma komai na ANAS IBRAHIM FAUZY.

     Office ne babban gaske me ciki biyu wanda harda d’aki ciki. Fridge, California bed, TV ba abinda babu ciki.
     Da yamma da misalin k’arfe 4:00PM daidai lokacin da suka tashi bayan Anas ya tattara stuffs nasa Kacallah ya shigo. “Uh sorry Boss bansan har ka tashi ba, wallahi seda aka tashi Ahmaz investment daga Kaduna suka kawo wannan kuma gobe zasu koma. “I’m so sorry please.”
   “Bakomai” Anas ya fad’i yana murmushi “kawo inyi signing.”  “Thank you Sir! You’re so kind.” Nan Anas ya zauna bayan yayi signing Kacallah ya sake masa godiya yakai da bakin k’ofa Anas yace, “uhm Kacallah are you free?”
     “Yes Sir wani abu ne?”
      “Ba abinda zanyi yau nace ko zakazo mud’an fita maybe muje muyi having snack tare I need someone to talk to.”
     “Oh yes ofcourse Sir barin kai wannan kafin su tafi.” Kai Anas ya giad’a masa “thank you”
    “The pleasure is mine sir.” Nan yafice bada dad’ewa ba ya dawo suka shiga elevator tare. A motan Anas suka fice, “so ina kakeso muje?” Anas ya tambayesa.
 
       “Duk inda kace will be fine Sir.” Cewar Kacallah cike da girmamawa.
    D’an murmushi Anas yayi “in mu bibbiyu ne kana cemun Anas kawai.”
      “I’m sorry sir amman baran iya ba, girman ka yayi yawa ace na kiraka da sunan ka. I’m sorry please.”
    “Tun da haka kace fine, so ina zamuje.”
     “Muje Fahmaz coffee shop Sir.”
   “Fahmaz Fahmaz...” Anas ya tsaya nazarin abu “ohh sune wanda in an kirasu waitresses nasu basua magana a wayan nan koh?”
   “Ahha Sir nakega basu gane ko kai waye bane. Muje chan d’in please you’ll like their services.” Ba musu Anas ya tuk’asu zuwa coffe shop nasu Fannah.

    Bayan yayi parking suka fito suka shiga tundaga bakin k’ofa aka fara tarerayar su Anas anga Nigeria’s most youngest billonaire. A special table suka zauna. Ya suleiman ne yazo ya musu sannu dazuwa da kansa sannan ya d’auki order’n su. “Mr. Fauzy is my honour having you here at my coffee shop what can I get you?” Ya fad’i yana washe 32.
   Kai Anas ya giad’a masa sannan ya dawo da kallon sa kan Kacallah. “Me zamuyi ordering?”
     “Sir nikuma zan mana ordering please do, ni ai duk abinda ka mana ordering I’m fine with it.”
    “No Kacallah I insist ka mana ordering. Feel free with me please.”
        “Tunda kace haka sir OK. Akawo mana caf`e lat`e.”
     “Unfortunately bana shan coffee.” Anas ya fad’a yana kad‘a kai.
     “Ohh sorry sir but da ka gwada gaskia nan coffee shop suna k’ok’arin yin coffee.”

     “Yes Sir” cewar Ya suleiman “ka gwada coffee’n mu I’m sure you will not regret it, please.”
       “Tunda kunyi insisting okay. Get us two caf`e lat`e.”
      “Thank you sir” sannan ya fice yana shiga ciki ya soma k’olla wa Fannah kira. Nan tafito tana daidaita hijabinta. “Yes Boss!” Ta fad’i cike da gatsine. “Yawwa yau zo ke zaki had’a coffee’n nan. Inason ki had’a coffee’n da baki tab’a had’awa ba.”

        “Tohhh d’an shugaban k’asa ne yazo coffee shop namun?” Ta tanbaya tare da d’age gira.
     “You will find out in kika kai musu. Two cups, ki had’a yayi kyau please Fannah give it your best. Table 03.”
   “Okay Sir” tace tana dariya. Nan ta hau had’awa bayan 3 minutes ta gama ta aza kan tray sannan ta fice. Kanta a k’asa tana kaiwa zuwa table 03 ta gaishesu tare da ajiye wa a gabansu.
 
     “Thank you” Kacallah ya fad’i nan ne ta d’aga kai ta kallesa “you’re welcome” ta masa murmushi jin d’ayan bece komi ba yasa ta juya ta kallesa lokacin kuwa hanky Anas ya cire yana goge fuskarsa se bata samu ta gansa ba. Tana ajiyewa ta fice.

