TANA TARE DA NI... PAGE 100
BY MIEMIEBEE
*SHARHI AKAN*
*TANA TARE DANI*
👫🎀❣👫🎀❣
_Assalamu Alaikum_
Da sunan Allah mai rahma mai jin kai
Alhamdulillahi
Allah ne abun godia da ya nuna mana karshen littafin nan lfy duk da anta samun matsaloli daban daban da korefe korefe na jamaa akan littafin amma Alhamdulillahi Allah mai kowa mai komai ya bata ikon gama shi lfy sbd kyakkyawar niyyata da kuma hakurinta da halayenta nagari tarbiyar kirki data samu wajen iyayenta da kuma masoyanta na gaskia masu nuna mata gaskia suna sakata a kan hanya ta kwarai yasa bata kula duk masu son ganin karshenta ba.
_Little advice to d haters_
*Always b urself, express* *urself, have faith in urself, do not go out and look 4 a successfull personality and duplicate it*
*TANA TARE DANI*👫🎀❣🎀
Warra luv story..this is really the best luv story of d year
Munsha soyayya gashi mun ilmantu mun waazantu kuma yayi mana tsaye a zucia sbd darussan rayuwa da ke ciki.
Abinda nake so masu zagin writers su gane shine duk yadda kuka dauki buk en writer a wulakance kuke ganin hauka da jahilci suke yi ku sani yana koya darasin rayuwa komin kankantar darasin kuwa.
*Kadan daga cikin darussan MieMie Bae*
1....Soyayya..soyayya wata ginshike ce ta rayuwar aure wadda idan babu ita auren na iya samun tangarda ko barazana da fuskantar matsaloli..soyayyar nan kuma a musulunci ta samo asali tun..hadisai da dama sun bamu labrin yadda Manzon Rahma ya rayu da iyalanshi cikin soyayya,wasu hadisan sun gaya mana yadda yake taya matanshi aikin gd,yake kula dasu yake ji dasu haka kuma yake zaunawa cikinsu suyi soyayya har wanka yake yi tare da matanshi..ya rayu cikin soyayyar matanshi ya kuma koma ma ubangijinmu cikin soyayyarsu. Don haka Annabin rahma shine shugaban masoya na duka duniar nan duk wata soyayya da muke yi yanzu ta samo asali ne a musulunci kuma kwafa mukayi..don ka sumbaci matarka ko ka rungumeta duk sun duk sun samo asali ne a musulunci..wanda kuma har yanzu dabia ce ta larabawa..idan dai har macen nan muharramarka ce. Yanzu ne mutanenmu suka dauka idan kana gwada ma miji soyayya sai ace baka da kunya ko kuma boko tayi maka yawa ko kuma ta cika fitsara..idan kuma marubuciya ce ta gwada yadda ake soyayyar miji da mata a tsaftace don jamaa suyi koyi su kuma gane nuna ma miji soyyaya ba rashin kunya bane sai a fara ce mata yar iska..wlh mata mu farka duk wani abu da marubutan mu ke yi sunayi ne don jan hankali da fadakarwa..mai yasa wasu mazajen sunfi gane ma matan waje? Sbd soyayyar nan da ake masu da kissa da kisisina wadda ta gd ta kasa tsayawa tayi alhalin ta wajen nan babu abinda ta fiki
MieMie Bae kinyi namijin kokari wajen nuna muhimmancin soyayya a rayuwar aure sbd ita ke kara so ta kawo shakuwa har aji baa iya rabuwa da juna
2.... Yadda ummimi ta tafi tabar yaranta da mijinta sbd talauci.
Wannan wata babbar magana ce da kika tabo wadda a karence karence na ban taba cin karo da irin wannan matsalar ba.
Wannan wata matsala ce da take faruwa a arewacin kasarmu kullu yaumun. Mata na zubda yaransu da mazajensu da sunan babu su tafi saudiyya *TUKARU* ko kuma su tafi wani sashe na kasar nan nesa da gd da iyalansu.. tafiya suke basu waiwayen bayansu, sunsa gabansu a hanyar neman dunia kawai suna mantawa da lahira. Duk Wanda kejin waazin malamai da wadanda ke zuwa saudiyya sunsan irin ta'asar da *tukaru* ke tafkawa wasu don rashin tsoron Allah har aure sukeyi kan aure sbd tabar gd da miji da yaya alhalin bai saketa ba kuma haka zata je tayi wani auran don neman abun dunia.
Shi arziki da talauci duk na Allah ne..babu mummunan arziki irin wanda aka samu ta hanyar haram wanda kuma neman arziki ta haka ya riga ya zama ruwan dare sai dai muyi fatan Allah ya karemu ya bamu mai albarka..kuma irinsu Ummimi a banza suke karewa dangin a wofi daga baya sbd dama duk wanda yahau motar kwadayi tashar wulaknci zata aje shi. Ga uwa uba alhakin iyaye,yaya da kuma miji.chaiiiii gaskia zunubin yayi yawa. Nasu hali irin na Ummimi gareku
Mie mie Bae ta gwada maku illar haka takuma ce don Allah a gyara.
3...Illar rashin uwa
( ba ina nufin wadda Allah yayi ma waadi ba) ina magana ne kan wadda ta tafi tabar yayanta da dacinta rashin rashinta wanda hotonta na rashin kirkinta baya taba goguwa a zukatan yayanta ..watakan rashin uwa ta irin hanyar nan ba Karamin illa da gibi yake ma rayuwar yara ba sbd basu manta abinda tayi masu wanda hakan kesa wasu su tashi cikin kunshi da bakin ciki su kuma tsani mata sannan wasunsu su fada harkar shaye shayen nan na zamani har su koma suna aikin Assha irinsu sata da raping..jst like how Anas raped fannah @ deir young age..ai sun samu abokan gaske ko kuma jajirtattar mata Kamar fannah sannan zaka ga suna rage wasu abubuwan a hankali har su daina ma gaba daya jst like Anas
4....Tasirin gyara musamman daga wajen wanda kake so ka yadda dashi kuma kake kaunarshi
Miemie na yaba maki sosai ta wannan fannin
Gyara ko a musulunci baa yinshi da cin fuska ko cikin bainar jamaa.. Idan dai har tsakaninka da Allah gyara kake son yi ma mutum to kayi shi ta hanyar da addini ya koya mana..ta hanyar lallashi nasiha da ban baki Kamar yadda Fannah tayi amfani da wadan nan makaman wajen gyara gurbatacciyar rayuwar Anas a hankali.. Tayi amfani da ilminta da matsayinta na ya mace da aka sani da iya kissa ta gyara *Anas* a hankali tana mai addua kuma har Allah ya nuna mata lokacin da ya shiryu ya dena masifa, fushi, zuciya, shaye shaye,yaudarar yan mata da sauran munanan halayen data gyara mai ta hanyar da addini ya shimfida
Haka kuma duk wanda ke gyara sai yayi hakuri Kamar yadda *Fannah* tayi sbd banna ce ke faruwa lokaci daya amma gyara sai a hankali.
5....Amfani da fa'idar hakuri
Kamar yadda *Fannah* ta yafe ma *Anas* duk da zunubinshi mai yawa ne amma daya tuba kuma tasan yayi nadamar gaskia
Haka ake son musulmi kwarai ya kasance mai yafiya..kuma yadda yaran ummimi suka yafe mata haka ake so duk wanda yace yasan yayi laifi amma yayi nadama kayi hakuri ka yafe mai to don Allah mu daure mu dinga yafe ma junanmu sbd ita kanta duniar da abinda ke cikinta kalilan ne kuma ita duniar nan ba matabbata bace
MieMie Bae kinyi kokari da kika tabo mana illar raping ko kuma ince illar Aiken yara mata kananu da daddare koma da ranan ne musamman idan kasan cewa unguwarku is not secured..Yanzu Allah ya kawomu wani zamani damu iyaye mata ke sake kana tarbiyar yaranmu mata musaman masu karancin shekaru.. Duk wanda ke aiki police station ko asibiti yasan yadda rape case ya zama vry rampant kuma duk sbd sakaci da saken da muke da yayanmu hannun almajirai,masu gadi, yaran unguwa,uncles, cuz,nephew duk babu yadda bata kasancewa..ya kamata musa ido mu gyara Kamar yadda MieMie Bae ta gwada mana illar hakan da irin rayuwar matsin da hakan ke jefa victim and her parent.. Kuma wani tabo ne da baya kankaruwa har abadaaaaa
Ina tsaya haka nan sbd lessons din cikin tana tare dani basu taba karewa sai dai inbar sauran masoya su fadi nasu suma. Tunda ni uwace bai kamata in hada komai in cinye ba.
Zanyi amfani da damar nan don mika godia ta ga
Yan grp dinmu na novel
*NOVEL 3*
*Fateemah Musa*
*Fateemah Dan maliki*
*Zareenah*
Kunfi kowa son *Tana Tare Dani*
MieMie Bae na sonku,nima ina sonku muna kuma *tare daku*
*ALLAH NA TARE DA KE*
# _Babbar tarayya_
*INA TARE DA KE*
# _Mumcynki_
*SUNA NA TARE DA KE*
# _Your true fans_
_Har abada insha Allahu_
*Aunty Sis* 💞 Nason dukkan *MieMie Bae's fans* a duk inda kuke kuma *INA TARE DAKU*
*Ina rokon Allah ubangiji* *ya cigaba da daukaki yasa kifi* *haka,ya kara maki basira da hazaka,ya kareki daga* *sharrin makiya da mahassada na fili dana* *boye ,da yan black belly da masu kambun baka*
*Allah ubangiji yayi ma rayuwarki albarka yasa ki fara karatunki lfy ki gama lfy ya kareki daga sharrin azzaluman malamai da kadangarun campus* *Idan lokacin aurenki yayi Allah ya* *azurtaki da miji nagari* *wanda zakuyi zama har a aljannah firdaus*
_Dx All wat ur mum wl say_
*I luv u so much*💞❣🎀
💞 *Aunty Sis*💞
alhamdulillah
ReplyDeleteWAnnan haka yake littafi ya hadu mun dau darasi 'yan da zamu zauna da matan mu in munyi aure nida kaina littafinki ya sakani innayi aure zan taya matata aiki kaman 'yanda Anas ke taya Fanna
ReplyDeleteAllah sa😄
DeleteAllah sa😄
DeleteWAnnan haka yake littafi ya hadu mun dau darasi 'yan da zamu zauna da matan mu in munyi aure nida kaina littafinki ya sakani innayi aure zan taya matata aiki kaman 'yanda Anas ke taya Fanna
ReplyDeleteAlhamdulillah 👌👍Allah ya kara basira
ReplyDeleteWeldone dear
ReplyDeleteWanne zamui expecting next
ReplyDeleteGaskiya kin yi kokari
ReplyDeleteBest novel on social media, u really entertained us wt ur novel, a big thumb up to u dearie... Wallahi kamar true life story..muna jiran sabi
ReplyDeleteThis is the best novel i had ever read,thank you so much
ReplyDelete