TANA TARE DA NI... PAGE 36
BY MIEMIEBEE
Duk ta gama tsorata ta d’au ko farkawa zeyi yako kama ta red handed, se taga kwanciyar sa ya giara, numfashi ta saki tare da godewa Allah. Inda ta mayar da littafin tasake cirowa, third page d’in ta bud’e taga another family photo, wannan harda Amal aciki da alama be jima suka d’auka ba. Gefen mahaifinsu ne taga wata mata wanda a da takeson tace ko matar sa ne sede kuma taga kamanninsu ya b’aci sosai da mahaifin nasu setayi tunanin ko sister’nsa ne amman toh me ze kawo sister’nsa gidansu har su d’au family photo haka? Ina asalin mahaifiyar tasu taje?
Next page ta juya taga an rubuta da babban bak’i “I REGRET KNOWING AND HAVING YOU AS MY MOTHER UMMIMI.” Ido wuru-wuru ta zaro yau tana ganin ikon Allah, mutum yace yayi nadaman sanin mahifiyar sa toh me dalili? Daidai zata fara karantawa kenan taji Anas ya sake motsawa tare da giara kwanciyar sa. Tana b’ari ta rufe tare da mayarwa yadda ta samu. Gabansa ta nufa ta karb’e giyan a hankali yadda bare tashe shi ba, taje ta zubar a bayi tare da yin flushing. Tanasan giara masa kwanciya amman tuna abinda ya mata lokacin datayi hakan a baya yasa ta fasa ta barsa kwance yadda ta samesa. So take ta karanta abinda yake rubuce cikin littafin d’azun amman kuma tana tsoro kar Mr. Fauzi ya kamata ya cicci mata mutunci da k’yar ta hak’ura ta fice zuwa office nata akan zata dawo anjima inya tashi yayi signing papers d’in. AC ta kunna kad’an ta kwanta kan makeken 3 seater cushion dake office nata a hankali bacci me nauyi yayi gaba da ita se can azahar ta tashi tayi alwala tayi sallah sannan tafito ta nufa office na Anas knocking tayi sau biyu ba amsa dan haka kawai tashiga kwance ta samesa har yanzu yadda ta barosa tin tin d’azu, daidai nan wayarta ya soma ruri tana kai dubanta taga Yusuf ba tare da b’ata lokaci ba ta d’aga “Asssalamu alaikum.”
“Wassalam, Fannah Boss yayi signing takardun kuwa? Mutanen sunce zasu zo su amsa yanzu sun fasa zuwa goben.”
“Mun shiga uku Yusuf Mr. Fauzi bacci yake tun d’azu nikuma tsorin tayar dashi nake.”
“Toh Fannah ya zamuyi? Kisan nayi please yasamu yayi signing.”
“Toh me zanyi Yusuf? Kazo ka gwada tayar dashi please.”
“LOL amman fa kin tsane ni Fannah, try your best kawai I’m hanging” nan ya katse.
Hannunta takai baki tana cin farcenta dan rashin sanin abinyi, chan ta d’ago files d’in da biro ta nufa kan Mr. Fauzi ta tsaya cak tana nazarin abinyi. A hankali cikin siririyar muryarta ta kira sunan sa “Mr. Fauzi!” Shiru be amsa ba. “Mr. Fauzi!” nan ma be amsa ba, biron hannun ta tad’an tab’a sajen fuskarsa dashi daga sama zuwa k’asa, kan nasa ya kad’a yana me cigaba da baccinsa. Haka ta tayi amman sam yak’i tashi da abin ya ishesa biron ya fisga sauran kad’an ya cafke da hannunta. Wurgi yayi da pen d’in. “Mr. Fauzi please kayi hak’uri ka tashi kayi signing papers d’innan.”
“Wake magana?” Ya tambaya cikin bacci.
“PA’rka ce Mr. Fauzi, Fannah Aleeyu.”
“Fannah Aleeyu inhar kinason aikin ki toh ki fita kibar min office, bakiga ina bacci bane?” ya fad’i idansa a rufe yana bacci.
“Nagani Sir hak’uri zakayi it won’t take long, kawai signing zakayi seka koma baccin, yi hak’uri.” A hankali ya bud’e idanunsa da suka kad’a sukayi ja yana kallonta inda wani ne ko wata daban da tuni yayi firing nasu amman ganin Fannah se bakinsa yakasa furta kalamun “you are fired” wanda ya rasa dalilin hakan.
Kanta ta sunkuyar, “Please Sir signing nasu kawai zakayi I’m sorry for disturbing you” ta fad’a cikin nitsatssiyar murya. Hannu ya mik’a mata da nufin ta basa papers d’in. Murmushi sosai tayi dan dad’in daya ratsa ta yau wata rana Mr. Fauzi be mata masifa ba cikin kyaftawan ido ta d’auko biro ta bud’e tare da mik’a masa, amsa yayi tana nuna masa inda zeyi signing har yayi signing duka. “Thank you Sir” tace masa a lokacin daya mik’a mata biron. “Sir azahar yayi da ka dage idar seka cigaba da baccin.”
Kaman wanda bareyi magana ba kuma chan yace, “me ruwanki da sallah na toh? Kabarin mu d’aya ne? Banasan shisshigi you can go tunda na miki signing.”
“I’m sorry” tace masa tare da juyawa ta fice. Tsuka yaja, tare da sake rufe idanunsa dan cigaba da baccin sede ya kasa kalamun Fannah na “Sir azahar yayi da ka dage ka idar se ka cigaba da baccin” suke ta yawo masa akai ai haka ya kasa cigaba da baccin dukda kuwa yanaji sosai dan dolen sa ya fad’a bayi yayi alwala sannan yafito yayi sallah bayan ya idar ya tsaya mamakin kansa ma. Wai meke damunsa? Taya Fannah zata ce yayi abu kuma yayi? Impossible! Bayan ya nad’e sallayan ya koma kan table nasa ya zauna se yanzu ma ya lura da state na office nasan, sab’anin yadda ya barsa kafin bacci ya sace sa. “Wait! Ina beer na?” ya tambayi kan sa. Office d’in kap ya duba ba alaman kwalban giyansa. Tashin hankali bame masa wannan d’anyen aikin se Fannah. Telephone nasa ya daddana ya kira Fannah tana zaune a office nata da sabuwar iphone da Anas yabata se game take bugawa hankalinta kwance bayan tama Yusuf submitting files d’in. Telephone nata ne ya soma ringing tana dubawa taga Anas ke kira, nan take bugun zuciyarta ya canza Allah sa bawani abun tayi ba.
Ko k’ala bata samu tace ba bayan ta d’aga Anas ya soma magana cike da tsiwa “Ke ‘yar shisshigi ba? come to my office right away!” karap! ya katse. Miyau ta had’iye dan tasan she is in trouble Allah sa ba ganewa yayi ta karanta masa wancan littafin ba. As soon as possible ta isa office nasa bayan tayi knocking yace, “enter” kanta a sunkuye ta shiga “yes Sir” tace.
“Ina ragowar beer na?”
I’ina ta soma dan tsoro “uhm uhm Si.. Sir...”
“Ina yake nace?!” Ya daka mata tsawa.
A firgice tace, “na... Na zubar...”
“Kin zubar?” ya tambayeta cike da mamaki “Ban hanaki ba?”
Kan wanda zatayi kuka tace, “ka.. Ka hana kayi hak’uri dan Allah.” Kai ya giad’a tare da sakar da wata murmushin mugunta “jeki d’auko pencils naki a office kizo ina jiran ki yanzu.” Kwata kwata bata fahimce me yake nufi ba, meh had’in pencil kuma a wannan matter? “Bakiji me nace bane?”
“Nna.. Naji” tace da sauri ta juya tafice bayan minti d’aya ta dawo da pencil pack a hannunta. “Good” yace mata kai ya sunkuyar k’ark’ashin table nasa tare da jawo wata kwali babba. Papers ne ciki ba iyaka hannu kawai yasa ya d’iba dayawa daga ciki wanda sun kusan d’ari biyar. Bayan ya ajiye kan table yace, “d’auka.”
“In d’auka kuma Sir? In kai ina?”
“Ki kai wa me k’osan unguwankau shegen suratan banza. Ki duba cikin kowani page a second paragraph akoi mistake da akayi agarin printing, wajen ‘how’ se computer yasa ‘hoe’ inasan ki zauna ki nutsu ki kibi su one by one ki giara mistake d’in.” Ido sosai Fannah ta zaro tare da sake baki.
“Sir duka?”
“Yes Miss Aleeyu duka, 500 pieces ne anan yi sauri karki b’ata mana lokaci akoi abinyi dayawa yau.”
Kamar wacce zatayi kuka tace cikin siririyar muryarta “Sir dan Allah badan hali na ba kayi hak’uri wallahi tun rubutun jiya hannu ya kumbura gakuma yankan danayi d’azu da glass kayi hak’uri please a sake re-printing.”
“A sake re-printing?” Ya tambayeta tare da d’age gira. “Wannan kuma ayi asaran su a zubar kenan ko meh kike nufi? Kefa kikace min almubazaranci ba kyau, ai kuma zubar da wad’annan yazama almubazaranci ko ba haka ba Malama? Kidena sani surutu tattara ki zauna acan ina ganinki ki fara giarawa, off you go.” Fuska ta kuma yamutsawa “Sir please I’m sorry barin sake zubar maka da beer naka ba.”
Nuni ya mata da hannu “banasan surutu kibar min kai please nima inyi abinda ke gabana.” Haka kamar zatayi kuka ta tattara papers d’ari biyar ta nufa kan kujera ta zauna ta soma neman mistake d’in can gani ta giara ‘e’ na ‘hoe’ zuwa ‘w’ wa ‘how’ kallonta Anas ya tsaya yi a ransa yace daidanki kenan, nan gaba zaki sake wuce gonanki, a karkace ma ta rik’e biron dan ciwon da hannunta yake mata, amman haka ba tausayi bale tsoron Allah Anas ya shareta ya ciro model nasa na ranan ya cigaba dakayi.
Guda d’ari Fannah tayi amman tagaji lik’is kai ta d’ago tana kallonsa “Sir please kayi hak’uri” banza da ita yayi ya cigaba da abinda ke gabansa. “Sir I’m sorry barin k’ara ba ka tausaya min please wallahi hannu na naciwo sosai please...” Nan ma bece mata komai ba. Ai kuka Fannah ta fashe masa da a office. Lallai yarinyan nan ya fad’i a ransa a yayinda ya d’ago kai yana kallonta da d’an gyalenta ta tare fuskarta tana share hawayenta ganin se kallonta yake ta sake k’ara k’arfin kukan. “Guda nawa kikayi?” Ya tambayeta.
Numfashi take ja kamar ‘yar yarinya “guda hundred.”
“Kacal?” ya tambayeta “you are not serious get on with it.”
“Sir dan Allah kayi hak’uri na tuba.”
“Ki k’ara 150 akai then zanyi deciding ko in hak’ura.”
“Sir 50 please, zan k’ara hamsin akai.”
“Nace 150 inkuma barakiyi abinda nace ba seki yi duka 500 d’in.”
“A’a zanyi” kanta ta sunkuyar ta cigaba dayi. Daidai lokacin wayar Anas ya soma ruri sanda ya kusan tsinkewa sannan ya d’aga ganin Salmar ranan ke kira.
“Hello eye candy, ya kake?”
“Ba lafiya ba” yabata takaicaccen amsa a fusace. A hankali Fannah ta d’ago kai tare da barin abinda takeyi tana kallonsa bata san da wa yake wayar ba amman daga jin wannan kalan walak’anci tasan da mace ne.
“Eye candy me ya sameka? Haka jiya na wuni ina jiran call naka shiru.”
“Eh Salma banida time naki ne shiyasa ban kira ba, ni nagaji dake ma lets just break up.”
Cike da mamaki Fannah ke kallonsa inba wai ta mance ba wannan itace salman da sukayi waya shekaran jiya har take ce masa ta gode da kayan daya siya mata, ayyah ita shikenan tabi sahu.
“Blue eyes dan Allah karka min haka, in wani abin nayi tell me.”
