TANA TARE DA NI... PAGE 85
BY MIEMIEBEE
Asuban fari ta tashi tayi Sallah da nafilfilunta bata damu da tada Farouq ba danko tasan bayi zeyi ba, bayan ta kammala addu’o’inta takoma kan kujera ta zauna tata Azhkar har garin Allah ya waye. K’arfe 8:30AM ta shiga bayi tayi wanka wani highwaist skirt da karinat blue tasa sannan ta lullub’e jikinta da mayafi babba se 9:30AM Farouq ya tashi ”good morning Ya Farouq” ta gaidashi.
“Morning wifey how was your night?”
“Alhamdulillah I hope yours too, na had’a maka ruwan wanka kashiga kayi semu karya” ba musu ya miqe yashiga anan ta ciro masa wani sky blue jampa ta ajiye kan gadon. Wajen bayin ta nufa ta kasa kunnenta jin bulbulan ruwa ta tabbata wanka yake dan haka ta nufa wajen side drawer’n kansa, kwalin baby nokia sabi tagani har guda biyar wanda taga alamun kamar an bud’e ta k’arisa bud’ewa tacire se juya baya take gudun kar Farouq yafito. Abin takaici taga ba sim ciki ta duba sauran drawers d’inma babu. “Mschww! Ya Salam!” Cikin wardrobe nasa ta nufa tasoma neman sim card one by one take bin kayakin nasa achan counter’n k’arshe taga sim packs kusan goma hamdala ta saki daidai tasa hannu zata zari d’aya kenan Farouq ya murd’a handle na k’ofan, a gigice ta miyar da su ciki. Da towel d’aure a k’ugunsa ya doso inda take “me kikeyi wifey?” Ya tambayeta ba wasa a fuskarsa. B’arin baki ta soma ganin bata gama miyar da kayan nasa yadda ya bari ba.
“Uhmm... Ermm. Ya Farouq har ka fito?”
“Eh meh kikemin cikin kaya?”
“Bbb.. Babu kaga kaya nake nema maka na cire wancan” tayi nuni da jampan dake kan gadon “sekuma bemin ba nafison kasa farin jampa.”
“Hakane wifey?”
“Eh Ya Farouq fari zefi maka kyau.” Dad’i sosai sokon yaji “toh ai ga inda nake ajiye fararen kayaki na” nan ta matsa masa ya zaro wani farin half jampa “good kayi ka shirya muje mu karya am hungry.”
“Okay wifey” cikin d’an k’ank’anin lokaci ya shirya suka fice zuwa dining room achan aka had’a musu had’ad’d’en breakfast suna hira suna chi Fannah na iya k’ok’arinta dan sakewa da Farouq tanason yayi trusting nata sosai.
*ANAS* _10:36AM_
Zaune yake a d’akinsa ya had’a uwa uba tagumi gabad’aya ya fita daga hayyacinsa ba aikinsa banda tunanin Fannah rabuwansa da bacci tun da Farouq ya d’auke Fannah.
“Anas!” Cewar Abuu yana buga k’ofar d’akinsa. “Kafito mu karya kaji already police d’in suna jiran mu.” Shiruuu... “Anas in shigo?” Nanma shiruu dan haka ya sa kai kawai. Hannu ya dafe a kafad’ar d’ansa. “Anas take it easy wallahi da abinda kakeyi zaka kamu da ciwon zuciya zamu sameta in shaa Allah. Ba kanada bank details nasa ba? Nayi magana da bank d’in za’ayi freezing account nasa.” Cike da tashin hankali ya juyo yana girgiza wa Abuu kai.
“A’a Abuu please kar muyi haka wallahi zamu sake worsening situation d’in karmuyi dan Allah banason yayi ma Fannah wani abu.”
“Anas wani erin magana kake?”
“Abuu please dan Allah kar ayi freezing account nasa ni nasan Farouq.”
“Shikenan zan musu magana abari kamar yadda kace yanzu tashi muje mu karya semu fita.”
“Abuu fitan nan baida amfani we can’t ever find her hanyan sauk’i shine mu kama Ya Khaleel. yaji an kama Babansa a hannu ze sake min Fannah.”
“Anas hakan bame yuwu wa bane we don’t have any evidence da ze nuna Ya Khaleel na aiki da d’ansa.”
“Akwai Baba muje mu duba record na Farouq wa yayi bailing nasa am sure Ya Khaleel ne.”
“Toh naji yanzu de katashi muje mu karya” Anas ya bud’e baki zeyi magana Abuu ya dakatar dashi “a’a karka cemin bakajin yunwa tashi muje” shida kansa ya miqar da Anas suka nufa dining.
★★★★ *FANNAH*
_1:15PM..._
Zaune Fannah da Farouq suke akan dining table daidai zasu fara chin lunch kenan aka k’wank’wasa k’ofa “MB get the door” cewar Farouq kamar yadda ya buk’ata haka MB yayi.
“Wayene?” Farouq ya tambayui MB. Kafin MB ya amsa yaron yayi magana;
“Bad boy ne ya turoni wai abasa kud’insa.”
“Ba yayi tafiya?” Yayi maganar yana barin kan kujerarsa dad’i sosai Fannah taji dataga be d’aga wayar saba, yanzu zata iya texting Anas. Har ya kusan bakin k’ofar sekuma ya dawo ya d’au wayar batasan lokacinda tayi tsaki a fili ba.
“Wifey lafiya?” ya tambayeta.
“Uhmm lafiya, banji dad’in d’aga kan da akayi bane daidai zamu fara chin abinci.”
“Karki damu I will be right back” kai kawai ta gyad’a masa ya fice ya rage daga ita se MB a d’akin, abincinta ta nutsu taci se tunanin ya za’ayi tayi texting Anas location d’inta take. Abu kamar wasa fa Farouq be dawo d’akinba.
_32 minutes later..._
K’ofan akayi banging dalilin firgitan da Fannah tayi seda ta yasar da apple dake hannunta tare da juyowa a kid’ime Farouq tagani idanunsa suna wani juyawa kallo d’aya tayi masa tagano abige yake. MB ne ya taimaka ya k’ariso dashi kan kujera ya zaunar dashi.
“Omg! Farouq meya sameka haka?”
“He had too much to drink” cewar MB.
“Okay excuse us zaka iya fita I will take care of him.” Ba musu MB yayi excusing nasu, anitse ta baro kujerarta ta nufa wajensa. “Ya Farouq meya faru? Me kasha haka?”
“Karki damu wifey wannan shegen bad boy d’inne yakeson rusa min plans ya dawo kuma yana buqatan kud’insa”.
“Toh ka basa mana.”
“Wifey kikace miliyan shabiyar kikeso in na basa kud’insa goma ne ze rage.”
“Semu sake tambayan Anas ai karka damu kasan me nakeso dakai? Ka huta yanzu kaji?” Kai ya gyad’a mata. Gabansa tayi clearing ta kwantar da kansa a hankali idanunsa suka soma kafewa har bacci yayi gaba dashi. Side pockets na jampan sa ta dudduba bata ga wayarsa ciki ba data leqa setagansa cikin aljihun chest na rigan tunanin ya zatayi ta ciro take seta kai hannunta se tsoro ya hanata danko tana da tabbacin baccin sa beyi nisa ba at any moment ze iya tashi yakamata red handed. Zama tayi gefensa tana tunani chan ta kira sunansa “Ya Farouq!” Shiru ba amsa “Ya Farouq” tad’an buga table d’in.
“Urghmmm” yayi groaning cikin bacci.
“Ya Farouq ka tashi muje d’aki ka kwanta kaji? Nan is uncomfortable.”
“Bari karki damu.”
“Dole in damu mana Ya Farouq d’ina na kwance a tak’ure tashi muje d’aki kaji?” A kasalance ya miqe dan yadda ya bugu ko bud’e idanunsa bai iyawa dan bata da wani hali ne kawai tasa hannu ta taresa ganin yakusa fad’i a k’asa. “Astaghfirullah” ta rigayi har seda ta jibgesa kan gadon d’akinsu. Kamar mamaci ya soma sabon bacci wajen.
Bad to worse tace a ranta “yanzu ya zanyi inciro wayar yadda yayi ruf da cikin nan?” dabara ce ta fad’o mata. “Ya Farouq ka cire kayan mana zaka fi jin dad’in baccin...” Shiruuu
“Kaji Ya Farouq tashi ka cire kayan se ka kwanta” da k’yar ya tashi ya cire kayan ya wurga mata hamdala ta saki. “Rataya min akan drawer” yayi maganan a bige. Yadda ya buk’aceta tayi a hankali ta juyo ta kallesa ganin idanunsa a rufe tasoma lalimo aljihun nasa dan ciro wayar har takai kai sauran cirewa kawaibFarouq ya miqe, da wuri tabar wajen ta k’ariso wajen gadon “mene ne Ya Farouq?” Bakinsa kawai ya toshe agurguje ya ruga bayi amai ya riga kwararowa hakan yabata daman ciro wayar, b’ari duk wani sassan jikinta ke har tasamu tayi texting Anas kamar haka;
_Anas Habeebi its me Fannah, Mobil filling station Yobe by pass come ASAP and save me please PS don’t call._
Bayan tayi sending tayi deleting a take, kafin tace zata miyar da wayan Ya Farouq ya fito daga bayin idanunsa basu sauk’a ako ina ba se Fannah dake riqe da wayansa seda ya k’ariso gabanta ya tambayeta “meh kike min da waya?” Gabaki d’aya ta tsure kasa koda furta ‘A’ tayi se rawa jikinta ke.
“Magana nake miki meh kikemin da waya?”
“Bbb... Babbu..” Hannu yasa ya fisge wayar, call logs ya shiga ya duba sannan messages nanma bega wani abu ba sede jikinsa na basa ba lafiya ba.
“Baki amsani ba nace me kikemin da waya?”
“Bb... Babu Ya Farouq wayar ne ya fad’i garin rataya maka kayan naka shine na d’ago.” Tayi magana cikin murya me rawa.
“K’arya kike Fannah meh kika min da waya?”
“Allah babu Ya Farouq ka duba kaga.”
“Fannah kinsan in na gano wasamin da hankali kike zan mugun sab’a miki.”
“Ya Farouq ya kake magana haka ne? Kaima kasan wannan ba trick bane inasonka Ya Farouq.”
“Barin ga ko dagaske ne kinaso na.” GPS radio yayi turning off sannan ya kira Anas***
*ANAS*
Yana cikin motarsa acikin gari yanzu barinsa police station an yarda da yamma za’a je a duba record na Farouq. Driving yake a hankali koda yaji wayansa yayi k’aran shigowan new message a while ago be damu yaduba ba acewarsa seya isa gida ya duban. Ganin kiransa kuma ake yanzu ya d’ago wayar ya duba sabon layi yagani kafin ya nemi waje yayi parking ya d’aga wayar ya tsinke. Daidai zeyi calling back kenan yace bari ya duba saqon tukunah. K’wararo idanunsa waje yayi bayan daya karanta. “Flower! Its Flower!” Har ya danna numban ze kira sekuma yatuna tace kar ya kirata take yayi mastering numban kar incase zata kirasa. Yakai kan numban Abuu kenan yaga exact numban da Fannah ta turo masa message dashi na kira, ba tare da b’ata lokaci ba ya d’aga “hello Flower??”
Wani shu’umin murmushi Farouq ya saki yana kallon Fannah “so its true you called him with my number koh?” kafin ta hankara ya shaqure mata wuya hannunsa tahau bugi “Ya Farouq dan Allah kayi hak’uri ka sak.” Kasa k’arisa maganan tayi dan yadda ya shaqe mata wuya.
“Hello Farouq?! Me kake mata please ka saketa. Flower kina jina?”
“Anas Habeebi please help me ze kasheni.” tayi maganar da k’yar.
“Farouq me kake mata? Ka saketa please dan Allah don’t hurt her.”
“Kasheta zanyi ni zata raina ma wayo kasani kayi ban kwana da matarka dakuma d’anka” yana kaiwa nan ya katse wayar. Koda Anas ya sake gwada kira kuwa bai shiga Abuu ya kira da sauri ya fad’a masa location da Fannah ke, shima Abuu ba tare da b’ata lokaci ba ya sanar da police koda ya cewa Anas ya jira sutafi duka a tare k’i Anas yayi he can’t wait to save his Flower.
****
“Kiransa kikayi ko meh? Munafukar Allah kawai ni zaki raina ma wayo kiyi tricking d’ina? Me kika yi da wayan nache?”
“Aahh..hahhh” ta soma wani erin nishi. “Yya.. Farouq dan-” sama sama nishinta ya soma ganin zata mutu masa ya saketa tari ta hau yi idanunta sun kad’a sunyi jazir suna tsiyayar hawaye. “Wait what do you mean da kikace Anas yazo ya taimakeki, texting masa location d’innan kikayi? Magana nake miki!” Nanma shiru se tari take tayi. “Kin fad’a masa location da muke koh? Hohoho! Smart girl zakiyi bayani.” Akwati ya ciro yasoma had’a musu kayakinsu har a yanxu Fannah bata yi recovering ba daga shaqentan da Farouq yayi bayan yagama had’a musu kayakin ya tattara abubuwan daze buk’ata “tashi mutafi.”
“Ya Farouq dan Allah kayi hak’uri karka kaini wani wajen.”
“Maganan banza ina ni zaki raina ma wayo? Semuga ya Anas nakin ze cetoh ki” bejira ta sake cewa wani abu b ya fisgota sannan ya soma janta se rok’onsa take amman ko a kwalan rigarsa. Daidai wajen staircase ta durk’ushe ta kankame k‘arafun “meh haka?! Ki tashi mutafi.”
“Wallahi barin bika ba mugu kawai ka sakeni.”
“Ina wasa dake ne?! Nace ki tashi!” sam tak’i motsawa ganin ba mahalicci se Allah ya sauk’a ya ajiye jakan nasu sannan ya sake haurowa nan suka shiga dambe sam tak’i sake k’arafun gagam ta rik’e ita barata bisa ba seda yayi dagaske sannan ya samu ya sauk’o da ita se fad’anshi take. Wani syrup ya ciro daga cikin jakar. “Ya Farouq dan Allah kayi hak’uri karka sani shan wannan abun, na tuba dan Allah kayi hak’uri...” Ko sauraranta beyi ba yaja hannunta ya danne ta a k’asa tare da had’a hannayenta biyu gu d’aya, kwalban yakai mata baki sede sam tak’i bud’ewa “ki bud’e nace!”
Se hawaye take abin tausayi tana girgiza masa kai, “nace ki bud’e” goshi ya gara musu wanda sanadin haka ta bud’e bakinta tare da sakar dawani irin azabartacciyar k’ara, hakan yabasa daman sa mata kwalban a baki seda ya juye mata tas sannan Ya cire, tarawa tayi a bakin nata tak’i had’iyewa “ki had’iye nace!” ganin tak’i had’iyewan kuma tana cinye masa lokaci ya matse mata hanci tun tana iya jurewa har numfashinta ya soma yankewa idanunta sunkad’a sunyi wani irin jaa bayan riqe numfashinta data tayi daga k’arshe kawai ta had’iye ganin zata iya mutuwa ga mugun yak’i sake mata hanci kuma.
Daidai nan aka hankad’o entrance door d’in da wani irin force da seda ya k’ofar ya fad’i a k’asa da hanzari Farouq da Fannah ke kwance bisa cinyansa idanunta suna wani kakkafewa ya miyar da kallonsa bakin k’ofar. Fannah kuwa da k’yar idanunta suka iya comprehending mutumin dake tsaye bakin k’ofar. “Anas! Habeebi” kad’ai bakinta ya iya furtawa. “FANNAAAHHH!!!” Ya kira sunanta cikin tattausar murya me uban sauti. Sandarewa Farouq yayi wajen yarasa taya Anas ya samu ya shigo bayan uban securities daya zuba awaje be k’arisa wannan nazari ba yaji an cukumo mai collar riga. Kafin ya hankara Anas yakai masa wani erin mumunar punch da hannunsa me zobuna uku, take hancin Farouq ya fashe ya soma zuban jini. Wani punch d’in ya sake kai masa aciki tare da miqar dashi ko ta kan Fannah beyi ba, nishi yake tamkar zaki. Dogayen k‘afafunsa ya d’aga d’aya ya tunkud’e Farouq dashi seda yayi tumbling a k’asa Anas be barsa ba ba har yanzu. Sleeves nasa ya sake rolling yabi kan Farouq tareda hayewa kansa yasoma kai masa punches tako ina afuska ko wani spot a fuskan Farouq zuban jini yake har yanzu Anas be barsa ba seda yaji muryar Fannah tana kiransa. “Anassss!!!” Da ihu, alokaci guda ya bar abinda yake tare da kewayo wa. “Anas please help me, wayyo Allah !!” ta k’are maganan hannunta dafe kan cikinta se juyi take a k’asan ga wani erin azaban da ita kad’ai tasan yadda takeji acikinta. Hawaye take me tsuma zuciya. A gurguje Anas yayi kanta tare da aza kanta kan cinyansa. Hannunsu ya had’e “shhh! Flower am here, your Habeebi is here kinji stop crying.” A kasalance ta d’ago idanunta ta azasu kan fuskarsa daba abinda ke kwance akai banda tsantsan damuwa da tashin hankali a raunane. “Habeebi I’m sorry, I‘m sorry plea-” bata k’are maganar ba ta sakar dawai irin wahalallen k’ara;
“Arghhh! wayyyooo Alllahh cikina Anas help me please zan mutu wayyyooo Allah!!” ta k’are maganar hannunta dafe kan cikinta.
“Flower me Farouq ya miki? Meya miki?” Yayi maganar cike da tashin hankali.
Da k’yar ta iya nuna masa kwalban da yatsanta, a hanzarce ya miqa hannu ya d’aga “Nooo!! Nooo!! Nooo!! please” abinda yake ta furtawa kenan bayan ya karance jikin kwalban, wani irin k’ara Fannah ta sake sakarwa tuni ya jefar da kwalban tare da d’aga skirt nata jini yaga yana bin k’afafunta unstoppingly.
“Noo!! please NOOO! Fannah please noo Flower.”
“Anas I’m sorry ple-” bata samu daman k’arisa maganan ba idanunta suka ruhu ta bar motsi kwata kwata. “Flower I can’t lose you please wake up dan Allah kitashi please Flower I can’t leave without you, don’t leave me please” jinin dake bin k’afafunta se dad’a yawa yake. Rungumota yayi a jikinsa gagam tare da had’a musu goshi se kuka yake yana sunbatu. Daga bisani ya mik’e a fusace ya nufi kan Farouq da har ayanzu ya kasa koda motsa k‘afa dan yadda ya bugu kansa Anas ya haye tare da shaqure masa wuya da k’arfin da Allah ya basa, zuciyansa se tafasa yake yana saqa masa ya kashe Farouq kar yayi sparing nasa. “You must die you filthy son of b*tch you are going straight to hell...”
*© MIEMIEBEE*
beeenovels.blogspot.co.ke
16 comments:
More grease to ur elbow so happy an Ga fannah yyeeeeeh but what did he give her so sad ooh
More grease to ur elbow so happy an Ga fannah yyeeeeeh but what did he give her so sad ooh
Tanks sis
Fannah ur plan worked but dat devil still killed ur baby 😨 anas don't spare him kill him😤😤😤😠😬
Faruq ur re a basterd
Wow at last, tank u n keep on d good job 👍👍👍
Wow at last, tank u n keep on d good job 👍👍👍
Oooh Allah
oh mrs writer.... don't let her Ciki zubewa and fannah kiyi qoqari thank for your plan
Thanks muna biye dake.A
llah y kara basira
Thanks muna biye dake.A
llah y kara basira
So happy ansamu Fannah but the baby hope it's not gone....
Wow atlast thanks dear
Mr fauzi mana take her to the hospital and let that stupid guy zuwa dawowar ka, fannah tho 😭😭
He came just in time to save his flower
Thanks miemie
Plsss dnt let d ciki ya zube.... tnxx alot
Sis pls continue
Post a Comment