Saturday, 3 September 2016

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 53
BY MIEMIEBEE

Ba Afrah ce ta dawo gidah ba se bayan Maghrib, hankalin Mami duk yabi ya tashi dukda kuwa Fannah ta tabbatar mata cewar Afrah is safe with Shettima k’anin Anas.
   
      “Shettima thank you for today.” Cewar Afrah alokacin da take k’ok’arin bud’e murfin motan. “No let me babe” nan ya zagayo ya bud’e mata tare da ciro shopping bags guda biyu daya cika mata da kayaki. “Will call you as soon as na isa gidah, I love you My Afrah.” Tana murmushin jin dad’i tace, “I love you too My Shettima” ahaka suka rabu.

     Taku take a hankali gudun kar a jiyota aiko tana shiga suka had’u da Aiman kafin tace meh Aiman ta sa ihu “Mami ga Ya Afrah ta dawo.” A 360 Mami da Fannah suka fito. “Ke Afrah zo nan” cewar Mami kai a sunkuye ta k’ariso kafin Mami ta fara mata masifa ta kare kanta ta hanyar yin k’arya “Mami wallahi motarsace ta samu matsala seda muka kira me giara.”
    “Uhn uhn fa Afrah kiyi a hankali daga had’uwan ki da yaro seku zarce da soyayya?”
   “La ilahi! Mami abakin wa kikaji wannan zance?”
   “Ni na fad’a mata ai ba k’arya bane” cewar Aiman. “Mami wallahi har zama sukayi gu d’aya.”
     “Ai Aiman barta-”
    “Mami yi hak’uri ya isa zan mata magana” Fannah ta katse ta a hankali cikin dabara. “Afrah mushiga daga ciki.” Amsar d’ayar ledan hannun nata tayi sukayi d’akinsu. Bayan sun baje kan gado Fannah ta soma mata magana; “Afrah ni bawai hanaki zanba amman ki bi komi a hankali kinji? Na miji na miji ne.”
    “Ya Fannah wai nikan hassada akemin neh? Me aciki keda Ya Anas nida Shettima darling kin-” bata k’are maganar ba wayarta ya soma ruri tana kai dubanta taga Shettima ne datayi saving da ‘hot baby.’ Karap ta d’aga. “Hello baby” tace a nitse cikin wata salon da Fannah bata tab'a saninta dashi ba. Baki ta bud’e cike da mamaki tana kallonta haka har Afrah tagama wayar ta katse Fannah bata bar kallonta ba.

      “Har haka soyayyar taku tayi nisa?”
      “Hummn!” Taja numfashi, “Ya Fannah kenan, guguwar son Shettima ne ya kamani, wallahi ya had’un had’ewa duk abinda nake nema jikin d’a na miji yaja dashi. Daman ni dream d’ina na auri kyakkyawa sega Shettima nan Allah ya kawo min.”
   “Awww! Har tunanin auransa kike?” Cewar Fannah baki wangalau.
    “Humm! aini barni kurum har yaran da muka haifa ma na hango, barni in duba kayakin da ya sissiyo min ma tukun.”

    ★★★★★

       “Ya Anas in shigo?” Cewar Shettima dake tsaye bakin k’ofar Anas.
     “Shigo” ya basa amsa. A nitse ya bud’e k’ofar ba kamar yadda ya saba ba, ‘yar vest na Anas dake k’asa ya d’aga “Ya Anas in sa maka wannan cikin laundry basket?”
   Kallonsa Anas yake yau wata rana. “Eh sa” yabasa amsa. Bayan yasa yadawo ya zauna kusa dashi. “Ya Anas dan Allah alfarma nike nema.”
   “Name fah?” Cewar Anas yana duban laptop nasa.
    “Ya Anas bundle na d’ari biyar zaka bani please.” Ajiye laptop d’in yayi gefe guda cike da mamaki, “Shettima yaushe ne na baka na 200 da zakace in baka na 500 yanzu? Me kake da kud’in. Awww! Kaima kasan kayi girlfriend ko? LOL ba abinda zan baka, go and work for it, earn it!”

      “Ya Anas mana please, wallahi na mayar da hanakalina wajen karatu yanzu ka taimaka please.”
    “Amman Shettima kai kanada hankali mah kuwa? Ina zaka kai Afrah?”
    “Ni Ya Anas banche ka zageni ba, kud’i kawai zaka ban.”
   “Aww kawai ne? Sekayi kashinsa ai tunda kawai ne.”
    “A’a Ya Anas please yi hak’uri.”
   “Naji banasan surutu ina ganinka bud’e safe d’in d’au d’aya kabani waje.” Tsalle ya daka yana masa godiya sannan ya zaro d’aya daya lek’a yaga Anas bai kallonsa ya k’ara d’aya tare da b’oyewa cikin kayansa.
     “Uhm Ya Anas dama nace batun mota ta wallahi ta tsufa tasoma shan mai ko za’a d’an canza min.”
   Maganar da yayi kad’ai yasa Anas shak’ewa harda tari. Dududu shekarar motar nawa ne? Da k’yar inya kai d’aya shine Shettima ke wannan zance.
     “Ai da fili kafito kawai kace min kayi budurwa kaima kanasan ka fara hawa babban mota irin nawa.”
   “A’a wallahi Ya Anas ni ko E350 ka siya min walillahil hamdh Allah zan karb’a, kaji Ya Anas.”
  “Hehehe! su Shettima an girma har ansan ayi budurwa.”
   “Ya Anas mana...”
“Naji in naga kayi hankali zan canza maka motar, inko a’a zaka cigaba da zama da C 230 d’inka.”
    “Thank you so much Ya Anas, nagode, Allah bar mana kai ya k’ara dank’on soyayya tsakanin ka da Fannah.” Bejira jin meh Anas zece ba yafice. Murmushi ya saki jin an ambato sunan Fannah, shi yau through out ma besha coffeen ta ba, yayi missing inshi kuwa sosai, wayarsa ya lalimo ya danna mata kira bada dad’ewa ba ta d’aga “hello Anas.”
    “Fannah” yakira sunanta.
   “Na’am” ta amsa.
   “Yau bansha coffee ba.”
    “Yi hak’uri gobe zanzo in had’a maka.”
   “Har gobe?” ya tambayeta cikin wani irin salo cike da damuwa.
     “Toh Anas ai bareyi infito yanzu ba yayi dare, goben kaji?” Shiru yayi bece komai ba. “Kaji Anas?”
   “Naji” yace chan k’asa k’asa.
   “Yawwa goodnight” sannan ta katse. Ji yake kamar ya sake kiranta bai gajiya da jin muryarta amman kuma bayyasan ta raina sa ta d’au ko sonta yake. Bayan ya idar da isha yayi forcing kansa yayi bacci da k’yar danko yunwa yakeji kamar hauka.

     Washegari ya tashi as usual ya soma shirin office yashiga wanka kafin yafito yaga an share masa d’aki anyi mopping an gyara gado, toh waye ne? Yaushe Amal ta share nata d’akin bale ta share masa nasa, ganin baida amsar wannan tambaya kawai yayi shirinsa yana fitowa yaga shock of his life, Shettima har yagama tsara masa breakfast da alama sharan d’akin ma shi yayi.
   “Shettima?” Anas ya kira sunansa still not believing abinda idanunsa suke gane masa.
   “Na’am Ya Anas good morning bismillah ga breakfast nan na had’a maka.” A hankali ya tako ya zauna kan kujerar Shettima ya zuba masa chips da scarmbled egg daya masa, sannan ya had’a masa tea.
 
      “Tsaya aljanu ne suka shige ka komeh?” Anas ya tambaya.
   “Aljanu kuma Ya Anas? Dan na had’awa wa Yaya na guda breakfast se ace aljanu sun kamani?”
    “Toh d’akina fah? Kai ka share?”
   “Eh Ya Anas bismillah ci kar kayi latti.” A zuci Anas yace ahhh lalle Shettima nasan in canza masa mota LOL gaba ta kaini, nasamu new man servant. Koda yagama breakfast d’in Shettima ne yakai masa jaka mota.
   Tuk’i yake hankalinsa kwance Baana ya danna masa kira cike da jin dad’i ya d’aga.
    “Maza ne!!” Yace yana murmushin jin dad’i.
    “Blue eyes nashigo gari fah jiya.”
  “Ohh haba! Shine baka fad’amin ba?”
   “Wallahi tafiyan dare ne, zanzo office naka yau.”
   “Toh sekazo, Kashim fah?”
    “Wancan? Ai yana chan a Bama ya washi tafiya.”
    “Kace be canza ba kenan, anyhow ina jiranka.” Ding! Ya katse wayar. Kamar kullum aka bisa da gaisuwa har zuwa office nasa, bada dad’ewa ba Kacallah yashigo da complain, na barin gidan man engine da akayi a dalilin haka ya b’aci se an kira me gyara. Bayan da ya gama karantawa yace, “fire him, ka kori me aikin ai ganganci ne yasa sa mancewa be rufe gidan man ba, ka kuma yi replacing nasa with someone better, clear?”
  “Yyy... Yes Sir.”

