Saturday, 3 September 2016

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 24
BY MIEMIEBEE


Haka ta ta zama shiru game dayake sata nishad’in ma Boss nata ya hana ta yi. Time-to-time take satan kallonsa dan ba k'arya model dake gabansan ya bala’in mata kyau. Kafin lokacin tashin su yayi as usual ta had’a masa coffee cikin flask takai masa har mota.

          Isan Anas gida keda wuya ya wuce d’akinsa thank god Amal bata nan sunfita da Ummie da ta cika masa kunne da surutu bayan ya watsa ruwa ya  sha coffeen sa sannan ya kwanta.

   _Bawan Allah ka cuceni, ka rabani da budurcita martaba ta, ka cuceni barin tab’a yafe maka ba. Kuma ina nan kusa da kai INA TARE DA KAI..._

     Firgit Anas ya tashi daga mafarkin dayake yana nishi sosai, ga wani uban zufan dake k’eto masa. Hannunsa bibbiyu yasa cikin gashin kansa yana hargitsawa daidai lokacin knock yazo daga k’ofar d’akin. “Waye ne?” ya tambaya. “Shettima ne in shigo?”
“Eh” ya amsa a kasalance. Shettima na ganinsa ya gane mafarki yayi wajen dispenser ya nufa ya d’ibo ruwa ya kai masa bayan Anas yad’an sha ya masa godiya.
      “Mafarkin wa kayi kuma? Ummimi?”
     Kai Anas ya kad’a masa. “Shettima yarinyan... *_TANA TARE DA NI_* I can feel it help me find her please. Wallahi shekaran jiya ma sanda nayi mafarkinta kuma it hurts me alot in naji tana cewa na cuce ta na rabata da budurcinta.” Kafad’arsa Shettima ya dafa “Ya Anas kai yanzu koda ka sameta me zaka mata? Kafa riga ka b’ata mata rayuwa”

     “Shettima I will seek for her forgiveness, zan nemi gafararta koda kuwa kneeling zanyi gabanta I will do it. A rayuwa inasan in karya wa mata zuk’atansu amman bawai in raba su da martabarsu ba Shettima.” Ya fad’a a hankali cike da damuwa kamar ba Mr. Fauzi da muka sani ba.
    “Toh Ya Anas what if tace bara ta yafe maka bafah? Tace sede ka aureta ofcourse kasan kowace mace zata so kasancewa matarka.”
     “I will do it Shettima inhar aurenta zesa ta yafemin zanyi, baraka gane yadda abin ke damuna ba.” Sosai Shettima yasha mamakin jin kalman ‘aure’ fitowa daga bakin Anas gaskia Anas yayi regreting abinda ya aikata yakamata yarinyan ta yafe masa duk sanda suka had’u. Kwanciya yayi jikin Shettima a yayinda shikuma ya dafa hannunsa kan kafad’arsa. “Karka damu I’m sure duk rananda kuka had’u zata yafe maka, ni da kaina zan mata explaining komai.”
   “Thank you” Anas ya ce masa tare da tasowa daga jikinsa ya kishingid’a jikin gado.

     “Toh zan wuce d’akina Ya Anas please karka sha wani abu, shaye shayen nan da kake ba shi ze warkar maka da tunanin yarinyan nan ba.”
    Kai Anas ya giad’a masa danko shi yasani sarai in be sha syrup nasa kokuma giya ba damuwansa barasu gushe ba. Shettima na fita shima ya sa kaya ya wuce paint house nasa(d’an k’aramin gida) acan ya bud’o fridge ba komi bane aciki inbanda kwalban giya masu tsadan gaske d’aya ya zaro daga ciki ya nemi waje ya zauna, ya kashe wayoyinsa tukunna yadda bara ma a damesa ba. Sannan ya shanye fiye da rabi. A hankali matsolilinsa suka soma gushewa har se sanda yajisa problem free daga nan ya samu ya kwanta yayi bacci sosai daga kan kujerar ma ya gangaro k’asa ya cigaba da baccinsa se can bayan isha Anas ya tashi nan ya biya sallolinsa.

     Yayi frying omalet yaci sannan ya k’are kwalban d’azu ya koma ya kwanta. Agida kuwa hankalin kowa ya tashi gashi in sun gwada lambobinsa duk bame shiga gashi kuma ba wanda yasan da zaman paint house daya saya wanda yake zama ciki if he wants to  be alone ko Shettima ma besani ba. Shide Shettima yasan sarai yanzu wansa is somewhere yana shaye shaye abinsa. Sosai shaye shayen d’an uwansa ke damunsa shi da yasan ina ze samu yarinyan da Anas ya tab’a raping da ya nemo masa ita, atleast suka had’u hala Anas ya rage shaye shayensa.

    Ba shi ya tashi ba se washegari da misalin k’arfe 9:30AM ko sallan asuba beyi ba. A gigice ya fad’a bathroom yayi alwala yafito yayi sallah sannan ya koma yayi wanka ko breakfast beyi ba kaya kawai yasa ya d’an gyara gashin kansa ya fice. Driving yayi da sauri cikin d’an k’ank’anin lokaci ya isa office yunwam uba yakeji ko breakfast beyi ba amman bedamu ba saboda zesha coffee. As usual yana shiga aka soma bisa da gaisuwa kai kawai yake giad’a musu har ya isa bakin office nasa can yaga su Kacallah sunyi layi kafin suyi magana yayi apoligising “I’m sorry na makara ne.”
     “Ba komai Boss tunda kasamu ka fito.” Layin kap yabi da kallo be ga Fannah ba to kode dan be kirata bane yasa bata zo ba yau? Amman ai kuma jiya ma be kirata ba kuma tazo maybe ko tana wajen Yusuf.

    Bayan ya sallamesu Kacallah da k’yar ya kira Yusuf dan yunwa. Sam Yusuf yace be sa Fannah a ido ba.

    ****

          Fannah kuwa yau baccinta tasha ba ita ta tashi ba se kusan to 9:00AM dad’i takeji yau Anas be kirata ba nufin bai buk’atar ta kenan. A dad’inta yau bara a sata kuka ba dan kuwa Fannah zata iya jure wahala da walak’anci amman banda masifa daga an mata masifa take soma kuka, Anas kuwa aikinsa kenan kullum masifa. Sun gama breakfast da d’anwanke se santi suke ita da Afrah suna zaune a d’aki Aiman ta tafi makaranta. “Afrah tashi muje mu gaishe da Baba naji Mami tace ya tashi.” Atare suka shiga d’akin Baba da Mami suka samesa a kishingid’e yana kurb’an tea. “Ina kwana Baba?” Suka gaishesa a tare.
    “Lafiya emmata na, Fannah ya gajiya kuma?”
    “Ba gajiya, Baba ya jikinka?” Nan Afrah itama ma ta tambayesa.
   “Da sauk’i sosai. Fannah Allah cigaba da miki albarka ya k’ara bud’i mungode sosai.”
    “Kai Baba dan Allah godiyan me haka?”
   “Shine ai Baba” cewar Afrah “ai nima banje makarantar bane da senayi fiye da Ya Fannah.” D’an dariya Baba da Fannah sukayi, hira kad’an suka tab’a se sanda Mami ta shigo suka fice zuwa d’akinsu.

    “Ya Fannah are you sure yau bara kije office ba?”
   “Eh mana ai be kiran ba gashi har goma da mintuna aka, baya buk’atan coffee yau.”
   “Allah sa!” Afrah tace.
   “Me kike nufi?” Fannah ta tambayeta a takaice.
    Wayar ta ta mik’a mata “duba nan kiga.”
     “Innalillahi! Na mutu!” Fannah tayi exclaiming. “4 missed calls?? Yau Mr. Fauzi zeyi ferfesu na.”
    “Akan wannan pointless suratan da kike ba gomma kin kirasa ba.”

        “Afrah wallahi baran iya ba balbale ni zeyi da masifa.”
   “Oh!” Afrah ta saki numfashi
“Ya Fannah yanzu kuka kike? Ai yaci ace kin saba da masifa tun gun Baffa Khaleel. Ki kirasa.” Kai Fannah ta kad’a, fisgan wayan Afrah tayi aiko ta soma dialing number’n Mr. Fauzi. “Afrah in kinayi wa Allah ki kashe tun kafin ya shiga dan Allah, wallahi zan kirasa ki kashe dan Allah.” Ai wayar na nuna an d’aga Afrah ta wurga wa Fannah wayar tayi bakin k’ofa jiran kallon drama tana dariya.

     B’ari Fannah take ta kai wayar kunne nan ma takasa fad’in komi, kamar yadda shima Anas d’in yayi shiru ransa b’ace se tafasa yake. “Hello Mr. Fauzi.” Tayi managing ta fad’a cikin murya me rawa.
    Cike da tsiwa yake maganar. “Se yanzu kika ga damar magana? Eh?? Me kika maidani? Toy abin wasa? Wayyo!” Ya saki k’ara tare da rik’e cikinsa dan yunwa.
     “Mr. Fauzi I’m sorry dan Allah kayi hak’uri.” Ta fad'a idanta na cikowa da hawaye.
  “Meya hanaki zuwa office yau?” Ya daka mata tsawa. Kuka take kam yanzu.
   “Si..sir naga jiya danaje baka kirani ba kace na dena ma shisshigi sesa banzo ba ya-” bata k’are maganar ba ya katse ta.
   “Nonsense na baki nan da 20minutes be at my office” karap ya katse wayar. Hannu Fannah tasa tana share hawayerta a yayinda Afrah ta k’ariso ta zauna kusa da ita. “Haba mana Ya Fannah wallahi kidena masa kuka ze raina ki.”

    “Da Allah rufa min baki ba duk ke kika jawo ba, ba abin na ja miki Allah ya isa ba.”
    “Yi hak’uri Anty babba, meya ce miki?”
Harara Fannah ta galla mata “bansani ba muguwa kawai.” Nan ta mik’e ta canza kaya ta sako red hijabi tare da jan jakarta ta fice. Afrah na mata Allah kare ma ko kulata batai ba. Bata sha wahala ba tasamu keke napep sede hold ups daya rik’a rik’e su a hanya. A takaice de lattin minti 5 tayi. Duk yadda tayi tabar b’ari takasa. Se addu’o’i take ta suburbud’owa Allah kare ta daga sharrin masifan Boss nata.

    Knocking tayi bisa k’ofar “come in” yace. Bayan data shigo tagansa yana attending wasu mutane kanta ta sunkuyar tajira har se sanda ya sallamesu. Kallonta yake bema san me ze mata ba chan yace. “In nache you are fired zaki ga laifi na?” Kai ta kad’a a hankali fuskarta na kallon k’asa se b’ari take.
             Table d’in ya buga da k’arfi a tsorace ta d’ago kanta tana hawaye.
        “Ban kuma hanaki min magana da body language ba?”
       “Ka hana” ta fad’i tana share hawayenta. “Na farko yau dagangan kik’a k’i zuwa office kika bar ni da yunwa, na biyu dana kiraki har 4 missed calls baki d’aga ba saboda kin mayar da Boss naki sa’an wasanki.”
       “Kayi hak’uri dan Al-”
Katse ta yayi a tsawace “ban baki izinin magana ba so shut up!” Hawaye se gangara suke kan kumatun ta tana sharesu “na uku da kika kirani back kika k’i magana se sanda kika ga dama. Na hud’u kikayi latti akan latti. Zakiga laifi na in nace na koreki daga nan? Am talking to you!” Ya k’ara mata wata tsawan.
   
       Hak’urin ma takasa basa se kuka takeyi shark’af shark’af. “Baraki amsa ba kenan?”
       “A’a I’m sorry” ta fad’a da k’yar muryarta na rawa.
     “Kuma kinsan me? Wannan kukan da kikeyin ba damuna yake ba, koda zaki tsiyaye hawayen ki tas barin damu ba, gara kiyi saving nasu kuma har yanzu tsaye kike?”
    Kai ta d’ago a hankali “a’a” nan ta wuce ta had’a masa coffeen bayan ta ajiye masa coffeen ta juya zata fice kenan ya finciko ta da hijabin ta da mugunta wanda sanadiyar haka ya shak’e mata wuya k’ara sosai ta saki take ta soma kuka.
    “Nan gaba zaki sake nanata abinda kikayi yau. Mschwww!” Bata ce masa komi ba jakarta kawai ta d’auka ta fice sam yi yayi kamar be ganta ba. Data sauk’o ma tana jin Yusuf na kiran sunanta ta sharesa k’ofa na bud’uwa ta fice bayan ta yabi da gudu Allah ya so ba keke napep a lokacin tsaye take tana hawaye tana kuka me d’an k’ara isowan Yusuf wajen yace, “Haba Fannah mene yafaru ina ta kirarki kika yi kamar bakiji niba. Wani abu ne?” Batace dashi komi ba se kukan da takeyi.
    “Fannah meya faru kike kuka haka?” Ya tambayeta cike da tausayi. Kukan take har yanzu kamar ‘yar yarinya tayi covering fuskarta da hannu. Hijabinta yaja a hankali ya zaunar da ita kan wata bench. Be sake ce mata komi ba har se sanda ta gama shan kukanta. “Fannah zaki iya fad’amin meya faru?”
     “Ni nabar aiki a nan.” tace tana share hawayenta.
    Cike da mamaki yace, “ban gane kinbar aiki ba Fannah kinsamu wani aikin ne?”
    “Ban samu ba amman zan shiga nema.”
       “Mesa Fannah, na miki wani abu ne?”
    “Baka min komi ba amman Boss naka yamin. Yusuf niba mutun ce me neman magana ba, nayi hak’uri da erin abinda Mr. Fauzi yakemin, I can’t take it anymore wallahi ko kashi bara’a masa abinda Mr. Fauzi kemin ba neman kud’in ba hauka bane. Ni kawai ya biyani kud’in ‘yan kwanakin dana masa aiki zanje in nemi wani.”

     “Fannah kibar magana, nasan you don’t mean what you are saying. Kinsan yadda neman aiki keda wuya ki hak’ura, sekace ban fad’a miki matsalan Boss ba? Haka yake inya k’untata wa mutum ne yakejin dad’i kiyi hak’uri. Yanzu har kika bar aikin nan baki sami wani bafah? Dame zaki biya kud’in magamunan Baba. Kiyi hak’uri.”

     “Kana nufin in cigaba da aiki k’ark’ashin Mr. Fauzi kullum yata cin mutunci na yana masifeni?”

    “Ba abinda nake nufi ba kenan. Abinda nake nufi shine ki k’ara hak’uri, ki cigaba da wannan d’in kina neman aiki nima in shaa Allah zan tayaki. Kinga in muka samo miki seki bar nan d’in amman karki bar nan bakida wani aikin please.”
     Shiru tayi na d’an lokaci “you are right Yusuf nagode sosai.”
    “Always... Mushiga daga ciki kinji?”
   Kai ta giad’a  masa suka dawo ciki tare. Duk inda zasa tana biye dashi. Seda azahar yayi ta koma office na Anas knocking tayi yace, “come in.” Bayan ta shiga ko kallonsa batayi ba ta zarce ta had’a masa coffee.

    “Na d’au kinbar aikin ne ai.” Yace da ita yana daddana laptop. Nanma shiru ta masa ta fice ba ita ta sake dawowa ba se to 4 ta had’a masa coffeensa cikin flask ta d’auka takai masa mota. Shiko Anas ko a kwalar rigarsa daman haka yake so, tana aikinta me kyau ba shisshigi.

    Washegari ya kasance Asabar ba aiki Anas kuwa through the week yasaba da karyawa da coffeen Fannah sam yak’i cin breakfast seya sha coffeen ta tukunah. Wayarsa ya d’au ya kirata da misalin k’arfe 10:30AM alokacin se shiri suke ita da Afrah zasu gidan wata k’awar Afrah data haihu tun bata gama secondary school ba aka mata aure, zasu yin barka. Fannah tayi bala’in kyau tunda nake ban tab’a ganin Fannah tayi kyau kamar na yau ba dake Afrah ce ‘yar gayu ta mata kwalya. Brick red jan baki tasa mata da kwalli da lining sannan ta taje mata dogayen gashin idanunta da mascara ta mata brushing gira tare da shafa mata powder had’adden daya mugun amsar skin nata.

     Sanye take da blue and red atamfa amman red d’in yafi yawa dan dolenta tasa gyale sabida Afrah ta tak’ura mata. Tana zaune tana game tana jiran Afrah wayarta ya soma ringing ganin Mr. Fauzi ke kira ya mugun bata mamaki yaude Asabar ce bakuma ranar aiki ba toh me zekira yace min? Ta tambayi kanta a zuci. “Afrah kiga Mr. Fauzi ke kira meze cemin?”
    “Taya zamu sani in bawai d’aga wa kikayi ba Ya Fannah.”  A hankali ta d’aga tasa a kunne.

*© miemiebee*

No comments: