Friday, 23 September 2016

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 83
BY MIEMIEBEE






   
    “Haba! wifey me yayi zafi haka? Tashi please I’m trying to change your future.”
     “Ya Farouq dan Allah karka gudu dani zuwa wani k’asa daban please.”
    “Kinsan me wifey? Wannan had’ani da Allahn da kike ba tasiri zeyi akaina ba ki tashi kiyi Sallah muyi breakfast inkuma se anjima zakiyi sallahn then muje mu karya.”
    “No Ya Farouq! Allah yafika mugu, azzalimi maras imani kawai wallahi baraka gama da duniya lafiya ba, you are going straight to hell such a demon.”
     “Ki kirani da duk wani sunan daya miki abu d’ayan da nakeson kisani shine ke TAWA CE! YOU ARE MINE!” bejira ta sake magana ba ya finciko ta da hannunta ta sama be direta a ko ina ba se abayin d’akinsu “na baki minti goma kuma” yana kaiwa nan ya ja k’ofar ya rufe.
    Kuka me tsuma rai takeyi tafi minti biyar tsugune a bayin sannan daga bisani ta miqe tayi brushing sannan tayi wanka da alwala, kayan jikin nata ta miyar sannan cike da tsoro ta fito mayafinta na jiya ta gani a k’asa dashi tayi Sallah tariga roqan Allah daya kareta daga sharrin Farouq.

     Bada jimawa ba Farouq ya dawo d’akin zaune yasameta ta d’aga hannu sama tana addu’a, waje yanema ya zauna tare da zura mata ido har seda ta tofe. “Excellent ina fatan kinyi addu’an Allah sa d’an cikin kin me cetoh ne.” Cikin dashasshiyar muryar tace, “me kake nufi Ya Farouq?”
     “Zubar da cikin zanyi bazeyi mu tafi dashi Ukraine ba chan inda na yanke hukuncin zamu, I want us to start a new life.”
      “Nasan ba point rok’anka amman dan Allah ka rufa min asiri karka min haka Ya Farouq na rok’eka please kamin rai.”
     “Wifey fa ba ke nace zan kashe ba shegen abinda ke cikin ki nace zan kashe” ya nuna cikin nata da yatsa. “Before then muje mu karya inajin yunwa.”
     “Banaji kaje ka karya kai kad’anka” ta k’are maganar hawaye na ciko mata a ido.
     “Wifey kinga banason taurin kai nace muje mu karya” bejira ta amsa shiba ya fisga hannunta be direta a ko ina ba se akan dining chair nata “eat wallahi ko kici ko in zubar da cikin nan at this instant.” Shiru tayi bata amsashi ba, bara kichi bane sena zubar da cikin komeh??”
    “Meh amfanin chin abincin? Ko nachi ko banchi ba bashi ze hanaka aiwatar da abinda kayi niyyah ba.”
    “No wifey” ya shafo fuskarta wanda tuni ta bige hannun nasa. “Kichi barin zubar ba.” Idanunta ta d’ago tana kallonsa da nufin bata yarda ba.
   
     “I swear wifey, kichi barin zubar ba, ki k’i chi in zubar.”
   “Kabani reason d’aya da zaisa in yarda dakai.”
    “Because I’m Farouq, now eat.” Fork d’in ta d’aga tasoma ci bayan tayo bismillah se anan ya koma nasa b’angaren dining table d’in shima yasoma chin nasa kamar jiya yau ma fargaba ya hanata chin abincin sosai kad’an tachi taji ta k’oshi. Bayan da yagama chi ya sake janta zuwa d’akin nasu tare dayin wurgi da ita a k’asa, wardrobe ya bud’e tare da ciro wani powdered substance fari k’ulle cikin leather. Tana gani jikinta yabata abin zubda cikin ne kuka ta soma papawa.
    “Ya haka sekace kinga mala’ikan mutuwa?” Kai kawai take kad’awa tana baya-baya. “Ya Farouq dan Allah kayi hak’uri.” Hannunta ya cafko “kinga karma kibani wahala ki bud’e bakinki kisha wannan dakanki if not zan d’ura miki na k’arfi da yaji.”
    “Ya Farouq I beg you dan girman Allah.” Ledar ya bud’e “ungo gashi” sam tak’i karba.
     Kad’an daga cikin maganin yasa a hannunsa tare da maquro fuskarta “bud’e bakin bud’e nace!” gamme bakin nata tayi se buginsa take a k’irji haka seda ta zubar da maganin hannunsa dana ledar duka a k’asa dan shuresan data tayi.

    “Ke?! Bakida hankali ne? Maganin kika zubar?” Wani wawan mari ya kai mata “tunda kince bara abi hanya me sauk’i ba by the time na miki fyad’e anan shegen cikin naki ze zube.” Bugata yayi da jikin bango yasoma sunsunar wuyanta yana bin jikinta da filthy harshensa k’afanta ta saita takai masa bugi a daidai manly place nasa fiye da na jiya.
    “Arrgghhh!!” Ya sakar da wani irin wahalallen k’ara tare da durk’ushewa da gudu ta bi ta gefensa mayafinta daya riqo tasa hanu ta fisge da sauri tasa gudu se k’olla mata kira yake amman sam tak’i juyawa a gurguje tafito daga d’akin ta inda taga staircase tabi wajen. Har a yanzu hannunsa na a rik’e a wajen nasa jikin bango yake dafawa har yafito daga d’akin.

    “Guards! Securities! restrain her!!” yayi maganar da ihu, k’ara gudun ta tayi bayan ta sauk’o last floor d’in ta dosa babban k’ofan data gani, chan tayi kicib’is dawani giant mutumi bak’i k’irin wane an pentasa, baya tayi da wuri ayayinda yake takowa gabanta. “Bawan Allah dan Alkah kayi hak’uri ka rufa min asiri kabarni in gudu dan Allah...” tana maganan tana ja da baya gum! Taji jikinta ya had’e dana mutum a hankali cike da tsoro ta juya fuskar Farouq tagani nan tashiga wani sabon b’arin.
    “You can never escape from me you stupid” yakaura mata mari. “Take her Joseph kaje ka k’ulla min ita da chains ka kuma rufe min bakinta.”
   “Ya Farouq dan Allah kay-” bata k’are maganar ba Joseph ya sab’ata a kafad’arsa achan yaje ya k’uk’k’ulleta****

                 *ANAS* 10:45AM

     Amal ce tsaye akansa yana zaune bisa Sallaya se kuka yake ba makawa, “Ya Anas dan Allah kukan nan ya isa bayida amfani ko bacci fa bakayi ba through out jiya da daddare nafilfili ka rigayi da garin Alkah ya waye yanzu kuma barakayi bacci ba? Please is okay in shaa Allah zamu sami Fannah kabar kukan please.”
    “Angel how?” Abinda bakinsa ya iya furtawa kenan, “taya zamu sameta bayan bamu ma iya reaching nata duk layin da nasan zan iya samun Farouq na kira basu shiga and I have no idea ina zan sameta bansan wani hali take ciki ba Amal.” Bayansa tahau bubbugawa “is okay Ya Anas zamu sameta in shaa Allah.” Daidai nan Ummie tashigo ma Anas da breakfast haka sam yak’i chi danko bayida appetite ko kad’an, inbega Fannah ba bai tunanin ze iya sake chin abinchi da k’ak’ani k’ak’a Ummmie tasamu yaci kad’an bayan yayi wanka suka fita police station dan fara investigating al’amarin. Daga gidansu Fannah suka fara inda akyi ma su Mami da Baba tambayoyi da dama cikin wuni d’aya Mami ta fita hayyacinta ta canza kamanni gabad’aya.

    Waya akasa Baba yayi wa Ya Khaleel bayan ya d’aga aka had’asa da police fitsari ne kawai beyi ba daga jin muryan police. Minti goma kacal aka basa da yazo sa gidansu Fannah if not za’a iya using rashin zuwansa against him ayi arresting nasa.

     _8 minutes later..._
     Daidai nan shigowar Ya Khaleel sekace salihin asali sewani behaving innocent yakeyi tambayoyi da dama aka masa wanda duk ciki be bada amsa d’ayan daya kasance gaskia ciki ba, “ya akayi Farouq yafito daga gidan yari?”
     “Bansani ba wallahi ranka shi dad’e.”
    “When last rabuwanka dashi?”
   “Sati uku da suka shud’e kenan yanzu, tun daga ranan dana kai masa visit dana sake komawa washegari akace min anyi bailing nasa nata gwada layinsa bana iya samunsa, ku tayani nemo d’a na please.”
     “Are you sure Mr. Khaleel danko kamana k’arya zamuje mu duba record.”
    “Www... Wallahi Ba k’arya nake ba” ya k’are maganar yana had’a gumi. Ko da aka buk’acesa da ya kawo wayarsa aduba aga, ba fargaba ya bada saboda Farouq ya fad’a mai aduk lokacinda sukayi waya yana deleting logs nasa dan haka ba’a samu aka gano wani abu ba.
      “Abuu wallahi he is lying he is definately lying yasan duk wani whereabouts na Farouq b’oyewa yake munafikin Allah kawai.”
    “Haba Anas d’ana-” katsesa Anas yayi “shut the f*ck karka sake misantani da d’anka criminal ass kaji na rantse Ya Khaleel kome kake wallahi in na gano you also have something to do with the disappearance of my wife I won’t hesitate to kill you da hannu na zan kashe ka irresponsible father kawai.”
     “Nasan da ky-” be k’are maganar ba Anas ya mik’e a fusace tare da shak’uresa jikin bango “ina Farouq yakaimin Fannah?! Tell me! Ina yakaita?!” Abuu ne dasauran police d’in suka yi sauri suka k’wato Ya Khaleel kafin Anas yayi masa illa, d’an banza tuni nishinsa ya canza idanunsa suka wani fito waje dan azaba.

            *FANNAH*  1:50PM
   A hankali aka bud’e d’akin da aka rufeta ciki, a firgice ta maida kallonta wajen idanunta suna tsiyayar hawaye. Bak’in fuska taga d’auke da abinci da ruwa a hannayensa nan tashiga rawa daidai gabanta mutumin ya ajiye abincin tare da since mata bakinta da hannu d’aya yace “ga abincinki inji Boss kichi.” Seda ta bari yakai bakin k’ofa sannan takirasa da “bawan Allah” chak ya tsaya. “Wani abu ne?” Ya tambayeta tare da kewayo wa.
     “Bawan Allah muslimi ne kai?”
   “Eh me kika ga?” ya bata takiacaccen amsa.
    “Masha Allah k’arfe nawa ne dan Allah?” Bayan ya duba agogon hannunsa yace, “1:52PM” numfashi ta saki “dan Allah ka sinceni inyi Sallah banyi Sallan Azahar ba.”
  “Boss bece in sinche ki kiyi Sallah ba so eat insamu inbar nan.”
    “Be fad’a ba amman ai kai kasan haqqin Sallah dan Allah ka sincheni.” Wayarsa yaciro ya kira Ya Farouq alokacin yana a airport yana proceeding abubuwan tafiyansa Ukraine da Fannah dakuma Ya Khaleel kasancewar yasamu passport nata acikin jakarta.
   
     “Hello Boss gata nan na kawo mata abincin amman tace setayi Sallah.”
   “Karka damu kabarta tayi amman ka tabbata kana tsaye a kanta har tagama okay?”
   “Okay Boss”
  “Good bayan ta gama kuma ka kuma d’aureta karku bari tayi escaping.”
   “Angama Boss” yana gama wayar ya maidashi cikin aljuhunsa sannan ya nufo gabanta ya sinche mata chain d’in da kwad’on da aka datse. Kamar wanda k’wai ya fashe ma aciki ta shiga bayi tayi alwala sannan tayi Sallah duk mutumin na kallonta, jira yake taci abincin yayi tafiyarsa amman tak’i koda bud’ewa.
    “Hey Miss kiyi ki ci abincin mana banason wasan cha-chan nan ya wuceni fah.”
   “Kayi tafiyar ni barin chi ba.”
   “Suits you right” nan ya mik’e ya kamata ya k’uk’k’uleta again hawaye take sosai “bawan Allah nasan da akoi ragowar imani a tattare dakai dan Allah ka taimaka min nakoma gun mijina dan Allah nace.”
     “Allah sarki kyakkyawar hallita sede yadda kika gannin nan barin iya cin amanan Boss d’ina ba” yana kaiwa nan ya fice haka tata kuka gawani erin bak’in yunwan da takeji. Har Sallan Maghrib Farouq be dawo ba kamar d’azu ya tura MB daya kawo wa Fannah dinner anan ne daya sinche ta tayi alwala ta had’a La’asar da Maghrib sede yunwa takeji sosai yanzu dan dole tad’an tab’a abincin.
 
       Tana cikin chi wayar MB yasoma ruri a hanzarce ya d’aga “hello Mazzaaa yaneh?” On the otherisde aka amsa “gani nan fah ina cikin gari wallahi harka ya taso kana ina?”
      “Ohh boi! Ina nan bayan gari ta wajen gidan man Mobil.”
    Gidan man Mobil? Fannah ta nanata a ranta dad’a kasa kunnenta tayi tana sauraronsa.
       “Mobil wanne d’aya kenan Mazzaa?” cewar abokin nasa.
    “Mobil daya d’auki hanyar barin Maiduguri mana ta Yobe.”
    “Oh okay toh zan iso semu had’u.”
   “Okay toh ina jiranka” nan ya katse wayar tare da kewayo da kallonsa kan Fannah, yi tayi kamar bata masan yana kallontaba se chin abincinta take a hankali.
    “Hey Miss ko Mrs kike kiyi sauri kina b’ata min lokaci.”
    “Nagama tace dashi ba imani kaman d’azu ya sake k’uk’k’ulleta sannan yayi tafiyarsa. Tunanin ya zatayi tasamu waya tayi texting wa Anas location da take yanzu take tunda tagano location d’in, sede sam takasa batasan ina zata samu waya ba duk masu ma Farouq aiki zuciyarsu a karye suke kamar nasa.


*© MIEMIEBEE*

beeenovels.blogspot.co.ke