Saturday, 3 September 2016

TANA TARE DA NI..

TANA TARE DA NI... PAGE 54
BY MIEMIEBEE



    Se Asuba da Fannah ta tashi Sallah ta tuna ashe waya take da Mr. Fauzi bacci yayi gaba da ita. Wayarta dake kwance a gefenta ta d’aga to her suprise taga Anas be kashe wayar ba. “OMG! Whattt!!!” Ta fad’a cike da mamaki, yanzu Mr. Fauzi be kashe wayar ba tun tun tuni? Har zata kashe seta tuna kuma what if be tashi yayi Sallah bafah? Daman ba ma’abocin Sallah akan lokaci bane. “Anas” takira sunansa ta wayar softly. Bacci sosai Anas yake wayar na ajiye kan pillownsa.
     “Anas!” Tasake kira da d’an k’arfi nan ma shiru. “Mr. Fauzi!!” Ta kira da ihu kwanciyansa ya gyara kodaya bud’e ido seya rasa daga ina ake kirar sunansa ko kad’an hankalinsa bekai kan wayar dake kan pillon sa bane.”

    “Mr. Fauzi wake up, wake up kaji? Fannah ce.” Se a yanzu yakai dubansa kan wayarsan yaga Fannah ke magana ba b’ata lokaci ya kai kunne cikin gigin bacci “Fannah” ya kira sunanta.
  “Huh!” Ta saki numfashi. “Good morning.”
   “Morning? Har safiya tayi neh?”
   “Yes Anas and bakayi Sallah ba.” Ze mata k’arya yace yayi sekuma ya fasa instead yace “lokaci beyi ba anan.”
    “Aww haba? Ta fad’i cike da gatsine “dad’in abin lokacin Morocco da Nigeria d’aya suke tafiya nan kuma lokaci yayi kaga chan ma haka kenan.” Kunya yaji sosai Fannah ta kamasa yana k’arya.
    “Toh aini bansani ba.”
   “But now you do tashi kayi Sallah toh.”
   “I’ll bari in 6 yayi I need to sleep a little more.”
   “Anas har 6? Ana sallah 5:10-5:20 kace kai sai 6? Ba kyau jingina Sallah fa. Yi hak’uri ka tashi kaga nima banyi ba semuyi tare kaji Anas?”
   “No se 6 I’m hanging up.”
    “No boyfriend karka katse please, katashi muyi Sallah kaji? Yi hak’uri kaga inka idar se ka koma bacci...” Da k’yar ta samu tayi convincing nasa ya yarda

   ****
   12:30PM su Anas suka k’are first meeting daya kawosu Morocco, da k’yar ya iya yayi breakfast da safe dan yadda yake missing coffeen Fannah. Zaune yake da laptop nasa a gabansa yana ‘yan aiki alokacin da wayarsa ya soma ruri. “Hello” yace bayan ya d’aga “dama nace meetings d’innan bara a iya rescheduling muyi duka a gobe ba? Nagaji da zaman nan, I wanna go back home.”
    Ta wayan akace, “but Sir you just arrived yestarday, nan da 3 days duk komai ze k’are, ka k’ara hak’uri please.”
   “NO!” Ya fad’a a tsawace “hak’uri na ya k’are ni nagaji ko kayi rescheduling a k’are komai a gobe kokuma kuyi meeting naku ba ANAS IBRAHIM FAUZI.”
  “Sir please calm down, naga bawai family kake dashi achan Nigeria ba why in such a haste?”
   “Yes banida family amman inada girlfriend and I’m missing her ni na fad’a maka do what is need to be done.” Karap ya katse wayar. Laptop d’in ya rufe a fusace tare da jingina jikin couch dayake zaune akai. Duk yadda yayi denying he can’t he is missing Fannah, baya missing Amal kamar yadda yake missing Fannah. Number’n ta ya kira.

     Alokacin Fannah na zaune dasu Baba a d’akinsa se hira sukeyi tana ganin number’nsa da tayi saving da Anas ta saci jiki ta nufa d’akinsu bayan ta baje kan gado tayi picking “hello Anas.” muryarta kawai ya jiyo se kawai yaji duk wani b’acin ransa ya gushe.
  “Fannah I’m missing you.” Yace tsakani da Allah ba kunya ba tsoro ba komai, he needs to tell her saboda the more yana keeping secret d’in wa kansa the more yake missing nata a kowani second.
    Gatsau tajiyo abinda ya fad’a matan, kamar ya he is missing her? Ai coffeen ta yake missing a kullum ba ita ba, ta b’angare guda kuwa wani irin feeling da bata tab’a feeling ba taji ya ratsa ta.
   “Fannah are you there?” ya tambaya jin tayi shiru. Nanne ta dawo daga duniyar tunanin data wula.
   “Uhm... Ermm. Yes Sir.”
    “Stop calling me Sir.”
   “I’m sorry Anas ban-” katse ta yayi.
   “Fannah I miss you, I want to come back, I miss everything about you.” Wai meke damun Mr. Fauzi ne? Ta tambayi kanta. Rasa na cewa tayi chan tace, “Anas calm down kaji? Nan da 3 days zaka k’are komai kaga seka dawo, dama zama mutum kad’ai ba dad’i hak’uri zakayi kaji?”
   “But I miss you.”
    “I miss you too Anas hak’uri zakayi kaji boyfriend?” Shiru yayi be amsa ba, “boyfriend?”
   “Yes” ya amsa chan k’asa-k’asa.
    “Kayi hak’uri kaji? What are you doung now?”
    “Nothing, jus sitting alone.”
  “Call up Amal nasan she will have alot to tell you, kaji?”
     “But I don’t want to, ni dake nakeson nayi magana.”
   “Toh nikuma ai bansan me zance maka ba.”
    “Tell me anything.”
   “Anything like?”
   “Your boyfriend.” Shi kansa besan lokacin daya fad’a hakan ba, kawai seyaji yanason yasan ko Fannah nada wani saurayin.
    “Ni banida boyfriend.”
  “Yusuf fah?”
    “Anas Yusuf ba boyfriend d’ina bane kawai good friend ne thats all.”
    “Okay who is your boyfrined yanzu?”
   “Banida boyfriend.” Ta mayar masa da amsar d’azu.
     “What of before?” Ahmad nata ne ya fad’o mata arai, masoyinta na hak’ik’a da aka rabasu na k’arfi da yaji, incident daya faru da ita a Bama na yadda wani azzalimi yayi raping nata ne kawai ya soma dawo mata batasan lokacin da ta fashe da kuka cikin wayar ba.

      A rikice yace, “Omg Fannah why are you crying? Saboda question dana miki neh? I take it back bar kukan kinji?” Hannu tasa ta share hawayenta cikin kuka tace, “no ba kai bane, I’m sorry.”
    “Ex boyfriend nakin ne?”
    Kamar tana gabansa ta girgiza kai. “Shine?” Ya sake tambaya hankali a tashe. “Ba shi bane.”
    “Do you want to talk about it?”
   “No it makes me cry.”
   “Shhh! Is okay bar kukan kinji? We will talk later.” Nan ya katse wayar duk hankalinsa yabi ya tashi, meh yasa Fannah kuka? Meh saurayin nata ya mata da dazaran anyi maganansa take kuka?

    Through out ranan Anas be kira Fannah ba aganinsa karya tak’ura mata, itako har ta saba d’an kwana biyu da suke yin waya, dabe sake kirarta ba setaji wani eri, ita kanta bata san wani erin feeling take ma Anas ba. Tana enjoying every single second da take spending da Anas hakan kuwa na nufin sonsa take kenan. Amman sede tana tsoro, tsoron ta fad’a tarkon son sa wataran gaskia ya bayyana ya guje ta, abinda barata iya jurewa ba kenan sesa take yayyafa wa zuciyarta ruwan sanyi da son Anas.

   ★★★★★
_1 day later..._  
    Kamar yadda Anas ya buk’ata a washegarin akayi rescheduling masa duka meetings d’in, a ranan yayi attending duka kansa kamar ze fashe gashi rabuwar sa da waya da Fannah tunda da ta fashe masa da kuka a waya shekaran jiya. Yana son kirarta amman bayasan tak’ura mata kuma he is damn missing her.
    Itama Fannah ta b’angarenta haka ne, so take ta kirasa amman kuma tana tsoro kar ya gwale ta yace mata waya rok’eta.

    _10:20PM_
   Kasa hak’ura tayi ta kira sa, dan hankalinta ya matuk’an tashi seji take kamar ba lafiya ba. Har call d’in ta tsinke Anas be d’aga ba, yana gani amman yak’i picking se a karo na biyu nan ma bece komai ba ita ta soma magana. “Anas.”
    “Yes Fannah.”
    “How are you?”
   Be amsa ba ya tambayeta “how are you too?”
    “Alhamdulillah, just called to check on you, se anjima.”
    “Wait Fannah, I miss you.”
     “I miss you too.” ta fad’a sincerely kamar yadda shima yayi. Hira kad’an suka tab’a sam be fad’a mata gobe ze dawo ba he wants to suprise her.
 
    Washegari da misalin k’arfe 2:00PM jirginsu Anas ya sauk’o a International Airport dake Abuja daga chan yashiga na Maiduguri direct. 2:30PM yamasa agarin Maidugiri, already Shettima da Amal suna jiransa. D’an tafiyan kwana uku yayi amman Amal seji take kamar shekara tayi bataga Ya Anas nata ba, haka kowa ma agidan. Abinci suka gama chi ya shiga d’akinsa dan watsa ruwa, tsatsaf ya sami ko ina har cikin wardrobe nasa yaga an gyara masa, murmushi kawai yayi danko yasan wa yayi hakan, Shettima ne. Bayan yafito yasa baqar ¾ wando da baqar plane T-shirt. Key’n motar sa ya d’auka ya fice.

     Fitowarsa parlour kenan, “Babana daga dawowa se fita kuma?” Cewar Ummie tana taya Amal tsifa.
   “Eh Ummie aiki just came up a office.”
   “Toh Allah kare.” Nan ya fice be zarce ko ina ba se gidansu Fannah. Almajiri ya tura ya mata sallama bada jimawa ba tafito sanye dawani light purple hijabi me hannu kodan ya jima be sata a ido bane seyaga ta k’ara masa kyau dukda ba makeup bane a fuskarta.

   He can’t explain how he missed her, rashin ganinta ya kasance wani babban rashi tattare dashi wanda bare iya bayaninsa ba.
Mamaki sosai tasha ganin Anas, har ma kamar bata yarda ba ko decieving nata idanunta suke ne? Ai ko ajiya da sukayi waya bece mata zezo ba.
      “Senayi magana kice ba kallon soyayya kike minba.” Magnarsa ne ya sake tabbatar mata da eh Anas ne a gabanta a hankali ta tako zuwa gabansa. “Anas! Yaushe kadawo?”
    “Some few hours back.”
  “Welcome back” murfin motar ya bud’e mata “get in I have something to show you” ba gardama tashiga bayan daya zaga ya shiga shima ya ciro wasu files ya mik’a mata bayan data amsa taga heading d’in *CONTRACT MARRIAGE AGREEMENT* rubuce da babban bak’i. A hankali tabi ta soma karanta rules d’in.
    Duka sun mata sede na had’a gadon ne battaso dukda kuwa yasa a k’asa ba abinda ze shiga tsakaninsu amman still tana tsoro, bata son Anas yasan ba virgin ce ita ba. Pen ya mik’a mata “sign them.” Ba gardama tabi su one by one tayi signing bayan da tagama ya amshe “very good I hope my rules are clear? Don’t fall for me, don’t get jealous in kinganni da wata mace.”

      “Ka kwantar da hankalinka nima dan banida wani option ne yazama min dole in yarda da wannan aure if not ba abinda ze had’a mu kwanciya gu d’aya da kai”
   “Allah sa” yace a lokacin da yake miyar da files d’in cikin envelope daya cirosu. “So auren will take place in a month time, you have 4 weeks to prepare.”
    “Wata d’aya?!” ta dafe k’irji tare da zaro ido in disbelief.
   “Yes wata d’aya Miss Aleeyu.”
   “But Sir wata d’aya yayi kusa ina laifi biyu ko uku?”
    “Huh! Look at you nid’in ance miki dan inaso ne? So nake ayi auren muyi mu rabu in huta dake in huta da Abuu. So don’t think othwrwise ki d’auka ko dan inason ganin ki ne always na matso da bikin.”

    Itade har yau barata iya fad’in ga halin Mr. Fauzi ba, in baya kusa da ita ya riga ce mata yayi missing nata ayau suka had’u kuma yasoma gasa mata bak’ar magana.
    “Anas to gidan da kake ginawan fa? Ai ba’a gama ba kaga ba yadda za’ayi ayi bikin nan in a month time.”
     “Nasani saisa zamu zauna a hotel for the meantime, nanda 2 months za’a gama ginin semu tare.” Ita har yanzu hankalinta be d’au wata d’ayan nan ba, haka kawai tasoma jin tsoro.
      “Anas ai bamu keda ikon sa wa bikin date ba, iyayenmu ne ko ba haka ba?”
    “I have money Miss Aleeyu inma a gobe nakeson ayi bikin za’ayi inada komai under control. Bana buk’atar ki saya wani abu, komai ni zanyi just ki sanar da Mami maybe gobe ko jibi Abuu zasu so kinji?” Kamar wacce barata motsa ba ta gyad’a kai.
    “Can I go now?”
   “Yes you can, nima nagaji da ganinki cikin motar.” Bata bar bak’ar kalamunsa suka tab’a taba ta fice. “Fannah I’m sorry for hurting you banasan kigane ko ina sonki ne saboda nima har yau bansan wani erin feeling nake miki ba, a farko nace tausayi ne sekuma naga bakida abinda za’a tausaya miki ayanzu amman kuma har a yau I care about you, I’m afraid I love you amman barin bar wannan love yayi ruining d’ina ba, I will do whatever it takes in kashe ‘yar soyayyar because I'm Anas Ibrahim Fauzi its not in me to fall in love.”

    ****
     “Anas, Ummie tace kanason magana dani.” Cewar Abuu dake k’arisowa cikin parlour’n da daga Ummie se Anas ke zaune ciki.
     “Eh Abuu.” Bayan Abuu ya zauna Anas yayi gyaran murya, “Abuu batun matan aurer da kace in nema ne nakeson sanar dakai na samu, ina sonta kuma zan aureta.”
   “Alhamdulillah! Alhamdulillah! Sede wace yarinyan? ‘yar wace gida ce?”
  “Ba ‘yar kowa bace Abuu, Fannah PA ta ce, tanada diploma a Business Admin am very sure she’ll bring a great contribution to my Enterprise bayan ta zamo mata ta saboda ko a yanzu with her beside me nayi achievibg abubuwa da dama.” Kai Abuu ke gyad’awa nufin he is convinced, ya yarda.

    “Toh Masha Allah Anas a gaskia ina me matuk’ar farin ciki da Allah yabani d’a me hankali kamar ka, Allah saka maka da alkhairi Babana. Ita kuma Fannah ko?” Kai Anas ya giad’a Abuu yacigaba “zanso kamin kwatancen gidansu sabida inje inji kuma ingani ko d’iya ce me tarbiyya.”
   “Ba matsala Abuu first thing gobe zan kaika har gaban mahaifinta.”
   “Toh toh masha Allah sannu ko Babana?”
    “Yawwa Abuu one last thing please.”
“Mene ne Baban tell me.”
   “Abuu inda hali banasan bikin auren ya wuce nan da wata d’aya, inason Fannah Abuu I can’t wait har zuwa nanda wani dogon lokaci bata kasance mata taba, if possible nan da one month ayi komi ya k’are.”
    “Wannan ai ba matsala bace Babana kaida kake da kud’i a hannu. Addu’armu de kawai Allah sa muji sheda mekyau a gareta goben, yaso ko a jibi a muku aure in iyayenta suka amince.”
   “In shaa Allah ma zasu amince Abuu nide kawai kar ya wuce nan da wata d’aya.”
   “Allah kaimun toh.” Nan duk suka amsa da “Ameen” sannan Anas yayi d’akinsa. A hankali ya bud’e k’ofar kamar ko yasan Shettima na ciki.

     “Aww ashe kaine b’arawon. Oya miyar! Miyar nace!”
   Shettima dake zaro bundle na d’ari bibbiyu daga safe na Anas ya tsule besan lokacin da ya zubar da kud’in daya kwasan duka a k’asa ba.
     “Wayyo! Ya Anas ka tsoratani wallahi.”
   “Naji miyar b’arawo kawai. Ashe kaine, tun dawowa na naga kud’in safe d’innan ya ragu ashe kaine b’arawon ka gama min sata kaje ka samu Afrah kace mata kana business koh? Toh k’aryanka ya k’are yau.”

    “Ya Anas fa basata nake maka ba, arranging kud’ad’d’den nake.”
  “Ka rantse” Anas ya katse sa shiru Shettima yayi yakasa rantsuwar. “Oya ina ganinka one by one mayar min da kud’i na.”
   “Ya Anas mana dan Allah ko guda biyu ne kabani please wallahi na mata alk’warari kaji dan Allah.”
    “Seka karya, nide miyar min kud’ina dan tsiya duk wanda ka riga d’iba basu isheka ba? Mayar min ka fice kuma.” Kamar wanda zeyi kuka yasoma miyarwa ganin idan Anas bai kansa ya zira d’aya cikin aljihu ai kuwa Anas ya gansa ta gefen ido. “Miyar fa na riga na ganka b’arawo kawai, kai barakayi karatu ba se soyayya da sata ka iya.”

     “Ya Anas d’aya fa dan Allah” ya maraice fuska.
  “D’auka ka bani waje.”
   “Yeyy! Nagode sosai Allah bar mana kai.”

   Washehari da misalin k’arfe 11:00AM Anas yasa Abuu dawasu uncles nasa guda uku cikin mota se unguwar su Fannah kafin su shiga gidansu Fannah seda sukayi tambaya gidan mak’ota kusan biyar kan halayen Fannah sede kowa shaida me kyau yake bata yana yaba hankalinta kuma. Dad’i sosai Abuu yaji daga nan suka shiga gidansu Fannah banda Anas. Maganar awa d’aya da mintuna aka sukayi aka yanke hukuncin date na bikin Anas da Fannah a wata d’ayan da Anas ya buk’ata, Abuu ya d’au nauyin yin komai, ko tsinke be yarda Fannah ta kai gidan mijinta ba saboda yadda ya karanchi basuda arziki. Shopping da Anas ya musu Abuu yasa almajirai suka shigo dasu. Inbanda godiya ba abinda Baba da Mami keyi. Afrah kam bakin nan har kunne Fannah zatayi aure, zata auri Nigerian’s youngest billonaire tasan dole suhau gidan TV suma.

   Fannah de ta rasa me ke mata dad’i, wani tsoron Anas da bata tab’a ji ba ta soma ji yanzu. Taya zata auri Boss nata? Taya zasu kwanta gado d’aya da Anas su zauna under thesame roof da wannan halin nasa. Tsoronsa ta soma ji alokaci d’aya segani take kamar wataran ze buk’aci abin da battaso wani d’a na miji ya tambayeta, inya tanbayeta me zata ce masa? “Wayyo Allah barin iya ba.”
   Ita dama Ya Farouq ta aura atleast shi yasan sirrinta. Wata zuciyar ce tace mata toh ai kunyi signing contract ba abinda ze shiga tsakaninku saboda haka ki kwantar da hankalinki. Zuciyar tata ta gwada bi sede tsoron se k’aruwa yake.


  *© miemiebee*

No comments:

Post a Comment