   8:30AM yama Fannah a building, kamar jirarta Sule me kula da engine yake, yana ganinta ya nufo ta dan yaji intama Boss magana yana saurarenta. Bayan ya gaisheta yake bata labarin abinda ya faru, “wallahi Hajiya waya aka min mata ta tana labour kuma ba motan da ze kaita sesa duk na rikice na mance ban rufe gidan man ba, dan Allah kima Boss magana ya dawo min da aiki na, in na rasa aikin nan bansan dameh zan ciyar da matata da d’an mu data haifa ba.”
   Tausayin sule ne gabad’ai ya ratsa ta. “Don’t worry kaji? Zan masa magana in shaa Allah ze dawo maka da aikinka.”
   “Godiya nake Hajiya, Allah saka miki da alkhairi.”  “Ameen” tace sannan ta fice. Bayan tayi knocking yace, “enter” a nitse ta bud’e k’ofar ta shiga tun daga chan yake kallonta, wata skyblue silky doguwar riga ne a jikinta me dogon hannu, seda kuma red gyale d’an siriri data yafa ta nannad’e a wuyarta. Jaka da takalminta kuwa fari ne. Kallonta yake har yanzu, yafisan ganinta ba hijabi tafi kyau, bayan ta k’ariso gaban table nasa ta gaishesa ba takan gaisuwar yake ba ko amsawa beyi ba “kinyi kyau” yace mata. Tana murmushin jin dad’i tace, “thank you” tare da juyawa nan da nan ta had’a masa coffee, ko ina taje idanunsa na kanta, bayan ta had’a ta kawo masa ta ajiye a gabansa.

     Ba tare da b’ata lokaci ba ya soma sha tana tsaye a gefensa seda taga ya ajiye cup d’in tace, “Sir.” Kai ya girgiza mata “Anas.” Ya gyarata.
   “Okay Anas nace ba batun firing Sule da kayi ne dama.”
   “What about him?” Ya tambaya yana kallonta. “Yabar min gidan mai a bud’e yayi destroying engine d’in sena kira me gyara fa yanzu, he is not paying attention to his work.”
   “Ayyah Anas ba haka bane, matarsa ce tashiga labour shine aka kirasa hankalinsa ya matuk’ar tashi. Dalilin dayasa ya mance kenan.”
    “Wancan kuma damuwansa, he is fired and that stays that.”
    “Anas ka dawo masa da aikinsa please, kaji? For me please.” Shiru yayi be ce komai ba. “Please kaji?” Nanma shiru. Kukan da baya bata wahalan yi ta soma take hankalinsa ya tashi. “Toh kukan me kuma?”
    Cikin kukan tace, “ka dawo masa da aikinsa please.”
   “Fannah NO!” Wani sabon kukan ta k’irk’iro harda me sauti. “Fannah for goodness sake me haka kitayin kuka? In na dawo masa da aikin zaki bari?” Kai ta giad’a “okay, okay naji stop crying.”
    “Se ka kira Adam kace adawo dashi zan dena.” Take yakira Adam, “bring back Sule aikinsa.” Ya katse. “Shikenan zaki bar kukan?”
   “Eh” tace tare da share hawayenta. “Thank you Anas.” Wajen coffee machine ta nufa dan had’a masa cikin flask. Knock ne yazo daga bakin k’ofa “come in” Anas yace. K’ofar na bud’uwa sega Baana bayan ya k’ariso sukayi manshake se hirar su suke irin tasu ta maza nan da nan Fannah tagama d’ura masa coffeen cikin flask, ko d’aga kai taga wayene batai ba. “Sir nagama zan tafi” kafin ya amsata ta fice.
   “Woooww!” Baana yayi exclaiming.
   “Maza wannan me zubin india fah?”
    “Kai de halinka na son mata na nan har yanzu ko?”
   “Me za’a fasa? Gaskia tamin inaso.”
  “Kanaso?” Anas ya tambaya tare da d’age gira. Kai Baana ya giad’a masa yana assuring nasa. “Lallai kam tun wuri ma gomma ka hak’ura wannan tafi k’arfin ka.”
 
    “Ban tsammanin akoi macen da zata fi k’arfi na yanzu, sufa mata kud’i kawai suke bi wallahi yau da za’ace biri goggo yazama billonaire mata zasu bisa su auresa, so ya za’ayi ne in samu lambarta?”
    “You are wrong Baana, kaga wannan duniya da abinda ke cikinta be dameta ba, your money will never impress her, she is different from all other women, saboda haka ka fita daga harkanta.”
   “Kode kaima kana ciki ne?”
    “Ai itace matar da zan aura.”
   “Aure Anas!” Ya tambaya yana zaro ido. “Yaushe a gari?”
“Nide na fad’a maka kafita kabar harkan Fannah wallahi dan akanta se mu b’ata.”
   “Allahu Akbar! Maza kaine kuwa? What changed you haka?”
   “Fannah, she is the one who changed me.”

★★★★★

     *MOROCCO, 2:15PM*
  _Cikin_ *_Royal Mansour Marrakech Hotel.*_
   
    Kwance Anas yke bisa kaftareren California bed ya d’aga pillow tare da jingina ajiki, da isarsu Morocco shida Kacallah awa biyu kenan yanzu. Jiran sim card daya aiki Kacallah siyo masa yake, through out yau be sha coffeen Fannah ba, besata a ido ba, bekuma ji muryarta ba, seji yake kamar ya rasa wani sassa a jikinsa Kafin subar Nigeria yaso kiranta amman girman kai ya hanasa sekuma yanzu yake regreting. Bada d’adewa ba Kacallah ya kawo masa yana sa sim d’in ko gida be kira ba ya zuba number’n Fannah.

****
    Tana kishingid’e a kan gado ita d’ayanta tana buga game a wayarta ya soma ruri ganin international number yasa bata d’aga da wuri ba. A hankali ta sa a kunne “hello.”
   “Fannah” ya kira sunanta.
  “Na’am Anas, ina wuni?”
   “Lafiya” ya amsa blankly.
   “Uhm har kun isa ne?”
   “Eh you didn’t even mind calling me.”
   “I’m sorry, so yaushe zaka dawo?”
   “Are you missing me already?” Ya tambaya yana jin dad’i.
    “Yes I am missing you, I’m missing your your girman kai da masifa.”
   “Ai nabar yin masifa yanzu.”
   “Anya kuwa?” Ta tambaya tana murmushi.
     “Yes, nikuma I’m missing your coffee, your crying and face.” Dad’i sosai taji ya ratsa ta, wannan na d’aya daga cikin abubuwan da takeson Anas, he is very sincere komin ya gaskia take yana fad’i unlike ita, itama tayi missing kyakkyawar fuskarsa sabida rabuwansu da juna tin ran tuesday yau thursday amman ta b’oye masa.

   “To be sincere I miss your face you too.”
    “I know you would, dole zakiyi missing handsome face d’ina ga kuma unguwan ku ba kyawawa ko?”
     “Mr. Fauzi kaga irin halinkan ba, sesa banasan fad’a maka abu kacika feeling dayawa, I have to go Mami na kira na.” Karap ta katse tana murmushi, bawani Mamin dake kirarta bata san me zata ce masa bane kawai, duk lokacin da take waya dashi setanajin wani iri.

      Shigowar Afrah d’akin kenan ansha gayu kamar ba gobe, “Afrah ina zuwa haka?”
    “Wallahi hot baby na ne yazo, yana jira na ma yanzu haka. Madubi nazo kalla in fice” aiko tana ganin kanta ta fice. Tsaye tasame Shettima yayi crossing arms da legs jikin motarsa sanye yake da wata farar half jampa.
  “My queen kinyi kyau” yace da ita alokacin data gama k’arisowa kusa dashi.
  “You too my king.” Hira suka sha kamar ba gobe se kusan Maghrib yace ze tafi  bundle na d’ari biyar ya tsakulo a aljihunsa ya bata. Ido tazaro “hot baby duka wannan?”
   “Eh nakine sweetie, jiya mun samu profit sosai a business namu shine nima nace barin kawo miki rabon ki.”
   “Thank you hot baby” ta amsa. Bayan ta dawo ciki ta wula kan gado ta sami Fannah. “Ya Fannah you won’t believe this.” Bandir na d’ari biyar d’in ta ciro ta miqa mata.

   “Ke ina kika samo wannan?”
  “Hot baby na yabani.”
  “Shettiman? Aina yasamu? Yana aiki ne?”
    “Yana business mana.”
   “Business? Toh aini bansani ba. Ke Afrah bafa haka ake soyayya ba, ai kika cigaba da amsar kud’i dayawa haka gunsa seki talautar dashi.”
  “Toh ai bani yayi ba rok’a nayi ba. Wayyo! A gobe zanje in siyo Iphone nima.”

****

   Chan dare misalin k’arfe goma sha d’ayan dare a Morocco ko bacci Anas yakasa se juye-juye yake, ga gajiya amman yakasa baccin ba abinda yake inbanda tunanin Fannah. “Oh God! What is wrong with me? Why can’t I think of anyone se Fannah? Why?” Pillow ya d’au ya rufe fuskarsa dashi ko ze d’an rage tunaninta, ai se worse ma yake. Wayarsa ya d’ago daga kan bed side drawer ya kirata. Tana cikin baccinta tajiyo ringing na wayarta kamar wacce zatayi kuka ta d’aga ko duba wanda ke kira batai ba.
  “Fannah” ya kira sunanta. Jin muryarsa ta tashi ta zauna.
   “Mr. Fauzi what is it?” Ta tambaya cikin bacci.
  “What are you doing?”
   “Bacci mana” ta amsa sa a takaice rai ad’an b’ace.
    “Okay shikenan” ya fad’a kamar d’an yaron da aka mai rowan sweet ya katse wayar. Wayar ta ajiye ta koma bacci sede kuma daga yadda Anas ya mata maganar kamar bacci ya kasa, sekuma taji tausayinsa yaje chan besan kowa ba wayar nata taja ta kirasa yana gani yak’i d’agawa.
   “Toh ko har yayi bacci ne? Barin sake gwadawa inga.” A karo na biyu ne ya d’aga “Anas” ta kira sunansa a hankali, jin shiru tace. “Anas are you there?”

    “Yes” yace chan k’asa k’asa.
“Ka kasa bacci ne?”
   Nama “yes” yace. Shiru tayi tana nazarin me zata ce masa chan tace, “uhm if you need someone to talk to I’m here for you.”
    “Just go, jeki kwanta.”
   “Anas kaifa?”
   “I can’t sleep” yanason yace mata saboda yana missing nata ne ya kasa bacci amman kuma yak’i.
    “I can’t either.” Ta fad’a.
   “Why? Ba bacci kikeyi ba yanzu?”
  “Not anymore, you can’t sleep I’ll stay awake with you.” Dad’i yaji sosai.
   “Are you sure?”
   “Yes” ta fad’a tana giad’a kai.
   “Thank you.”
   “So yaushe zaka dawo?”
   “Maybe in 3-4 days time.”
  “Okay Allah kaimu.”
  “Ameen, so ya Afrah da Shettima?”
  “D’azu ma yazo wajenta, wai dama Shettima na business?”
   “Business kuma wani erin business kenan?” Anas ya tamabaya cike da rashin fahimta.
    “Nima I don’t know haka yace mata wai yana business harda kawo mata bundle na N500 dayazo.”
    “Are you serious?? Lallai ma Shettima, abinda zeyi da kud’in kenan dama. LOL”
   “Kamar ya Anas?”
     Nan ya labarta mata yadda Shettima yasamu kud’in. Dariya sosai dukansu suka b’arke da. Haka sukata hira kamar ba gobe sekace ba Mr. Fauzi ba, sun fi awa suna waya har bacci ya sace Fannah.
Jin shiru ya kira sunanta, shiru bata amsa ba “kinyi bacci ne?” Nanma shiru. “Goodnight” ya fad’a ahankali, k’in kashe wayar yayi yana d’an jin nishin Fannah da haka shima ya samu yayi bacci wayar mak’ale a kunnesa.

 
   *©miemiebee*

No comments: