Saturday, 3 September 2016

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 38
BY MIEMIEBEE


Washegari tun asuba Anas ya tashi saboda kasa bacci da yayi ga kuma rashin abin shaye shayen sa kusa dashi, koda na kusa dashin ma se yayi drama yake iya sha yanzu tun maganan da Fannah ta masa har yau yakasa erasing daga memory’nsa. Bayan yayi wanka ya shirya yafito already Ummie da Amal sun had’a masa breakfast, as usual shida Amal suka karya sede yau Anas ya zage yaci abincin sosai sab’anin yadda ya sabayi danko in be sha coffeen Fannah ba bai iya breakfast me kyau. Se forcing kanshi yake yana ci shi a dole yanasan mancewa da coffeen, a tunanin sa in ya dena shan coffeen ta ze iya mancewa dashi, eventually Fannan ma ze manta da ita seta zama missed call. (LOL)

    “Wai! wai! wai! Ya Anas ai ka cinye abincin bani yau.”
     Murmushi ya mata tare da rufa bakinsa ta hanyan aza hannunsa kai. “I’m sorry Angel yunwa nakeji. Nikam kunyi waya da Fannan office d’ina jiya?” Shiru tayi bata amsa saba gudun karya masifeta. “Angel I’m talking to you.”
     “Ya Anas kayi hak’uri.”
    “For? Amsa min tambayan dana miki mana kunyi waya jiya?” Kai ta giad’a a hankali cike da tsoro saboda Anas ya hanata waya da Fannah.
    “Meh tace miki?” Nan ma shiru tayi.    “Feel free and tell me barin miki komai ba kinji?” Ya d’ago hannunta yasa cikin nasa.
     “Promise Ya Anas baraka sake hana ni waya da ita ba?”
     “Yes Angel I promise.”
     “Tacemun batada lafiya mentral cramp yana damunta.”
     “Tace zata office yau?”
       “Tace min baza ta ba wai seta warke gabad’aya.”
    Kai ya giad’a tare da kewayo da kallonsa daga kan Amal zuwa kan plate na abincinsun “in ta haka menstral cramp d’in da wahala kenan.” Ya fad’i wa kansa kasancewar Amal na kusa dashi seta jiyo sa. “Sosai Ya Anas ni in ya tashi min ji nake kaman zan mutu.”
     Murmushi ya mata “bara ki mutu ba ma in shaa Allah barin wuce office kinji?” Kai ta giad’a masa a yayinda ya bata peck a goshi. “Ummie thank you for the breakfast na tafi” yache da d’an ihu dan Ummin dake kitchen ta jiyosa. “Adawo lafiya Babana” ta mayar masa itama da ihun.

    As usual k’arfe 8:00AM yayi masa a office nasa, Kacallah ya kira ya tambayesa ko yanada meeting yau. Unfortunately Kacallah yace masa ai duk wani schedule nasa na wajen Fannah. “Toh mesa ka bata duka?”
    “I’m sorry Boss but she is your PA, aikinta ne yanzu.”
    “Toh naji” yayu hanging.

  *****

     “Mami ni wallahi barinje office d’inba, barin sake komawa bama gabad’aya. Bakiji me Afrah tace masa jiya bane? Che masa tayi wai MP ke damuna.”
    Baki Mami ta bud’e tana kallon ikon Allah. “Lallai fa Fannah se akayi ya? Abune kowace mace tanayi, basuda mata ne a gidansu? Shi kansa ya riga yasan mene, ni banga abin jin kunya ba a nan ba.”
    Can k’asa k’asa Fannah tace, “ai dama baraki gani ba.”
    “Nima de wallahi Mami” cewar Afrah.
    “Kekuma Afrah kika kuma wannan rashin hankali zan sab’a miki, Aiman ce yakamata tayi wannan sokanci ba ke ba.” Mami tayi lecturing nata. Juyawa Fannah tayi tana mata gwalo a dole an mata masifa itama.
    “Ke kuma Fannah sa hijabinki ki fice kinga already kin makara kuma Anas baya san latti.”
   “Kar yason” tace a k’asa k’asa.
     “Maza- maza! Tashi ki fice Fannah kar muyi fad’a dake da safiyan nan ko inje in sanar da Babanku ne?”
     “Allah sarki Mami dan Allah mana, gobe zanje I promise.”
   “Wannan kuma ke ya dama Afrah taho muje ki tayani shirya kayakin Aiman.” Da gwalon da Afrah ta ma Fannah tasa kai tabi Mami suka fice. Se zumbure zumbure Fannah take ita jiya da bata sa Mr. Fauzi a ido ba, ta wuni lafiya ba tashin hankali amman tasan definately suka had’u yau seya sata kuka, ita da ana shan maganin hana zuban hawaye da tasha. Ganin ba mahallici se Allah yasa kawai taja blue hijabinta me torches fari tasa, ta d’au jakarta ta sak’ala tare da cikasa da duk wani abinda zata buk’ata sannan ta fice ko sallama batayi dasu

    Ba ita ta isa office ba 8:34AM. Tana tsaye gaban office na Mr. Fauzi amman ta kasa shiga seta d’aga hannu zatayi knocking setaji kunya, yanzu yau wani irin kallo ze na mata? “Mschww Afrah ba kiyi ba wallahi” ta sake nanatawa for the hundredth time a zuciyarta. Ai haka ta kasa shiga office nasan, daga k’arshe nata ta zarce kawai taje ta had’a masa schedule (kamar time table haka) na ranan, tayi arranging komi, meeting d’aya yake dashi se mutanen da zasu zo ganinsa na signing contract guda biyu, sekuma na siyan shares na Global investments. Tagama ta ajiye a gefe guda chan ta ciro wayarta tana game itade yau barata had’a ido da Mr. Fauzi ba sekace wanda tayi sata.



      *****

     Anas kuwa yakasa tsinana wa kansa komai banda tunanin Fannah wai anya yau inbe sata a ido ba ze iya kwanciya lafiya kuwa? “Oh No! No! No! Why am I acting in this way? Coffee nake missing ba Fannah ba, coffee ne” ya tunar wa kansa. Ai daga k’arshe kasa hak’ura yayi ya tashi ya nufi office na Fannah koda bare ganta ba yau yaga office nata he is okay with it. Fannah na cikin game taji an murd’a hannun k’ofar office nata ido tasa wa k’ofan jiran ganin ko waye dukda kuwa zuciyar ta na sak’a mata wai Yusuf ne.

         Wayar ta tayi wulli dashi da suka had’a ido hud’u da Anas dama dalilin dayasa ta sako hijabi me hula kenan yau, da sauri sauri taja ta rufe fuskarta. Yin hakan seta tuna masa da incident na jiya seya gano dalilin dayasa take rufe fuskar kunyan sa takeji dan Afrah tace masa MP ke damunta, shi kansa kunyan ta yakeji bama batun MP’nta ba. In kuma tace meya kawo sa office nata fah? Karkuma tagane dan yana missing nata ne yashigo ta raina sa. Ganin batada niyyan magana yasa yayi giaran muryar. “So kinzo shine baki sanar dani ba? Nazo picking wani file ne dama” yayi k’arya yana wani basarwa.
     Da k’yar ta iya bud’e baki ta gaishe sa. “Good morning, wani file ne?” ta tambaye sa cikin siririyar muryarta.

          Rashin sanin wani k’aryan ze sake mata kawai yace, “to my office” chike da isa. Yana fita ta d’ago kai “to my office” ta kwaikwaye sa sannan tad’au jakarta da jotter’nta da pen da pencil tabi bayansa. Bayan like minti d’aya da shigan Anas office nasa Fannah tashigo itama kanta sunkuye a k’asa daidai gaban table nasa ta tsaya tare da mik’a masa jotter’n gabansa “here is your schedule for today, inda akoi abinda za’a giara let me know” D’agawa yayi ya dudduba yaga komai yayi, yaga ta ma fi Kacallah iya amfani da lokaci dan kuwa by 2:30PM ya gama komai nasa yau.

     So yake ya tambayeta ya jiki amman kuma girman kai irin nasa bare barsa ba seya bud’a baki zeyi magana se wani abu ya katse sa. Itako tana nan tsaye kansa har yanzu tana jiran amsar sa in da akoi abinda be masa ba yafad’i seta giara. Can k’asa k’asa almost kamar da kansa ma yake magana yace, “ya jikin ki?”
     Fannah kuwa taji sa amman dan yadda mamaki yaso kasheta se kawai tace hala kunnenta ke mata k’arya yaushe Mr. Fauzi ze tambayeta ya jiki? Karkuma tayi shiru yace ta rai na sa yasoma balbaleta yanzu a nan, dan haka tace, “eh? Excuse me” fuskar nan a rufe da hijabi har yanzu.

      “Ya jikin ki nace” yasake nanatawa with thesame voice level dayayi d’azu.   Se yanxu ta tabbata ba yaudarar ta kunnenta suke ba. “Da sauk’i” ta amsa a hankali duk seji take kamar ta nitse  k’asa dan kunya. Da k’yar tayi managing tace, “thank you.”
     “Bana buk’atar godiyar ki” ya fad’i mata gatsau sekace bashi yanzu yayi magana a hankali ba. Itafa har yau ta kasa gane hali irin na Mr. Fauzi yanzu yanzu seya mata mutunci take wajen kuma ya zagesa yadda yaga dama. Juyawa tayi ta nufa wajen coffee machine dan had’a masa ai bata soma ciro cup d’in ba ya jefa mata tambaya. “Me kuma zakiyi acan?”
    “Had’a maka coffee sir.”
    “Banaso, bana buk’ata just kitafi kije office naki if am in need of anything I will let you know.”
     Wai yau Mr. Fauzi ne ke fad’in baya buk’atan coffee to kode wanda ta had’a masa jiya beyi dad’i bane kasancewar zogin da hannunta yake mata. Shi kansa be zata ze iya fad’in baya buk’atar coffeen ta ba se gashi ya fad’a confidently ma kuwa.

        “Sir indan na jiya beyi dad’i bane I apologise hannu na ke ciwo, will make it better yanzu.”
    “Banaso nace just get out kuma na hanaki ja min wannan hijabin kina rufe fuskarki dashi, me kike dashi da banida? Ja hijabin baya.” Dakewa tayi tak’i ja seda ya daka mata tsawa “ja nace!” Tana b’ari ta giara “now leave” a sanyaye ta juya ta fice tana isa office nata ta zauna kan cushion.
    “Mschww wallahi Mr. Fauzin nan kanada mental illness, yanzu kama mutum mutunci da ‘yan mintuna kuma ka koresa kaman kashi thank god kai kazo har nan ka kirani bani na kai kaina office nakan ba. Wallahi kawai dan na danne zuciyata ne da nayi kuka, sede kata wa mutane masifa kai aikin ka kenan, Allah shirya wallahi ina tausaya wa matar da zata aure ka” (ni miemie nace kina tausaya wa kanki kenan) “ace kullum masifa, masifa. Ni barin cigaba da yin game d’ina ma.” Wayarta ta ciro tacigaba da buga candy crush.

      Kusan to 12:30PM Anas ya danna mata kira ta telephone kan ta shirya zasu meeting. Yau akeyinta ita gaskia bata shirya zuwa meeting ba amman ya ta iya? Bayi ta nufa tayi changing sannan tafito tak’i shiga office nasan ma bale ya mata korin kare kona akuyan daya saba mata. Bayan like 5 minutes Anas ya fito taga ya canza shirinsa yasa navy blue suit, white shirt da ocean blue tie sosai kam yayi kyau ga yadda gashinsa yasha giara kafin ya kamata tana kallonsa tayi saurin kau da kai, bece mata komi ba koda yaganta tsaye bakin office nasan juyawa yayi ya soma tafiya a yayinda take binsa a baya. Driver ne ya tuk’asu har hall da za’ayi meeting d’in sun iso da shiga ya juya ya kalleta “sauran yau ma kiyi tsaki kokuma ki baje kina bacci kinji ba Miss Aleeyu?”
      “Naji” tace ba tare da ta kallesa ba. Kamar ranan yana shiga mutanen suka tashi masa bayan sun gama gaggaisa wa ya zauna a kujerar tsakiyan nufin shine babba ma a meeting na yau kenan.
 
      Duk abinda ke gudana Fannah ta kasa kunne tana sauraro tare da jotting down major points kuma, gajiya tayi da tsayuwan ta zauna still hankalinta na kan meeting d’in. Time to time Anas yake d’ago kai yana kallonta sam idanunsu basu had’u ba.

     Se 2:30PM suka k’are boring meeting d’in, indagin Fannah yayi tsami dan zama bayan sun shiga mota ya tambayeta, “ina abubuwan da kikayi jotting?” Cikin jakarta tasa hannu ta ciro jotter’ta tare da mik’a masa. Se kuwa yaga duk important abubuwan da sukayi discussing akai na had’a kan Flames Enterprises da C&C Enterprises duk tayi jotting down  da kuma abubuwan da zasu amfanar da juna dashi, sosai kuma yaji dad’i. Amman meya kamata yayi wa Fannah? Godiya koba haka ba? But saboda dan girman kai irin nasa ya kasa, “nan gaba in ana meeting seki dena frwoning fuskarki ai kowa yasan meeting d’in ba dad’i gashi ki ajiye zan buk’ata anjima.” abin da yace da ita kenan.
      Sanyi taji sosai a ranta da beyi complaining akai ba amman kuma yak’i mata godiya dan uban girman kai. Sede abin da ta lura yau shine besa an k’ure AC kamar na ranan ba, kad’an kawai yasa driver ya kunna. Shikuwa Anas yayi hakan ne saboda batada lafiya, bayasan ya k’ara mata wani rashin lafiyar akan wanda take fama dashi, tunda ya karanci bame san sanyi che itaba. Yauma daidai gaban wata makekiyar hotel driver ya tsaya tare da bud’e masu k’ofa. Bayan sa tabi a hankali har suka shiga ciki, ba kowa daga su se masu aiki. A ranta tace wato kai baka iya cin abinci se kayi reserving, lallai kud’i ya maka yawa. A table daya zauna ta zauna itama, ko da waiter yazo d’aukan order’nsu Anas ne yamasa bayanin komi ita batace ko uffan ba ,wasa da siraran yatsunata kawai take tana kallon yankan da tayi shekaran jiya a yayinda Anas ke latse laste kan wayar sa. Bayan 3 minutes abincin su ya iso sede taga combination na yau yafi na ranan yawa, ba abinda babu kan plate nata k’wai ne kaza ne, kayan ciki na, pepper soup ne bade abinda babu shiko Anas kalan abincin ranan ya sake ordering.

      Toh mesa? Mesa za’a bani wannan babban plate cike da abincin kusan dubu biyar? Na Mr. Fauzi kuma na N1,500? Kode waiter’n yayi b’atan kai ne? “Uhm Sir are you sure wannan shine abincin nawa?” Ta tambayi waiter’n a yayinda yake zuba mata drink.
     “Yes Miss your Boss asked me to bring it for you.”
    “Boss?” Ta nanata a ranta tare da juyawa ta kalli Anas. Sam yi yayi kamar bema san maganar da sukeyi ba yakai spoon bakinsa a hankali. Bayan waiter’n ya tafi still Fannah ta kasa tab’a abincin ta dan bata yarda ba har yanzu.

     Anas kuwa dalilin dayasa ya sai mata abincin dubu biyar yau shine akoi time da ya tab’a kai Amal asibiti da menstral cramp ya tab’a rik’eta bayan da likita ya dubata ya bata maguna seyake cewa Anas a tabbata tana cin abinci me kyau saboda asaran jinin jikinta da take in tana period same goes to Fannah, sesu samu suyi restoring energy’n jikinsu. Itama saboda bleeding da takeyi yazamo dole taci abinci me kyau dan lafiyarta sesa ya siyo mata wannan abinci me kyau kuma me tsada.

   Ganin batada niyyan chi yasa ya dakata tare da kallonta, “well? Bara ki chi bane? Kinsan ba jiranki zanyi in na gama bako?”
     Baki na rawa tace, “S... Sir yayi yawa. In kace ni zan biya bansan ya zan biya ba.”
   Kallo ya watsa mata “last time da mukazo ke kika biya? Kin cika surutu, mschw. In zakici fine in bara ki chi bama fine” ya cigaba da chin abincinsa. K’in ci tayi wane ita abincin dubu biyar. Miss Aleeyu eat! Ko sena sab’a miki zakici? Ko kici kokuma in muka koma office inciro miki 500 papers kiyi zaman giaransu”
    Ai a hankali ta d’aga spoon nata ta soma ci a hankali, ta tab’a nan ta tab’a can sosai abincin ya mata dad’i. Bata san lokacin data baje ta fara ci kamar ba gobe ba Anas dake satan kallonta se mamaki yake mutum gata ba k’iba amman se aukin chi. Duk uban girman plate nata sanda taci morethan half, data jita dam tukuna ta goge bakinta ta kora da juice. Kallonta yake cike da mamaki har yasa ta jin kunya.
     “Kin k’oshi ko a k’ara?” Kai ta kad’a masa cike da kunya da nufin a’a. Waiter yakira ya biya kud’in plates nasu sannan suka kama hanyan dawowa office.

   *© miemiebee*

No comments: