Saturday, 3 September 2016

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 20
BY MIEMIEBEE


Ringing wayar yake amman ba response, bayan ya tsinke ta sake gwadawa nan ma haka har ta tsinke Anas be d’aga ba.
         Anas na kwance kan gadonsa yana ganin wayan na ringing ko yunk’urin d’agawa beyi ba danko baya d’aukan waya within time d’innan inba wai familiar number yagani ba. D’ayar number’nsa ta zuba nanma two missed calls duk be d’aga ba. Anas na gani nanma yak'i d’agawa. Fuksarta cike da disappointment tajuyo ta kalli Afrah. “Afrah be d’aga ba 4 missed calls na masa be d’aga ba. Omg!” Wayarta ta duba taga lokaci pass 5. “Oh no! Se yanzu na tuna sanda yace min kar na kirasa within 5 to 8.”

     “Toh seki bari se anjiman ai ki gwada.” Kai Fannah ta giad’a mata.

****
     Sosai Anas yayi missing coffee’n Fannah, bayasan shan komi inba coffee’n Fannah ba. Tun ranan da suka had’u yake jiran kirarta amman shiru. Bayan kwana biyu yaje ya duba coffee shop nasun yaga k’urumus komi ya k’one a tunanin sa wai a ranan ko washegari Fannah zata kirasa ta amshi aikin daya offering mata amman ina har yau shiru, k’ok’arin mancewa da coffee’n yake tunda basamu zeyi ba. Inda kuwa yasa a binciko masa ita da a ranan ze sameta amman kuwa girman kai irin nasa bare barsa ba.

     Washegari da safe da misalin k’arfe tara bayan Fannah tagama shiri tasaka atamfa ne ja da baki seda bak’in hijabi wanda yamugun sake fidda hasken ta. Ba makeup kamar yadda ta saba, daga kwalli se kwalli da lipgloss a baki ta d’au credentials nata tana shirin fita zuwa company’n Anas tunda bata samesa ta waya ba zataje ta samesa in person. Koda ta sake kiran sa ajiyan around pass 9 be d’aga ba acewarsa wai ko irin mata masu kiran san nan ne danko kirar yayi yawa.

      Isarta company’n keda wuya. Wannan shine karo na biyu da take sa Enterprise d’in a ido. Bayan tashiga ciki ta tsaya raba ido dan bata ma san ta ina zata fara neman Anas cikin wannan babban building ba, ita bama wannan ba karya ganta ya cicci mata mutunci yanzu danko baida mutunci. Reception ta hango ta k’arisa wajen da fara’arta ta gaishe da receptionist d’in wani kallon bakwai saura kwata ta mata “how can I help you?” Tace da Fannah tana tauna chewing gum bakin nan yasha jan janbaki.
       “Uhm Mr. Fauzi nazo gani please.”
     “Mr. Fauzi?” Cewar receptionist d'in tare da d’age gira. “Ked’in zaki ga CEO? LOL” ta k’yalk’yale da dariya.
       “Eh kwanakin baya ya tab’a offering d’ina aiki yace kan duk sanda na yi making up mind d’ina in zo in samesa. Ki kaini wajensa please.”
      “Ya sunanki?”
    “Fannah Aleeyu.”
    “Kina da appointment dashi ne? Yasan da zuwanki? Is he expecting you?”
     “Actually no amman in ya ganni ze tuna please ki kaini wajensa please.”
     “Uhm Fannah kinga Boss d’ina is a very busy man bareyi in kaiki wajensa ba, ba tare da yasan da zuwanki ba in zaki zauna kijira in masa magana yaso ko zuwa gobe ko jibi se a had’a muku appointment seki dawo.”
     “Ma’am please kiyi hak’uri dan Allah I need this job so badly mahaifina ba lafiya ki taimaka please wallahi ya ganni ze gane ni.”
    “Fannah kinga kiyi hak’uri ki fice daganan dan nan ba gidan bada taimako bane.”
    “Ma’am please.”
     “Security!” Receptionist d’in takira “kuzo ku fita da wannan ‘yar please.” Nan security sukayo wajen suna tambayan meya faru. Daidai lokacin elevator yake bud’uwa Anas ne ya bayyano yana sanye da navy blue suit da blue sunglasses a fuskarsa, gashin nan anyi styling nasa masha Allah, fuskar nan nasa tamk’e ba alaman murmushi. Wani na miji ne a bayansa wanda ga dukkan alamu PA’n sa ne.
   
     Taku yake magestically cike da k’asaita yana duba agogon hannunsa da alaman meeting zasa, tafiya yake kai a sama yakaida wajen su Fannah ta kira sunansa “Mr. Fauzi” cak ya tsaya sannan a hankali ya juya ya kalleta ba tare da ya cire sunglasses d’inba. Yana ganinta ya tuna da ita danko kullum seya yi tunanin coffee’n ta ba k’arya yayi missing coffeen nata sosai sosai amman kunsan Anas da girman kai sam ba nuna mata zeyi yayi missing ba. “Good morning Mr. Fauzi.” Fannah ta gaishesa. Security’n ne ke k’ok’arin jan Fannah waje Anas ya dakatar dashi. Ba tare da ya amsa gaisuwar taba “whats going on here?” Ya tambaya authoritatively.

     Receptionist d’ince ta amsa sa. “Uhm Boss wannan yarinyan ne wai sunanta Fannah Aleeyu that tazo ganinka kuma ni na duba banga kunada appointment da ita ba.”
     Kallon rainin wayo yake ma Fannah “You’re right banida appointment da ita send her away.” Dagangan ya fad’i hakan danko yasan she is badly in need of the job saboda aikinta data rasa.
   “Mr. Fauzi please don’t send me away. Na yarda da aikin daka bani koda N10,000 ne zan karb’a please. I’m badly in need of the job na rasa aiki na please Mr. Fauzi.”
   
      Shiru yayi kamar wanda bareyi magana ba sannan cikin muryar sa me dad'i yace, “okay so wannan aikin is a second choice to you, sanda kika rasa wancan zakizo nan. I don’t need you yanzu na samu wanda ke had’amin coffee. Take her out” yace da securities d’in.
     “Mr. Fauzi please I beg of you dan Allah karka korani, I'm badly in need of this job.”
    Agogon hannunsa ya duha “I will have to think about it yanzu haka inada meeting in zaki zauna kijirani zuwa 12 zan dawo then se inyi deciding ko zan baki aikin ko baran bayar ba.”
       Wani sanyi Fannah taji a ranta dukda kuwa bawai aikin ya bata ba considering yace zeyi but still she is thankful. “Nogode Mr. Fauzi thank you so much zan jiraka.” Kallon ta yasake cike da rainin hankali sannan ya fice. Harara receptionist d’in ta watsa ma Fannah ita so take kar Fannah tasamu aiki anan da kyantan tannan tsab zata iya juya ma Boss hankali. “Toh ai ba tsayuwa zaki tayi nan ba ga kujeru can sekije ki zauna ki jirasa Allah sa bawai kinzo bane ki mana snatching boss dan ki sani yafi k’arfin ki.”

     Murmushi Fannah ta mata, “karki damu I have no intention of doing so, kema kin fad’a Boss naku yafi k’arfi na kinga ko ba ruwa da shiga harkansa.” Wucewa tayi ta zauna kan  d’aya daga cikin kujerun. Haka tata zama a wajen har tayi bacci ta tashi, har shabiyun tayi Anas be dawo ba. Azahar nayi taje tayi alwala tayi sallah yunwa tasoma ji gashi bata da kud’i. Se k’arfe biyu Anas yadawo wani dad’i taji data gansa shiko yi yayi kamar be ganta ba sanda ya kaida elevator’n ya tura saurayin dake bayan san kan ya kira Fannah.

     Hijabinta ta daidaita ta d’au jakarta sannan a sanyaye tabi bayan saurayin suna isa bakin elevator’n Anas ya sallami d’an nasa. Bayan ya bud’e elevator’n yashiga Fannah da be gayyace ta ba kuwa ta tsaya tana wasa da dogayen yatsunsa. Tsawa ya daka mata “well? Bara ki shigo bane kokuma se ya ruhu? Kin tabbata zaki iya min aiki kuwa? Banasan ana sani surutu.”
    “I’m sorry.” Sid’ak ta shiga bada jimawa ba elevator’n ya ruhu. Haka kawai taji zuciyarta na bugawa ita kad’ai da na miji cikin elevator. Ko kallonta ma beyi ba elevator’n na bud’uwa ya fita tana biye a bayansa. Wani card ya ciro yasa a jikin k’ofan office da aka rubuta Mr. Fauzi a sama. Bayan ya bud’u ya shige ciki, itama haka. Suit na jikinsa ya cire ya rataya jikin hanger sannan ya k’arisa kan fankacecen glass table nasa ya zauna kan kujera tare da sakar dawata numfashin gajiya. Kujeran ya nuna mata a hankali ta taka ta zauna. Hijabi ne a jikinta amman sanyi takeji dan yadda Anas ya k’ure AC’n kuma da alama shi bayya ji.

      “So seda kika rasa aikin ki na can zaki amshi nawa?”
   Rasa me zata ce masa tayi, ba kallonsa take ba amman tanajin alaman idanunsa kanta. “Have we ever met?” Ya tambayeta dan shima yasoma ji kamar ya tab’a had’uwa da ita somewhere.
    Take ta d’ago kai suna had’a ido ta kawar da kallonta a garesa sannan ta kad’a kai ai take ta tuna ya hanata using body language. “A’a” ta fad’a murya na b’ari.
    “Okay So kin karanta catering related course ne a university?”
      “A’a diploma nakeda a business admin.”
    “Uhmmm!” ya fad’i yana giad’a kai. “So are you ready to work for me?”
        “Yes I am” tabasa amsa take.
     “Nice” yace nanma yana giad’a kai. “Mesa kikazo office d’ina, dana baki card na ce miki nayi ki kirani bawai kizo ki sameni ba.”
       “I’m sorry Mr. Fauzi amman na kiraka har kusan 4 missed calls baka d’auka ba.”
        “Saboda kin kira ni time dana ce kar ki kira” ya amsata a takaice. “Ki kiyaye banasan ana sab’a min. So fad’a min nawa kikeson albashin ki ya kasance?”
     “Sir ni ko nawa kabani muddin be gaza N10,000 ba zan amince.”
    “Okayyy I will make it N100,000.”
   
   Ido wururu wururu ta zaro “N100,000 sir? Gaskiya yayi yawa karya zamo kamar ina cutanka-”
    Katse ta yayi “kinga da wannan halin bara mu shirya dake ba ko million na yanka miki albashi ba ruwanki bana san shisshigi ki tsaya a inda Allah ya tsaida ke clear?”
   Miyau ta had’e “yes sir I’m sorry. Nagode.”
   Hannu ya d’aga da alaman a’a. “Ba’a min godiya. Inada rules sosai in zakiyi aiki a k’ark’ashi na which I have to tell you dan ki kiyaye. Na farko kamar how I told you duk lokacin da nakeda buk’atan shan coffee zan kiraki and zaki bar duk wani abinda kikeyi kizo ki had’a min, clear?”
   Kai ta giad'a “Yes.”
    “Good, na biyu banasan shisshigi duk abinda kika gani inba wai nace kiyi magana bane baruwanki aikinki making coffee ne kawai, clear?”
   Nanma ta giad’a kai “yes.”
   “Na uku banasan yawan kallo, aiki kikazo yi ba kallo na ba. Ki kiyaye, clear?”
     Fannah ji take kamar ta k’urma ihu wai mesa wannan Anas yake haka ne? “Clear?” Ya sake tambayanta.
   “Yy..yes sir.” Ta amsa sa.
    “Na hud’u ba late coming ko minti d’aya karki k’ara kan time danake buk’atar zuwanki and last but not the least obey all my rules. Nakega for now wannan sun isheki.”

      “In shaa Allah sir zan kiyaye duka rules naka thank you.”
        “Kin karya d’aya ready banasan godiya.”
          “I’m sorry.”
      “You better be” yace ba tare da ya kalleta ba,  duban cikin wasu files dake kan table nasa yake “gobe zaki fara aiki.” Bayan ‘yan mintuna ya d’ago fuskarsa yaga Fannah zaune kan kujerar har yanzu tana wasa da yatsunta. “Well? Me kikeyi har yanzu? You’re dismissed ko komai ne se an riga fad’a miki sekace karatu?”
    “I’m sorry” tace. So take ta tambayesa alfarma amman kuma tana tsoro kar yace tacika tak’uri da rashin godiya.

    A hankali ta mik’e har takai bak’in k’ofa sekuma ta kasa fita tasan inba Anas ba bata da wanda zata nema alfarma gunsa ya bata a yanzu, dubu goma take nema ta gama biyan kud’in asibitin Baba. A hankali ta juyo ta k’arisa gaban table nasa ta tsaya ba tare da tace komi ba dan bata san ma ta ina zata fara ba. Sarai yaji tsayunwanta kansa amman yak’i d’aga kai se files dake gabansa yake ta dubawa can da kallon da take masa ya ishesa ya d’ago kyakkyawar fuskarsa tare da kafa blue eyes nasa kanta. Take ta sadda kanta k’asa. “I thought na fad’a miki banasan ana kallonna haka ko?”
      “Kayi hak’uri” ta fad’a a takaice ba tare data d’ago kai ba.
    “So me kike min tsaye akai? Ko bodyguard kikeson na baki? Nace you’re dismissed zaki iya tafiya.”

      “Mr. Fauzi dan Allah kayi hak’uri nasan banida right da zan tambayeka wannan alfarma amman kayi hak’uri please ina buk’atan kud’in ne sosai.”

       Kallonta yake cike da mamaki. Papers na gaban nasa ya rufe tare da had’e hannunsa biyu k’ark’ashin hab’ansa yana kallonta. “What are you saying? Zo ki zauna” yayi gesturing nata. Bayan ta zauna ta soma kamar haka;
 
      “Mr. Fauzi mahaifina ne baida lafiya nagama biyan kud’in magunan sa sauran 10k sekuma na rasa aikina yau kusan sati kenan ‘yan asibitin sunce in ban biya ba zasu iya sueing d’ina court. Please taimakon ka nakeso.”

       Kallonta yake amman sede wannan karan kallon bana tsiya da rashin mutunci kamar yadda ya saba ba. Duk banzan hali irin na Anas when it comes to family ne yanada tausayi sosai. “Me zan miki kenan?” Ya tambayeta a hankali sekace bashi ba. Ita kanta mamaki question nasa ya bata dakuma yadda yayi tambayar. Kai ta d’ago tana kallonsa cike da mamaki samnan ta kau da kanta.

      “Acikin salary na nakeso kayi deducting dubu shabiyar kabani please, in shaa Allah zan maka aiki me kyau ba fashi that I can assure you.”
     Kai ya giad’a a hankali. Drawer’n gefen damansa ya ciro bundle na d’ari bibbiyu da d’ari biyar-biyar ne ciki na d’ari biyu ya ciro tare da rufowa. A gabanta ya ajiye. Ido ta zaro “sir-”
  Nan ya katse ta “take it, kije ki biya kud’in asibitin mahaifinki dashi Allah bashi lafiya.”
     “Sir thank you so much but dubu shabiyar ma ya isheni banason in k’arasar da kud’in duka kafin wani watan.”
 
     “Ba baki nayi dan in cire daga salary’nki ba nabaki ne a matsayin taimako so you can go now.”
     Mamaki ne yacika Fannah tama rasa ta ina zata soma masa godiya.
     “Jazakallahu khairan Mr. Fauzi nagode sosai.” Kai kawai ya giad’a mata dukda kuwa baisan godiyanta. Ta tashi zata tafi ya tsaida ta “before you go inasan ki had’a min coffee.”
     “Okay sir amman-”
Katse ta yayi “just shut up!” Ya daka mata tsawa. Har tsakiyan kanta tajiyo wannan tsawa wai ace yanzu mutum yagama magana da hankali kuma seya soma masifa. Tana kallonsa ya kira wani a waya bayan ‘yan mintuna wani d’an saurayi yashigo. “Yes Boss.”
   “Uhm Yusuf ka kai ta kitchen ka jirata ta had’a min coffeen seka kawo min kekuma daga can sekiyi tafiyan ki bainda number’nki by 4:50PM ki kirani saboda inyi saving.”

     “Okay Mr. Fauzi in shaa Allah zan kiraka.”
     “Allah sa dan in kika manta kika kirani before or after the time a bakin aikin ki. Off you go” nan suka fice tare da Yusuf zuwa kitchen.

 


   *© miemiebee*

No comments: