Saturday, 3 September 2016

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 23
BY MIEMIE


     “Ya Anas wace wannan tamin kyau.” Cewar Amal da suka had’a ido hud’u da Fannah dake ta kallonsu.
   “Wannan?” Ya nuna Fannah. Kai ta giad’a “ai kin fi wannan kyau Angel.” Fannah dake murmushi take yanayinta ya soya jin abinda Anas yace. “Dagake Ya Anas?”
     “Sosai ma Angel wannan ai bata da kyau.”
    “To Ya Anas wace ita? Metakeyi anan?”
     “Nima bansanta ba tana aiki anan ne.”
    “Nikam tamin kyau Ya Anas.” Nan ta mik’e daga kan cinyarsa ta nufo wajen Fannah. “Hi” tace da ita. Fannah na murmushi tace, “hello beautiful.”
    Amal ta murmusa sosai “dagaske ina da kyau kamar yadda Ya Anas yake fad’i?”
     “Sosai Ya Anas naki beyi k’arya ba.”
   “Toh me sunanki?”
   “Fannah kekuma fah?”
    “Amal amman Ya Anas na kira na da Angel.”
   “Nice name Amal.”
   “Amal kije kiyi breakfast kinji? Karki biyeta da surutu kinji Angel d’ina?”
    “Okah Ya Anas, Fannah ba-bye.”
     “Ba-bye” Fannah tamata sannan ta fice. Ita ina ma yadda halin Amal ke haka halin Anas yake dataji dad’i, kawai se tana murmushi wa kanta.

      “Kuma murmushin me kike?”
     Babu ta amsa sa a takaice. Kallo ya watsa mata sannan yaci gaba da abinda yakeyi. Coffee sau uku ta had'a masa a ranan sannan da yazo tafiya ta had’a masa cikin flask kamar jiya.

   ****

     Fannah da Afrah ne zaune tsakar sede kallo d’aya Afrah tamata tagano Fannah ta wula duniyar tunani.
    “Wai Ya Fannah tunanin me kike haka?”
    “Aww ni!” Ta fad’i a birkice. “Ba komai.”
      “Oh common kidena min k’arya dan Allah. Bade kema kin kamu da san Mr. Fauzi ba?”
     “Ya Salam!!! Afrah wai giya kike sha ne?”
    “Toh fad’a min tunanin me kike?”
       Numfashi Fannah taja, “kinsan wani abu ne Afrah?” Kai Afrah ta kad’a Fannah ta cigaba; “ni al’amarin Mr. Fauzi mamaki yake bani kinsan ban tab’a ganinsa yana dariya ba ke ko murmushi bayya yi kullum cikin masifa da tsawace mutane yake, amman yau da wata k’anwarsa tazo bakiga yadda yake dariya ba wallahi-”
    Afrah ta katse ta “sekuma ya miki kyau kikaji dama kema yana miki dariyan koh?”
    “Ke Afrah anyi mutum wallahi.” “Nama fasa baki labarin.” cewar Fannah.
      “A’a yi hak’uri Ya Fannah please.”
       Fannah ta cigaba, “kinsan wani biggest secret nasa kuma?” Kai Afrah ta kad’a mata.
      “Dan Allah karki fad’awa kowa, Mr. Fauzi yana shaye shaye.”
    “Iyye!” Afrah ta zaro idanu waje. “Yana mene? Shaye shaye fa kikace?”
    “Ke da Allah kiyi a hankali kar a jiyo mu. Yana shaye shaye amman kuma danayi tambaya se akacemin wai yanada horrible past, akoi abinda ya tab’a faruwa a rayuwarsa can baya wanda yasa yake duk wani abinda yakeyi yau kuma kinsan the most interesting part of it? Duk tsiyar Mr. Fauzi wallahi when it comes to family yanada kirki sosai kiga yadda yabani bandir na N200 mana.”

     “Gaskiya ne amman Ya Fannah wallahi tausaya miki nake, shaye shaye fa in randa ya bugu ya miki wani abun fah? Ki nemi wani aiki please banasan abu ya tab’a ki.”
       “Karki damu Afrah in shaa Allah ba abinda ze min, ni so nake naji me tarihin sa mesa yake shaye shaye. No offense amman Mr. Fauzi kyakkyawan namiji ne da duk macen data gansa (musamman ‘yan matan miemie bee novels group LOL) zataji tana sonsa kotaji ya burgeta ga kyau ga kud’i ga class ba abinda ya rasa mesa zena shaye shaye? Dole da akoi k’wararren reason and I must find out wayasani ko in giara masa rayuwa.”

      Cike da mamaki Afrah ke kallon Fannah, yaushe rayuwar mutane ya soma damun Fannah’n da bata shiga cikin jama’a. Ahhh! gaskia Mr. Fauzi ya k’ure ta fannin had’ewa. “Toh kekuma tanan kika b’ullo yau? Ai bari ya cigaba da saki kuka ni ba ruwa na. Ina ruwanki da shaye shayensa yaga dama ya dawwama dashi mana. Nikam gaskia ina ji miki tsoro.”
    “Worry not Afrah.”
 
    Washegari ma tun 7:00AM Fannah tagama shirinta se jiran call daga Anas take amman shiru 7:30AM nayi kawai ta tsari napep ta k’arisa office nasa koda datayi knocking bakin k’ofar kuwa ba response ta gwada bud’ewa ma a rufe waje ta nema ta zauna daga gefe tana jiran dawowansa.

   8:00AM on the dot k’ofan elevator ya bud’u Anas ya bayyana daga bayansa. Cike da mamaki Fannah ke kallon Anas dake sanye da suit as always. Wai shi jira yake ne se takwas d’in daidai ya cika ya shigo a’a kokuwa kawai perfect timer ne? Binsa da kallo take tana wannan nazari har ya iso bakin k’ofar bata sani ba.
      “Incase kina mamakin ko tsayawa nake se daidai 8:00AM yayi nake iso nan toh you are mistaking kuma wai ban hanaki kallo na haka ba?”
      “I’m sorry” ta fad’a a kunyace.
     “Ba abinda na tambaya ba kenan.”
     “Ka hana...” Ta fad’i kanta a k’asa.
      “Then kidena, saboda ke barin fara sa niqaf ba. Mschww!” nan ya bud’e k’ofar office d’in yashiga, Fannah na biye a bayansa. Bayan ya ajiye jakansa ya juyo tare da crossing arms nasa a chest nasa yana kallonta.

       “Waye ya gayyace ki nan?” Sam bata fahimce sa ba. Hijbanta me hula ta sake ja tare da rufe mata kusan rabin fuskarta, ta tsani taji wannan blue eyes nasa kansa.
      “So kike na sake repeating kaina?” Ya sake tambayarta yana mata wani erin kallon rashin isa.
    Murya ciki ciki tace, “Sir ban fahimce ka ba.”
    “Dama ina zaki fahimta? Uban wa ya gayyato ki nan yau? Ni na kiraki nace kizo?”
  Kai ta kad’a masa “Sir naga yau thursday ne kuma ranan aiki ne shiyasa.”
       “So what? Nifa sanda na fad’a miki banasan shisshigi, wai ku mata duk haka kuke ne? Tunda kin kawo kanki off you go, make me coffee. Kuma wannan fuskarki da kike rufewa ki bud’e is not as if I’m interested in looking at it.”

     A hankali ta mayar da hijabin daidai sannan taje ta ajiye jakarta ta had’o masa coffeen yauma sauran kad’an ta sake zubarwa. “Wai wace erin clumsy mutun ce ke? Ehh? Am teilling you yau da wannan coffee ya zube kan wannan building drawing sekin re drawing min I don’t care baki iya ba. Mschww!” fisgan cup d’in yayi daga hannunta wanda a garin haka ya tab’a mata yankanta dake kan warkewa. K’ara ta sakar amman ko a kwalan rigarsa komawa tayi ta zauna kan kujera tana kuka. Anas be ma san tanayi ba can da kukan ya ishesa yace, “ke!” A hankali ta d’ago jajayen idanunta ta a zasu kansa. “K’aran kukan nan na distracting d’ina ko kiyi shiru kokuma ki fita.”

      A hankali ta mik’e ta sauk’o k’asa inda ta saba ganin Yusuf yau ma can ta samesa. “Fannah ya haka idanunki duk sunyi ja? Kin ji ciwo ne.”
     Murmushi ta k’irk’iro “a’a ba komai.”
      “A’a da akoi komi keda Boss ne?”
    Kamar ta masa k’arya sekuma ta fad’i gaskia kawai. A hankali ta giad’a kai hawaye na sake cikowa idanta.
      “Haba! Fannah I thought you were a fighter, ai in kikace zaki biye wa Boss kullum kina cikin kuka kenan, haka shi yake in ya bak’anta wa mutum rai ne yake jin dad’i, hak’uri zakiyi kina basa uzuri, wallahi kina ganin Boss haka ne he is weak kawai pretending yake to be strong, past d’insa kullum bibiyarsa yake zuwa present kinga ko dole yana sauk’e haushinsa kan mutane. Kiyi hak’uri.”

     “Toh amman Yusuf mesa duk tsiyarsa naga yafi wa mata kan maza mesa?”
     “Nima bansani ba Fannah wannan lamari se Allah. Barinje inyi arranging wad’annan a file room.”
     “Muje tare ba abinda nakeyi nima.” Haka duk inda ze je Fannah tana biye dashi, sosai ta zagaya building d’in ranan floors kad’an ne batayi exploring ba. Duk wani walak’anci erin na Anas ma ta manta dashi se enjoying kanta take gun Yusuf gashi da surutu da kayan ban dariya. Abinci ma tare sukaci bayan sunyi sallan azahar tama manta yakamata taje ta had’a wa Anas coffee tunda azahar tayi.

      Anas na zaune kan table nasa bayan ya idda sallah se zanen building drawing d’in yake. Bayan ya gama ya soma modeling zanen, zane ne me uban kyan gaske, bungalow ne amman had’ade harda underground ga garden da swimming pool ba abinda babu ciki. Jiran Fannah yake tun d’azu tazo ta had’a masa coffee amman shiru, shi yanzu ya saba inbe sha coffeen Fannah ba baijin dad’i. Inde ze sha coffeen ta kuwa be damuwa da cin abinci. Har to 1:30PM Fannah bata dawo ba.

       Wayarsa ya ja daga kan table ya yayi scrolling kan contact nata ya kira to his suprise waya ya soma ringing cikin office d’in wato ko fita da wayartan ma batayi ba. Tsuka yaja yayi hanging take ransa ya b’aci Kacallah ya kira ko ya ganta sam Kacallah yace besa ta a ido ba. Ya kira kusan mutane uku duk ba wanda ya ganta, kokuma suce d’azu sunga wucewarta. Yusuf ya kira daga k’arshe.
      “Hello Boss?” Cewar Yusuf.
     “Kaga Fannah?” Anas ya tambayesa ba wasa cikin muryarsa. Tunda Fannah taji Yusuf yakira Boss taji cikin ta ya rud’e. Kai take kad’a wa Yusuf kan yace batta nan amman inaaa shima Yusuf d’in tsoro yake kar Anas ya gano gaskia yayi firing nasa.
     “Yes Boss.”
   “Ina take then?” Anas ya tambaya almsot kamar masifa.
    “Mu.. Muna tare Boss.”
    “Aikin daka koma yi kenan ko? Toh kaji kasani nan ba wajen baza soyayya bane zaku iya yin abunku a waje amman banda cikin building d’ina.”
   “I’m sorry Boss it will never happen again.”
     “Better” cewar Anas “ita kuma budurwar taka kace mata tazo ina jiranta.” Ding! Ya katse wayar kafin Yusuf ya masa bayani, sam ya kasa kallon Fannah.
     “Yusuf meyace?” ta tambaya duk ta rud’e.
     “Karkiyi kuka please, kije yana kiranki kinyi wani laifi neh?”
    “Innalillahi!” Nan ne ta tuna bata had’a masa coffeen rana ba. “OMG! Mr. Fauzi zeyi ball dani yau wallahi coffeen sa na mance, nashiga uku” take ta soma cin faratun ta.
    “Don’t panic kiyi sauri kije kafin ya sake fusata.” A sanyaye ta mik’e k’afafunta se b’ari suke. Koda ta isa sama kasa knocking tayi bakin k’ofar already hawaye ma sun fara ciko mata a hankali tayi knocking sau d’aya shiru be amsa ba kuma sarai yaji nan tayi na biyu. “Come” yace a hankali ta bud’e k’ofar ta mayar a nitse sannan ta tako cikin office d’in ta tsaya da kanta a k’asa. Pencil dake hannunsa ya ajiye ya d’ago kai yana kallonta.

       “D’au jakarki kibarmin building” ya fad’i ba tare da nuna damuwa ba. A razane ta d’ago kai hawaye na bin kumatun ta “Mr. Fauzi I’m so sorry dan Allah kayi hak’uri please.”
     “Don’t let me repeat myself. Kin jini ki d’au jakarki ki tafi zan kira Adam ya biyaki kud’in ki. Now off you go.”
  Kuka take sosai in Anas ya koreta bata san ina zata samu wani aikin ba yadda neman aiki keda wuya “Sir please, hakan bare sake faruwa ba dan Allah kayi hak’uri.”
  Ko sauraranta baiyi “in kika barni na sake nanata kaina ranki ze b’aci.”
   “Sir dan Al-”
   Yi yayi kamar ze tashi. Har k’asa Fannah ta durk’ushe tana kuka “dan Allah kayi hak’uri wallahi in kayi firing d’ina bansan ina zan sake samun wani aikin ba, ni nake kula da family na Baba na bashida lafiya have mercy please.” Yana jin ta ambato family’nta seya nemi fushinsa ya rasa “get up” yace mata. A nitse ta mik’e tana share hawayenta.

      “For your family’s sake, zan barki ki cigaba da aiki anan.”
    Wani sanyi taji a ranta “thank you sir thank you so much.”
      “Inba wai na manta bane na hanaki min godiya.” Duk wannan magana dayake bai kallin Fannah. Se a yanzu ne yad’ago kai yana kallonta da blue eyes nasa. “Ki bud’e kunnuwanki dakyau ki jini.” Kai ta giad’a “inaji Sir.”

      “Yau shine na farko kuma na k’arshe da zaki sake zuwa wani waje kibar min wayanki a office kina jina?” A hankali ta giad’a kai. Ya cigaba “kin ajemin saboda in miki recieving calls ne?”  “A’a kayi hak’uri.”
    “Ai dama saboda na hak’uran ne saisa kike tsaye cikin office nan har yanzu. Secondly, building d’ina ba wajen yin hira da saurayi bane in keda saurayin naki kunasan spending time tare seku bari in kun bar nan banasan iskanci cikin nan aiki ya kawo ku ba soyayya ba. I hope am clear.”

        “Sir Yusuf fa ba saurayi na bane ka-” ta fad’i kanta na kallon k’asa a yayinda ya katse ta “ban damu ba koda mijinki ne, nide na fad’a miki the next time kika manta abinda ya kawo ki nan saboda hira ya miki dad’i you will be fired for good.” Da hannu ya mata nuni wuce ki had’a min coffee.

    Bayan ta had’a masa ta ajiye kan table d’in. Sosai model dayake had’awan ya mata kyan bala’i sarai ya gane abinda take kallo kenan. “Cikin rules naki I made it clear banda shisshigi so mind your business please”
   “I’m sorry” tace sannan ta koma ta zauna tare da ciro wayarta tana game ita ta k’osa ma lokacin tashinsu yayi  ta tafi gida. Tana cikin yin game a wayarta Anas ya buga table da k’arfin daya firgita ta. “Kashe game d’innan” ya fad’i ransa b’ace.
     “Sir I’m sorry amman fa nasa a silent.”
    “Meaning baraki kashe ba kenan?”
    “A’a zan kashe” ta amsa a takaice.
    “Then make it quick.” Nan ta kashe daidai lokacin wayarsa ya soma ringing ganin Amal ke kira ya murmusa kallonsa kawai Fannah take.

     “My Angel” ya ce da Amal.
    “Ya Anas zan taho office naka yau tunda banje school ba.”
    “Angel amman fa bakida lafiya kikace.”
    “Toh Ya Anas ni banasan physics d’innan kuma har double muke dashi yau sesa nayi k’arya.”
    “Angel! K’arya!” Yayi exclaiming.
    “I’m sorry Ya Anas.”
   “Toh karki sake.”
    “Ya Anas inzo? Inasan inga wancan Fannah d’inne I want to be friend with her.”
   “Da Fannan?” Ya tambaya cike da mamaki. Jin an kira sunanta ta d’aga kai ta kallesa shima kallon nata yake take ta kau da kai.
 
   “Eh Ya Anas ita tabada hankali.”
   “A’a Angel, Fannah bata zo office ba yau kibari se watarana.”
   Cike da mamaki Fannah ta d’ago tana kallonsa toh in ba’a office take ba  ina take?
    “Yawwa ba-bye” yayi hanging. Ko kallon Fannah ma beyi ba yacigaba da yin abinda yake.

*© miemiebee*

No comments:

Post a Comment