      Anas na kai coffee’n baki yaji k’amshi sosai. Dayasha kuwa yaji dad’insa sosai tunda yasan kansa be tab’a shan coffee me dad’i ba kamar na yau ba last time dayasha a London kwata kwata be masa dad’i ba sesa yabar sha ma. Be cire cup d’in daga bakinsa ba sanda ya kurb’e duka. “Wow! coffee’n nan yayi dad'i sosai, this is the first time coffee yamin dad’i. In ba damuwa inason in k’ara.”
   Murmushi sosai Kacallah yayi “I told you sir. Waiter!” Ya kira wani na miji me uniform “caf`e lat`e zaka k’aro wa Boss d’ina.”
     “Okay” ya fice nan da nan yaje ya had’o ya kawo saidai da Anas ya tab’a ya ji na d’azun yafi dad’i. Da kyar ya had’e dan yadda ya yamutsa fuska yasa Kacallah tambayan ko lafiya.
    “Sir are you okay?”
    Ajiye cup d’in yayi “ba wannan nasha d’azu ba. Irin na d’azu nakeso.” Anas yace.

     “Sir” cewar waiter’n. “Caf`e lat`’n daka buk’atan nefa kalan na d’azu.”
   Tsawa Anas ya daka masa “No!” “nace ba eri d’aya bane kaje ka sake had’o min irin na d’azu.”
  “But sir-”
     “I said now.” Anas ya sake daka masa tsawa. A tsorace yabar wajen.
    “Sir I'm so sorry please” cewar Kacallah. “Is okay ba komai.” Anas ya tabbatar masa.

    Shigar waiter'n ciki yasamu Ya Suleiman. “Ya akayi Harauna?” Cewar Ya Suleiman.
    “Ya Suleiman CEO’n Flames Enterprises ne yace na had’o masa caf`e lat`e na had’o masa kuma wai ba irinshi yakeso ba, wai ba irinsa yasha d’azu ba.”
     “Omg!” Ya Suleiman yayi exclaiming.
  “Ina Fannah? Jeka kirata ita ta had’a masa kace tazo ta barinje in basa hak’uri” da “toh” suka rabu. Isan Ya Suleiman cikin shop d’in yayi kan table nasu Anas. “Sir please kayi hak’uri anje kiran yarinyan data had’a na farkon ne yanzu zata zo kayi hak’uri dan Allah.”

      “Make it quick inada abinyi please.” Cewar Anas nan Haruna yafito “Ya Suleiman Fannah bata nan ta tafi yanzu Asma’u ke fad’a min.”
    “What!?” Cewar Ya Suleiman. “Taya zata tafi? This is the first time take barin nan bata fad’a min ba.” Nan ya kewayo da kallonsa kan Anas.
    “Mr. Fauzy I’m so sorry please yarinyar data had’an ta tafi gida nakega emergency ne yataso but akoi wata itama ta iya had’awa sosai barin mata magana.”
   
      Ran Anas tafasa yake, “then make it quick!” Yafad’a a tsawace.
    Bayan ‘yan mintuna Asma’u tafito da coffee’n Anas. Tana ajiyewa ya d’auka yayi sipping nan ma taste d’in be masa ba wurgi ma yayi da cup din coffee’n ya zube a yayinda cup d’in ya tarwatse b’ari Asma’u ta soma. “Wai ace nan cofee shop amman ba me iya had’a coffee?” Ya Suleiman ne yafito yana ganin irin b’arnan da Anas yayi shi bama wancan ba kar Anas yasa ayi sueing coffee shop nasu.

    Hak’uri ya soma basa. “Mr. Fauzi wallahi wanda ta iya had’awan ne ta tafi gida.”
    “Wacece ita?” Anas ya tambaya rai b’ace.
   “Fannah ce Sir Fannah Aleeyu.”
    “Koma wace ita call her now kace mata ta dawo and make me coffee.”
      “Yyesss sir” Ya Suleiman ya amsa baki na rawa. Wayarsa ya ciro ya kira Fannah har ta tsinke bata d’aga ba se a karo na biyu. “Hello Fannah ina kikaje? Ki dawo please is urgent.”

      “Ya Suleiman jikin Baba ne yatashi yanzu haka asibiti zamu kaisa bareyi in dawo ba.”
   
     “Fannah dan Allah su Mama barasu iya kaisa ba? Nasan lafiyan Babanki means alot amman you are needed here rashin zuwanki ze iya jefa lafiyar coffee shop in mu cikin matsala please.”

     “Ya Suleiman if only I can come, baran iya barin Baba ba dan Allah kayi hak’uri I have to go” karap ta kaste wayar. Fuskar Ya Suleiman kad’ai amsa ce ga tambayar Anas. “So?” Ya tambaya

     “Sir we are so sorry amman yarinyar barata samu zuwa ba.”
     Kallonsa Anas yake “kasan ko ni waye ne? Nace ka kira Fannah take ko meh and tell her tazo ta had’a min coffee.”
       “Mr Fauzi mahaifinta ne ba lafiya saisa barata iya zuwa ba.” Anas najin ance mahaifinta yaji ya hak’ura. “Okay” yace tare da ajiye musu N1,000 kan table d'in yaja jakarsa a yayinda Kacallah yabi bayansa.
      Mamaki ne yacika Ya Suleiman da Asma’u daga jin ance mahaifinta kawai ya canza mind nasa ga kuma dubu d’aya daya ajiye musu ba tare da ya amshi chanji ba. Shide gode wa Allah yayi.

   _Wahsegari..._

     Da misalin k’arfe uku da rabi Anas ya zo coffee shop nasu Fannah shi kad’ansa. Tun jiya ya kasa bacci dan kwad'ayin coffee’n dayake tayi. Sam yarasa meke masa dad’i duk abinda yasa a bakin sa bai masa dad’i shi coffee d’in kawai yakeso duk ya k’osa yasake sha. Bayan yashigo aka karb’esa da girmamawan daya cancanta, nan yayi ordering caf` lat`e. Bayan yaron ya juya Anas ya kirasa “and kace Fannah... Fannah Aleeyu ce ta had’a and no one else okay?”
   “Okay” yaron yace masa. Yana shiga yasamu Fannah zaune tana buga gamw a wayarta yakai mata order’n ba tare da ta kallesa ba tace, “wai nikad’ai kake gani anan ne Boy? Ga Asma’u da Allah ka kai mata kaga game nake yi hak’uri.”

     “Ya Fannah shi wanda yabada order’n ne yace ke zaki had’a.”
   Baki wangalau Fannah ta bud’e lallai ma “yaushe aka fara wannan sabon salo? Coffee ba coffee bane waikam. Koma waye ne yayi hak’uri barin had’a ba tunda ba shift d’ina bane, Asma’u da shift nata ne ta had’a.” Daidai lokacin Asma’u ke shigowa cikin kitchen nasun. “Yawwa gara ma da kika shigo. Gashi caf`e lat`e zaki had’ama wani kiyi sauri.”

     “Waye ne?” Asma’u ta tambayi yaron. “Nima bansan sunansa ba.”
   “Ya yake? Fari ne yanada blue eyes?”
 
     “Eh” yaron ya giad’a kai. “Fannah dan Allah kiyi hak’uri ki had’a masa wallahi shine wanda yazo jiyan.”

    “Wai waye shi duk kika bi kika tsure haka?”
     “Fannah wallahi shine, Mr Fauzi d’an marigayi Alhj.  Muh’d.”
    “shi???” Fannah tafad’i tare da zaro ido.
      “Fannah dan Allah wallahi naki kawai yakeso, jiya nida Haruna muka had’a masa coffee wulli yayi dashi, please Fannah” ta k’are maganar kamar zatayi kuka.
    “Chabdi!” Cewar Fannah “ai gara ke ni da kike gani nannan wallahi banasan abinda ze sake had’ani da Anas d’innan ranan har kuka sanda yasani.” Daidai lokacin Ya Suleiman yashigo ransa b’ace “wai Fannah meke damunki ne? Bakisan da abinda kikeyi zaki haddisa mana problem ba? Wuce ki had’a masa coffeen kinsan ko waye shi?”

      “Ya Suleiman amman shift na Asma’u ne fah.”
   Katse ta yayi “amman kuma ke Mr Fauzi yakeson ki had'a masa off you go.” Zata k’ara magana ya daka mata tsawa “now!” hawaye taji na ciko mata a sanyaye ta mik’e ta had’a masa takawo gaban Ya Suleiman ta ajiye. “Gashi.”
      “Aww nikuma zan kai masa? Kikai masa yana san miki magana.”
     “Ya Suleiman dan Allah kayi hak’uri kaba wata ta kai masa wallahi banasan magana dashi dan Allah.”

     “Fannah I can’t say no to him kawai kije ki rufa wa coffe shop namu asiri.” Zata sake magana ya fice juyowa tayi ta kalli Asma’u da take ta kau da kallonta elsewhere. Miyau ta had’iye sannan ta fice kaiwa Anas kujerun ta duba sannan can ta hangesa dukda bata ga fuskarsa ba amman daga farinsa ta ganesa. A hankali ta k’arisa kan table d’in ta ajiye a lokacin yana kan waya yana kallon window. Tana ajiyewa ta juya zata tafi holding wayar yayi “Boss naki be fad’a miki inasan miki magana bane?” Ya fad’i authoritatively ba tare da ya kalleta ba. Cak ta tsaya tare da kewayo wa...

    *© miemiebee*

No comments:

Post a Comment