“Tak’uri na da kike min shi yake damuna karki sake kira na fad’a miki we are done.” Ding! yayi hanging. Kallonsa Fannah ta tsaya yi. “Zaki bar kallo na ne kokuwa se na k’ara miki wasu papers d’in.”
Take ta kau da kallonta daga garesa tare da cigaba da abinda takeyi. Ta gefen idanta taga ya ciro littafin d’azun, d’an rubuce yayi kad’an ciki ya mayar. Toh me ya rubuta ciki? Mesa baya mutunta mata ne? Toh aima ba abin mamaki bane mutumin dayace yayi regreting sanin mahaifiyar sa kam wace mace ce bare wulak’an ta taba? Tayi ta huta tayi ta huta ahaka har tasamu tagama iyaka 150 dayace ta k’ara. Hannunta ya kumbura iya kumbura gashi se wani shaking yake shi kad’ansa dan azaba.
Bayan ta mik’e taje ta ajiye masa kan table nasa “Sir gashi na gama”
“Ki k’ara 50 akai, punishment naki na kallo na d’azu.”
“Sir wallahi baran iya ba hannu na na ciwo kayi hak’uri barin k’ara ba.”
“Senace ki k’ara d’ari zaki bar nan?”
“A’a Sir dan Allah kayi hak’uri.” Kuka ta soma masa kamar ‘yar yarinyar da aka k'wace mata sweet. Shark’af shark’af. Blue eyes nasa ya d’ago yana kallonta a yayinda ta rufe fuskarta da gyalenta ta tacigaba da kukan.
“Kin d’au wai kukanki ne ze sa incanza mind d’ina?”
Kai ta kad’a masa tana me cigaba da kukan.
“Toh kimin shiru” yace. Kum tayi tsit. “I’m letting you go for today amman nan gaba na sake kama ki kina kallo na guda 500 gaba d’aya zaki giara kuma in dad’a miki, I hope am clear?”
Kai ta giad’a a hankali, sekuma ta tuna dokokinsa. “Yes Sir” tace masa.
“Ina jotter’nki?”
“Yana office Sir.”
“Yau ma ko? Ban hanaki ajiye jotter’nki a office ba?”
“Sir I’m sorry.” Ta basa hak’uri tana share hawayenta.
“No, you are not Miss Aleeyu d’au ragowar papers d’in kigama giarawa nan gaba baraki manta ba.” Zata soma masa kuka ya tsawatar mata “in kika bari wancan hawayen yafito believe me wasu sabi zan d’auko miki kuma ki giara.” Hadi’ye hawayen tayi duka. “Na baki a minute kije ki d’auko jotter’n the next time kika sake mancewa dashi kuma zakiyi bayani.”
Tun kafin minti d’ayan ya cika taje ta d’auko ta dawo. Sanda ya k’are mata kallo sannan yace, “Good. Kije mail room a first floor ki kawo min important mail d’ina sauran da kika ga basuda ma’ana ko amfani sekiyi watsi dasu. Kije kitchen also kiyi firing Chef Khadija akwai list na wanda suka jima da applying a 3rd floor wajen Ahmed ki karb’a ki musu sending email ta email addresses nasu. Akoi business trip da zanje in 2 weeks time a Morocco have it rescheduled nan da 2 months haka. You can go.”
Ita duk ba abinda yake damunta ba kenan taya zataje ta fara firing mutum, gaskia barata iya ba. “Bakiji me nace bane?” Ya fad’i tare da dawo da ita daga duniyar tunanin data wula.
“Naji Sir but please batun firing chef Khadeeja barin iya ba.”
“Baraki iya ba?”
“Eh I’m sorry” ta giad’a kai a hankali.
“Toh sekizo ga 500 papers a nan kizo ki cigaba da correcting mistakes d’in.”
“A'a Sir dan Allah kahi hak’uri wallahi hannu ya kumbura.”
“Then kije kiyi firing nata banasan sake jin wani abu, get out!” Kamar tayi kuka ta fice se tunanin ya zata soma firing Khadeeja take har elevator’n ya bud’u. A sanyaye ta fita tare da shiga kitchen d’in.
*© miemiebee*
No comments:
Post a Comment