Saturday, 3 September 2016

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 52
BY MIEMIEBEE


English wears had’ad’d’u na ‘yan gayu maras tsireci ta siya wa kanta sannan wani had’ad’de wa Aiman itama bata damu da Fannah ba saboda tasan bara’a rasa d’aya cikin kayakin da Anas ya siya mata ba.

    _2 days later..._
   _Monday 3:30PM_

     Kaya ne wargaje cikin d’akinsu Fannah, su Afrah ana shirin zuwa party. Ba hassada tayi kyau, kayan ya mata kyau makeup nata yayi kyau, kamar yadda ta tsara kanta haka ta tsara Aiman ma dukansu biyu sunyi kyau banda Fannah dake zaune kan gado tana buga candy crush da towel d’aure a k’irjinta.
   “Wai Ya Fannah bara kije bane? Dubi time fa! Ga kayanki nan tun d’azu na cire miki kink’i sawa.” Cewar Afrah
     “Barin jeba in kun had’u kice masa banida lafiya.” Daidai da shigowar Mami kenan “waye ne baida lafiyan?”

    “Mami wallahi gatanan tak’i tashi ta shirya.”
  “Mami wallahi k’arya take, yanzu fitowa na daga wanka ko Aiman? Ina kayan nawa insa. Wane ni ace birthday na in-law na barinje ba.† Kallonta Afrah ke cike da mamaki. Kayan ta jawo ta zira wata maroon doguwar riga ne har k’asa me hannun vest da kwalya sosai a jikinsa ta saman, bayan tasa shi ta d’auko wata had’ad’d’iyar ash-ash jacket me siririyar dogon hannu dake shek’i ga kwalyan stones daya sha, yana nan da tsayi shima har kusan k’asa amman be gama kaiwa ba, ta d’aura akai. A bud’e yake saboda ya bayyano da kwalyan dake d’auke da doguwar rigar dake cikin. Afrah ce tamata makeup d’in basu d’au lokaci ba saboda ba wai gira za’a zana mata ba. Maroon gyale tayi rolling dashi seda ash jaka da takalmi data sa. Feffeshewa sukayi da turare 4:00PM on the dot driver’n yamata waya kan gashi nan.

   Allah kare Mami ta musu suka fice. Daidai gaban gidansu Anas ya tsaya bayan an bud’e gate ya shiga dasu. An k’ayata filin tsakar gidan da had’ad’d’en decoration na red and white, tsayuwa dan kwatanta kyan wajen ma b’ata lokaci ne. Bayan sun fiffito daga motar suka tsaya chak Afrah da Aiman kam se k’are wa gidan nasu Anas kallo suke bada jimawa ba gate ya bud’u motan Shettima ya  bayyana. Yana ganin Fannah yaji wani dad’i ko lura dasu Afrah beyi ba seda ya fito suka gaisa da Fannah sannan idanunsa suka sauk’a kan Afrah (fire) kasa dena kallonta yayi dan had’ewar data masa, ashe ba Ya Anas kad’ai keda rabo ba harda nima ya fad’a a ransa.
    “Ina wuni?” ta gaishe sa.
   “Lafiya sannu ko? Fannah kuna kama ko sister kice?”
   “Eh sunanta Afrah wancan kuma Aiman.”
   “Wow pretty ladies sede ma Afrah duk tafi ku kyau.”
    “Noi! Wani kyau tafimu? Kwalya de ta fimu, nida Aiman duk munfita kyau.”
   “A ganinki kenan nide Afrah tafi min kyau.” Afrah kam se blushing take, wani me kama da Blue eyes yace mata tanada kyau.

       “Fannah kushiga daga ciki su Ummie suna parlour you all are welcome.† Duk wannan magana dayake yakasa d’aga idanunsa daga kan Afrah.
   “Tam, taho muje Aiman, Afrah lets go.”
    “A’a ni dakaina zan kai Afrah koban fad’a miki tafi ku kyau duka bane.” A hankali ta d’ago idanunta da suka sha tozali da liner ta azasu kan Shettima dake d’auke da murmushin dayake k’ara masa kyau, murmushin ta mayar masa, “lets go ko? My lady.,By the way I’m Shettima, k’anin Ya Anas amman fa karki d’au wani babban bro na ne, dududu shekara d’aya da rabi yabani.”
   Murmushi sosai Afrah ke harda ‘yan hakwara a waje.

    “Nima ai, 1½ years ne kawai tsakani na da Ya Fannah.”
   “Owww really? Zo mud’an fita kafin programme d’in ya fara.” Motarsa ya bud’e mata tashiga se rawan jiki yake yasamu ‘yar kyakkyawa. A ice cream shop ya tsaya suka sauk’a, kud’in Ya Anas zeyi amfani.
      Bayan an kawo musu ice cream d’in suka soma sha a hankali. Cikin d’an k’ank’anin lokaci suka saba sosai, dake halayensu na neman tsokana da neman zance duk d’aya ne, labarin abubuwan da suke ma yayunsu suka rigayi, bayan sun gama chan suka tab’o b’angaren karatu Shettima harda zuzutawa wai yana d’an business. Afrah ta jima tana nan perfect boyfriend segashi tasamu kyakkyawa k’anin billonaire. Ba b’ata lokaci Shettima ya fad’a mata santa yake, tunda idanunsa suka sauk’a kan kyakkyawar fuskarta yaji yana sonta. Aiko itama ma hakan ne, take sukayi exchanging I love you da I love you too. Bayan sun k’are shan ice cream d’in yakaita shopping duk acikin kud’in daya sata gun Anas ranan.

    Afrah kam dad’i kasheni.

     ****
   Fannah kuwa tun shigarsu gidan bata had’u da Anas ba taji Ummie na cewa baya gida ma, Abuu kuwa yayi tafiya, hamdala ta saki. Birthday girl ansha kyau sosai tana ganin Aiman taji tana san miyar da ita little sister tunda ita batada. Bada dad’ewa ba programme ya fara har a yanzu su Shettima masu soyayya basu dawo ba. Bada dad’ewa ba gate ya bud’u had’ad’d’iyar benz na Anas ya shigo. Bayan yayi parking yafito ko kallon direction na mutanen baiyi wajen Amal nasa ya nufa yayi wishing nata happy birthday tare da ajiye mata present nata na iphone 6+. Direct parlour ya nufa bayan yasha ruwa ya ciro wayarsa ya kira Fannah yaji ko sunzo. Tana zaune abinta taga call na Anas. Me kuma zece mata yanzu? Da k’yar ta d’aga “hello?”
  “Kunzo?” Ya tambayeta a takaice
“Eh.” ta amsa sa.
   “Ina kike? Kizo parlour yanzu ina jiranki” karap ya katse. Inje kamin me ta tambayi kanta kamar wacce barata ba, sekuma ta mik’e taje zaune kan dining chair ta samesa ya aza k’afafunsa kan table d’in yana kad’awa da wayarsa rik’e hannunsa. Sosai shirin dayayi ya masa kyau kodan bata tab’a ganinsa da erin shirin bane?
   Shima kallon nata yake, gani yake kamar bata tab’a kyau erin na yau ba, kodan be tab’a ganinta cikin english wears bane? Kasa dena kallonta yayi, da k’yar ya iya cemata “zoki zauna” tare da ja mata kujeran gefensa.
    A sanyaye tanufa wajen sede bata zaunan ba gudun kar Ummie tazo ta kamasu bibbiyu.

     “Mr. Fauzi you called for me, wani abu ne? Kaga I need to get back.”
   “Sit toh.”,Yi tayi kamar bata ji saba. Hannunta ya rik’o “sit first.” Dan kawai ya sake mata hannu ne ta zauna. Bayam daya k’are mata kallo kusan na mintuna biyu yace, “kinyi kyau.” ‘Yar murmushi ta saki, “thank you.” Dad’inta kenan da Anas duk sanda tayi kyau ze fad’a mata. Cameran wayarsa ya shiga yayi muting, yasoma d’aukanta hoto seyi yake kamar amfani da wayar yake.

    “About business trip da zanje Morocco ne, nafasa zuwa dake tunda you are now my girlfriend, zamuje da Kacallah.” Dad’i sosai taji.
   “Okay Sir.”
   “Call me Anas.”
   “Okay Anas shikenan zan iya tafiya?” Besan meh ba seyaji bayason ta tafi yafison ya kasance tare da ita always.
   “Jibi ne tafiyan nayi rescheduling.”
   Nanma “okay” tace. So barata ce masa ko safe trip ko Allah kare ba wato.
    “What kind of an I don’t care girlfriend are you? I’ll be travelling ko d’an safe trip babu.”
   “Toh Sir nag-”,sekuma tayi shiru ganin battada abin cewa “I’m sorry, safe trip Allah ya kare ya dawo dakai lafiya.” Chan k’asa k’asa yace, “ameen seda na tambaya.” Ita Fannah bata aza abin boyfriend girlfriend nasun a ka ba saboda batasan ta sake bud’e zuciyarta ma wani na miji because a k’arshen ita zata wahala danko duk na mijin daya gano some day batada budurci ze guje ta, abinda bataso kenan, maganin bari kar ma a soma.

   “Zan tafi.”,Tace a hankali.
  “No I want you to stay Fannah don’t go.” Har a yanzu bebar d’aukanta hoton dayake tayi ba haka yak’i  barinta ta tafi, kuma bawai hira yake janta dashi ba kallonta kawai yake yana d’aukanta hoto. Da kallon ya isheta tace, “Sir kaifa kace adena kallo dayawa.”
    “Yes amman ni ai am your boyfriend me aciki dan na kalleki? You also enjoy it when ever I’m starring at you so kidena pretending.”
    “Nima ai am your girlfriend amman dana kalleka sekace bakasan kallo, kayi adalci kenan?”
        “Miss Aleeyu kallon soyayya kikemin nikuma banaso, ni kawai kallonki nake saboda kinyi kyau.”
   
        “Toh nima ai saboda kayi kyau nake kallonka.”
         “Ni ai kullum inayin kyau, am handsome kekuma time-to-time kikeyin kyau.” Ganin inta sake magana ze iya zaginta tayi shiru kawai bata sake cewa komai ba k’arfe 5:30PM nayi ta mik’e “Sir zamu tafi kar Maghrib ya mana anan.” Hannun ta ya rik’o “I will take you guys home.”
     “No please karka damu we can go on our own.”
    “Fannah I’m your boyfriend I insist.”
    “Toh Mr. Fauzi kasakemin hannu please.”

   “No Fannah, I enjoy holding your hand, allow me.”
   “Sir ba kyau ne.” Kafin yace wani abu ta b’arke masa da kuka, shark’af shark’af besan lokacin da ya ciro hanky ya soma share mata hawayen nata ba. “Fannah why are you crying? Na miki wani abu ne? Kodan danace time-to-time kikeyin kyau? I don’t mean it kinji? You are beautiful, always looking gorgeous saisa nake kallonki kullum. Bar kukan kinji?”  Har yanzun be sake mata hannun ba duk yabi ya kid’ime ganin yadda take kuka. Baya san ganin ta tana kuka bayyaso ko kad’an.

      “Niba wancan ba” ta ce tana kukan still.
Sosai taji dad’i daya yaba kyanta haka. “Toh meneh Fannah? Stop crying please”
      “Anas ba kyau, akace da namiji ya tab’a jikin macen daba muharramarsa ba gomma yatab’a garwashi, azabansa kuwa yafi ad’au k’usa a buga masa a kai har se ya nitse. Anas banason amaka wannan azaba, banaso please kadena rik’e min hannu gomma ace ma muna da aure ne kake rik’emin hannun I wouldn’t mind amman a yanzu haka haramun ne, kadena kaji? Banason amaka wannan azaba, please.” ta k’are maganar tana hawaye. Shiru yayi chan yace a hankali “shine dalilin da kike kuka?”

   Kai ta giad’a masa a hankali har yanzu bata bar kukan ba. Hannunta ya sake a hankali “toh ya isa daga yau barin sake rik’e miki hannu ba kinji? Stop crying.” Da murmushi a fuskarta ta d’ago kai tana kallonsa “promise?”
   Kai ya giad’a mata.
    “Bani kad’ai ba kowace mace baraka sake rik’e mata hannu ba?”
    Nanma kai ya giad’a, “what of Amal? Har itama?” Ya tambayeta.
    “Amal muharramar kace zaka iya rik’e mata hannu da ita da Ummie amman banda matan waje.”
   “Okay...” ya fad’a yana giad’a kai. “Cry nomore kinji? Barin k’ara ba”
    Tana murmushi ta giad’a masa kai “I won’t ever. Thank you Anas lets go?”
  “Yes lets go.” Yayi assuring nata, da a dana ne hannunta cikin nasa zasu fice amman banda yanzu. Side-by-side kawai suke tafiyar. Bayan sunfito suka sami Afrah da Shettima zaune kan wata doguwar kujera sun baje se hira suke suna dariya kamar wanda suka jima da sanin junansu.

      “A ina suka saba?” Anas da Fannah suka tambayi juna a tare.
   “Nima bansani ba” suka sake amsar junansu a tare. Murmushi kad’an suka saki. “Shettima fa baida matsala ina shi ina Afrah?” ya tambaya cike da mamaki.
   “No let them be please karka mishi magana.” Cewar Fannah cikin salon da dazaran tama Anas magana dashi yake amincewa da k’udurinta.
  “Fannah amman kina ganin is okay?”
   “Yes don’t bother, lets go.” Bayan ta ajiye wa Amal birthday present nata taja hannun Aiman, ai atapir Amal tace se Aiman ta kwana mata, ita a dole tasamu sister. Da k’yar ta amince tabar Aiman ta tafi bayan ta kwashe mata kusan rabin birthday present nata tabata.
    “Toh Afrah seki tashi ai mutafi ko? Soyayyar ya isa.” cewar Fannah. Murmushin jin dad’i Shettima ya saki a yayinda kunya ya ratsa Afrah musamman ma dataga Ya Anas gefen Ya Fannah yana kallonsu.
 
    “A’a kuje ni zan kaita.” Cewar Shettima. Anas zeyi magana Fannah ta dakatar dashi “lets go ze kawo ta yace.” Badan Anas naso ba yabi Fannah suka fice.

*kuyi min uzuri please da rashin posting da nakeyi kwana biyu, somethings came up*

*© miemiebee*

No comments: